Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/07/2024
Taƙaitattu
Harkoki sun fara daidaita a sassan duniya da aka samu katsewar intanet
Mutane 11 sun mutu bayan karyewar gada a China
Gobarar jirgin ruwa ta kashe mutane 40 a Haiti
Ƙaruwar masu kamuwa da cutar ƙoda na tayar da hankali a jihar Yobe
Ɓata-gari ka iya amfani da katsewar Intanet don aikata laifuka - Masana
Rahoto kai-tsaye
Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar da Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin namu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni daga sassa daban-daban na duniay.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
'Za mu yi cikakken bincike kan ingancin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya'
Asalin hoton, Hon. Tajudeen
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta gudanar da cikakken bincike kan ingancin man da masu ababen hawa ke amfani da shi a faɗin ƙasar.
Hon Tajudeen ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin wata ziyara da ya jagoranci shugabannin majalisar wakilan ƙasar zuwa matatar mai ta Dangote da ke birnin Legas, kamar yadda Gidan talbijin na Channel ya ruwaito.
Kakakin majalisar na wannan maganar ne bayan gwajin ingancin man disel da aka yi a gabansu lokacin ziyarar tasu zuwa matatar.
Tun da farko dai shugaban matatar Alhaji Aliko Dangote ne ya yi wasti da wani zargin da ke nuna cewa man da ake tacewa a matatar tasa bai kai ingancin da ake buƙata ba.
Domin tabbatar da iƙirarin nasa, Dangote da tawagar ma'aikatansa sun gudanar da gwajin man dizel da aka sayo daga wasu gidajen mai biyu da kuma wanda matatar ke tacewa a ɗakin gwajin ingancin mai da ke matatar.
Bayanai sun ce an sayo man ne a gaban jagororin majalisar, sannan aka ɗauki na matatar Dangoten ma a gabansu domin kawar da shakku.
Shi dai mai marar inganci, masana na gargaɗin cewa amfani da shi ka iya lalata injinan ababen hawa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa man Dangote ya fi inganci fiye da na sauran gidajen mai biyu da ka shigo da shi ƙasar daga waje, kamar yadda Channels din ya ruwaito.
Dangote ya ce sakamakon gwaji alamu ne da ke nuna cewa man da ake shigar da shi ƙasar ba shi da ingancin da ake buƙata.
Kwastam ta miƙa wa NDLEA tabar wiwi ta naira miliyan 371 da ta kama
Asalin hoton, NCS/X
Babban kwanturolan Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Najeriya da ke lura da filin jirgin sama na Legas, Michael Awe ya miƙa wa hukumar Hana sha da Fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA tabar wiwi ta kusan naira miliyan 371 da jami'ansa suka kama.
Cikin wani saƙo da hukumar Kwastam ta ƙasar ta wallafa a shafinta na X, ta ce jami'anta sun kama tabar ranar 17 ga watan Yuli ɗaure cikin wasu ƙwalaye 40 da aka yi yunƙurin safararta.
Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar inda shi ma ta hannunta shi ga hukumar ta NDLEA.
Kwanturolan ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar NDLEA domin kakkaɓe ayyukan masu fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Asalin hoton, NCS/X
Ɗan Najeriyar da ke shirin kafa tarihi a Gasar Olympics ta 2024
Asalin hoton, BADMINTON CONFEDERATION AFRICA
A yayin da zakaran wasan Badminton na Afirka Anuoluwapo Juwon Opeyori ke shirin kafa tarihi a gasar Olympics a birnin Paris, ɗan Najeriyar na jin cewa ya yi abubuwan bajinta.
Duk da cewa an haife shi a wani ƙauye a Lagos, mafi cunkoso a Najeriya, ɗan wasan mai shekara 27 ya lashe kofin nahiyar guda huɗu, fiye da kowane ɗan Afirka a baya.
Abin da ya ƙara ɗaukar hankalinsa shi ne, yana zaune ne a ƙasar da babu wani wurin da aka gina don wasan Badminton, amma duk da haka yana fatan zama ɗan Afrika na farko da zai samu ci gaba a gasar ta Olympics.
Cutar kyandar biri na ci gaba da bazuwa cikin sauri a DR Kongo
Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo sun ce cutar Kyandar biri da ta ɓarke na ci gaba da yaɗuwa cikin sauri a ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ta ce tana ɗaukar jerin matakai domin yaƙi da yaɗuwar cutar, ciki har da lura da waɗanda suka cuɗanya da masu cutar da kuma ƙara sanya idanu.
Kakkain gwamnatin ƙasar, ya ce mutanen da ake sa ran sun kamu da cutar ya haura 11,000 ciki har da mutum 450 da suka mutu.
Lardin Equateur da ke yammacin ƙasar ne ya fi yawan masu fama da cutar.
A Farkon wannan wata ne Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ayyana cutar a matsayin barazana ga harkokin lafiya a duniya.
A Afirka ta Kudu rahotonni sun ce an samu mutum 20 masu ɗauke da cutar, ciki har da mutum uku da suka mutu.
Ana dai iya yaɗa cutar ta hanyar cuɗanya ko taɓa jikin mai cutar.
Hezbollah ta kai harin roka arewacin Isra'ila
Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar Hezbollah mai ɗauke da makamai a Lebanon ta ce ta kai harin roka zuwa arewacin Isra'ila ranar Asabar.
Hezbolla ta ce harin nata ramuwar gayya ce ga wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kakkaɓo wasu makamai da ta yi ƙiyasin sun kai 30.
Rahotonni sun ce wasu makaman sun faɗi ne a wurin da babu jama'a a yankin Upper Galilee da ke arewacin ƙasar, inda suka tayar da gobara.
Musayar wuta a kan iyakokin Isra'ila da Lebanon tsakanin Hezbollah - da ke samun goyon bayan Iran - da sojojin Isra'ila na ci gaba da ƙaruwa a makonnin baya-bayan nan, lamarin da ke haifar da fargaɓar ɓarkewar sabon yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.,
Jagororin majalisar wakilan Najeriya sun ziyarci matatar mai ta Dangote
Asalin hoton, Hon Tajudeen Abbas/X
Shugabannin majalisar wakilan Najeriya sun ziyarci matatar man fetur da hamshaƙin ɗan kasuwar ƙasar, Alhaji Aliko Ɗangote ya gina a birnin Legas.
Cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Hon. Tajudeen Abbas ya wallafa shafinsa na X - wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar 'yan majalisar -ya ce sun tattauna batutuwa masu amfani da shugaban matatar Alhaji Aliko Dangote.
Ziyarar 'yan majalisar ita ce ta biyu zuwa matatar cikin wata biyu.
Baya ga kakakin majalisar, akwai kuma mataimakinsa, Hon. benjamin Kalu da Hon. Ikenga Ugochinyere a cikin tawagar
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matatar ke shirin fara fitar da mai a wata mai zuwa, yayain da yake fuskantar matsalar samun ɗanyen man da yake buƙatar tacewa daga kamfanonin mai na duniya.
Ɓata-gari ka iya amfani da katsewar Intanet don aikata laifuka - Masana
Asalin hoton, ..
Masana harkar tsaron intanet sun yi gargaɗin cewa ɓata-gari ka iya amfani da matsalar katsewar intanet don aikata miyagun laifuka.
A yau ne hukumar Kula da tsaron intanet ta Australiya (ASD), ta fitar da sanarwar game da masu satar bayanai da ke aika saƙonnin iƙirarin yin gyare-gyaren manhajojin daga kamfanin 'CrowdStrike', mai kula da tsaron intanet.
"Gargaɗi! Mun fahimci yawancin shafukan intanet marasa kyau da masu fitar da lambobin da ba na hukuma ba suna iƙirarin taimakawa ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi don warware matsalar katsewar intanet da aka fuskanta" in ji sanarwar.
Don haka hukumar ta yi kira ga masu amfani da fasahar intanet, da su yi amfani da manhajar kamafanin 'CrowdStrike' kawai don samo bayanai da duk wani taimako da suke buƙata.
Gargaɗin ASD na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da Cibiyar Tsaron Intanet ta Burtaniya (NCSC) ta yi a jiya don mutane su yi taka-tsan-tsan da sahihancin saƙon imel ko kuma kiran da ke nuna cewa na CrowdStrike ne ko taimakon Microsoft.
Tun a jiya ne dai aka fuskanci katsewar intanet ɗin a wasu sassan duniya, lamarin da ya haifar da tsaikon abubuwa da dama ciki har da tashin jirage da katsewar wasu kafofin yaɗa labarai da aiki a wasu asibiton faɗin duniya.
An kashe wata tsohuwar 'yar kishin ƙasa a Ukrainian
Asalin hoton, Getty Images
An harbe tare da kashe wata tsohuwa 'yan majalisar dokokin Ukraine, kuma 'yar kishin ƙasa a birnin Lviv da ke yammacin ƙasar.
A shekarar 2023, Iryna Farion ta janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar bayan da ta ce bai kamata ''yan kishin ƙasa na gaskiya'' a Ukraine su yi magana kan Rasha ba ko ta wane hali.
'Yansanda sun ce suna bincike game da kisan matar, mai shekara 60, wadda farfesa ce a fannin kimiyyar harshe.
'Yansanda sun ce ba a gano mutumin da ya kai mata harin, suna masu cewa rashin wutar lantarki ya sa kyamarorin tsaro ba sa aiki a lokacin.
Gwamnan yankin Lviv, Maksym Kozytskyi ya ce Ms Farion ta mutu ne a asibiti bayan harbin da aka yi mata.
Duk wanda zai ce a yi gaskiya 'yan Najeriya ba sa son ganin sa - Shugaban ICPC
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Matsalar cin hanci da rashawa ta gawurta kuma ta shiga jinin 'yan Najeriya ta yadda duk wanda zai ce a yi gaskiya, ko a kwatanta yin daidai, mutane na ɗaukar sa a matsayin wani bauɗaɗɗen wanda ba a maraba da shi.
Shugaban hukumar yaƙi da cin da hanci da rashawa ta ICPC Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka a zantawar da muka yi da shi a kan batutuwa daban-daban da suka shafi hukumarsa.
Ya ce ICPC kuma tana mayar da hankali a kan yaƙi da lalata mata da 'yan mata a wuraren aiki da makarantu, matsalar da ya ce tana ƙaruwa har a ƙananan makarantun sakandire da na firamare.
Ƴan sanda sun gano wajen haɗa ƙwaya a Afirka ta Kudu
Ƴan sanda a Afirka ta kudu sun ce sun gano wani waje da ake haɗa miyagun ƙwayoyi da yawan gaske.
Sun nce sun kama wasu mutane huɗu, ciki harda wani ɗan Mexico.
Ƴan sandan sun ce sun gano sinadaran haɗa ƙwayar ne a wata gona da ke yankin Limpopo inda suke zargin ana haɗa ƙwaya ta miliyoyin dala.
Rahotanni sun ce Afirka ta Kudu na fama da yawan matasa masu shan ƙwayoyi masu haɗari ga rayuwa, ciki harda hodar iblis.
Ƙaruwar masu kamuwa da cutar ƙoda na tayar da hankali a jihar Yobe
Al’ummar garuruwan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun koka a kan yadda ake ci gaba da samun karuwar masu fama da cutar koda, inda suka bayyana cewa adadin na ci gaba da karuwa cikin sauri.
Garuruwan Gashuwa da Jakusko da Nguru dai na cikin wadanda ke sahun gaba a fama da wannan matsala.
Jama’ar na neman agajin gwamnatocin jihar ta Yobe da kuma tarayya da su tallafa musu da karin taimakon a bangaren tacewa masu fama da wannan matsala jini a kyauta samakamakon tsananin talauci da al’umma ke fama da shi a Najeriya.
Ga rahoton da Zubairu Ahmad ya hada mana:
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton.
Ƙwararru sun yi hasashen sake katsewar intanet a karo na biyu
Asalin hoton, Reuters
Ƙwararru a fannin tsaron intanet sun yi gargaɗin cewa za a iya ƙara samun katsewar intanet saboda masu aikata laifi da ke son amfani da yanayin da ake ciki domin cimma burin su.
Yau da safe hukumar kula da tsaron intanet ta Australia ta fitar da wata sanarwar gargaɗi a kan yunƙurin da wasu ke yi domin aikata laifuka da sunan suna aiki ne a kamfanin CrowdStrike.
Sanarwar ta ce "Munafargar da jama'a cewa akwia wasu ɓata gari da ke aikewa mutane adireshin shiga wani shafi, tare da iƙirarin cewa za su gudanar da wasu gayre-gayre ne.
Hukumar ta buƙaci masu huɗɗa da intanet su kiyaye bayanan su da kuma daina shiga adireshin da babu tabbacin sahihancin sa.
Gobarar jirgin ruwa ta kashe mutane 40 a Haiti
Asalin hoton, Reuters
Mutane aƙalla 40 sun mutu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kama da wuta a gaɓar tekun Hiati.
Hukumar kula da masu yin ƙaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kuɓutar da wasu mutane 41 da ransu.
Hukumar ta ce hjirgin ruwan yana kan hanyarsa ne zuwa tsibirin Caico ne daga Cap-Haitien a lokacin da gobara ta tashi a cikin sa.
Ba a dai tantance abin da ya haifar da gobarar, amma rahotanni sun ce mutanen cikin jirgin sun riƙa kunna kandir, a wani ɓangare na ibada da addu'oin su.
Hukumar kula da masu yin ƙaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na kula da waɗanda suka samu rauni, kuma an kai wasu daga cikin su asibiti mafi kusa.
Dubun dubatan mutane ke yin hijira daga Haiti kowacce shekara, a wani mataki na guduwa daga tsananin talauci da rikici da ake fama da shi a ƙasar.
Mutane 11 sun mutu bayan karyewar gada a China
Asalin hoton, CCTV
Mutane 11 sun mutu, wasu 30 kuma sun ɓace bayan ruwan sama mai ƙarfi ya rushe wata gada a China.
Kafar yaɗa labaran gwamnati ta ce lamarin ya faru ne bayan ruwan sama ya janyo ambaliya a yankin Shaanxi.
An gano gawar mutane 11 da suka mutu ne a cikin motoci biyar da aka zaƙulo daga cikin ruwa. Ana zargin akwai motoci 20 yanzu haka a cikin ruwan.
A ranar Juma'a,aƙalla mutum biyar suka mutu a ambaliya da kuma zaftarewar ƙasa a wasu sassan yankin Shaanxi.
Sauran sassan China ma suna fama da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Sojoji sun ƙwace aikin sintiri a sassan Bangladesh bayan zanga zanga ta ƙazance
Asalin hoton, Getty Images
Sojoji na sintiri a kan titunan Bangladesh bayan rikicin da ya ɓalle tsakanin dalibai masu zanga-zanga da ƴan sanda.
Mutane fiye da 100 aka kashe a zanga-zangar ta nuna ƙin jinin gwamnati wadda ta tashi bayan sake ɓullo da tsari ware guraben aikin gwamnati ga iyalan ƴan mazan jiya.
Mutane sun watse a Dhaka babban birnin Bangladeshi, bayan hukumomi sun sanya dokar hana fita da za ta yi aiki har zuwa ranar Lahadi, bayan rikicin da ya ɓalle a ranar Juma'a da dare.
Masu zanga-zangar sun afka gida yarin birnin Narsingdi, inda suka kuɓutar da ɗaruruwan fursunoni.
Shugaban hukumar kula da ƴancin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya bayyana damuwa kan yadda jami'an tsaro ke amfani da ƙarfin da ya wuce kima a kan ɗalibai masu zanga-zanga, kuma ya ce dole ne su fuskanci hukunci.
Donald Trump ya tattauna da shugaban Ukraine ta waya
Asalin hoton, Getty Images
Dan takarar
shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya ce ya yi magana ta
wayar tarho da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Ya sha
alwashin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha idan aka zabe shi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada
zumunta, Truth, Mista Trump ya ce zai hada bangarorin biyu, domin su sasanta junansu.
Mista Zelensky ya tabbatar da kiran ne a wani sako da ya wallafa a
dandalin sada zumunta na X da aka
fi sani da Twitter.
Ya ce ya amince ya gana da Mista Trump da kuma tattauna matakan da suka
wajaba don tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a Ukraine.
Abokan Ukraine dai na fargabar idan aka zabi Trump a watan Nuwamba, zai
tilastawa Ukriane amincewa da yarjejeniyar da za ta kasance dai dai da shan kaye a hannun Rasha.
Harkoki sun fara daidaita a sassan duniya da aka samu katsewar intanet
Asalin hoton, EPA
Al'amura sun fara dawowa dai dai a fannonin lafiya da na zirga zirga da
bankunan da kafafewan watsa labarai da dama na duniya bayan katsewar hanyoyin
sadarwar da aka samu.
Kamfanin tsaron Internet na CrowdStrike wanda ya haifar da matsalar ya nemi gafara, bisa
lamarin da ya faru.
Lamarin ya samu asali ne sakamakon kuskuren sabunta tsarin Microsoft Windows.
Shugaban
CrowdStrike George Kurtz, ya
ce an gyara matsalar.
Sai dai ana iya shafe kwanaki kafin magance al'amura su dawo kamar yadda
suke a baya.
Sama da jirage dubu biyar ne aka soke tashinsu a jiya Juma'a sakamakon
faruwar lamarin.
Ana ci gaba da kira ga Biden ya janye daga takara
Asalin hoton, Reuters
Wani dan
jam'iyyar Democrat a majalisar dokokin Amurka ya ce shugaba Joe Biden ya kasa shaida shi, lokacin da suka hadu a wajen wani
taro a watan Yuni, duk da doguwar abotar da ke tsakaninsu.
A wani ra'ayi
da ya rubuta a jaridar Boston Globe, Seth Moulton, daga jihar Massachusetts ya jaddada kiran da ya yi wa
shugaban a farkon wannan watan cewa ya hakura da sake neman shugabancin kasar
saboda yadda shekarunsa suka tura.
Akalla ‘yan
jam’iyyar Democrat 30 ne a Majalisa suka bi sahun wannan kira.
Sai dai Mista
Biden ya dage cewa shi ne dan takarar da ya fi dacewa ya kayar da Donald Trump.
Ya kuma sanar da aniyarsa ta ci gaba da yaƙin neman zaɓe a mako mai zuwa.
A halin da ake
ciki, JD Vance dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Republican ya
ce idan har shugaban kasar ba shi da koshin lafiyar sake tsayawa takara, to bai
kamata ma ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki ba.
Barka da zuwa
Barka da zuwa shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa.