Za a bayar da Zobe ga wadda ta lashe Gasar kofin duniya ta 2026, Gasar kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images
A karon farko a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, zakarun gasar za su samu wata kyauta ta musamman baya ga kofin da lambar yabo ta zinariya, za a bayar da zobe wato (championship ring).
Wannan sabon tsari ya samo asali ne daga al'adar wasannin Amurka, inda ake bai wa zakarun manyan gasa zobba na musamman domin tunawa da nasararsu.
Ƴan wasan da za su lashe wasan karshe tsakanin Argentina ko Sifaniya, za su karbi lambobin yabo na zinariya kamar yadda aka saba, sannan kuma za su samu wadannan zobba na tarihi.
Za a buga wasan karshe ne ranar Lahadi a filin wasa na MetLife da ke East Rutherford a New Jersey.
An riga an tsara zoben, inda a gefe guda za a ajiye Kofin Duniya, yayin da daya gefen za a sa zoben.
Bayan an tashi daga wasan karshe, kocin tawaga da kyaftinta za su karbi wani zobe na wucin gadi. Daga baya idan an kammala kera shi, za a maye gurbinsa da asalin zoben a hukumance. Sauran ƴan wasan kasar za su karbi nasu zobban a wani lokaci a gaba.
Jimillar zobba 2,026 ne kawai za a kera, kuma kowanne zai kasance da lambar sa ta musamman. Daga cikinsu, 30 za a bai wa tawagar da ta lashe gasar, yayin da sauran za a sayar wa jama'a. Har yanzu ba a bayyana farashin su ba.
Idan Argentina ta lashe gasar, za ta zama kasa ta farko da ta kare kambunta a jere tun bayan Brazil a shekarar 1962. Ita kuwa Sifaniya, tana neman lashe kofin duniya karo na biyu bayan nasararta ta farko a shekarar 2010.
A gefe guda kuma, Ingila da Faransa za su kara a ranar Asabar domin tantance wanda za ta kare gasar a matsayi na uku.

























