Abu uku da zan mayar da hankali a kai don gyara Man Utd - Pochettino

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye daga BBC Hausa daga 16 zuwa 22 ga watan Nuwambar 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Chelsea na kukan rashin Joao Pedro a wasanninta, Chelsea

    Joao Pedro

    Xabi Alonso ya ce dole ne dukkan 'yan wasan Chelsea su taimaka wajen cike gibin rashin Joao Pedro yayin da Blues ke fama da ƙarancin cin ƙwallaye, saboda rashin lafiyar ɗan wasan gaba.

    Alonso ya ce ƙungiyarsa tana buƙatar koyon yadda za ta tunkari wasanni ba tare da Joao Pedro ba, yayin da ɗan ƙasar Brazil bai buga wasa ba tun bayan nasarar 2-0 da suka yi a kan Everton a ranar 17 ga watan Oktoba.

    Pedro ba zai buga wasan Leeds United ba da za a yi a Stamford Bridge ranar Asabar.

    Pedro ya kasance muhimmin ɓangare a farkon kakar wasan da Chelsea ta yi a bangaren gurbin hari. Ya ci ƙwallaye biyar, shi ne na biyu cikin waɗanda suka fi yawan cin ƙwallaye a ƙungiyar a wannan kakar, amma tun bayan raunin da ya ji, Chelsea ta rage kai matsin lamba a wasa da abokan hamayya.

    Chelsea ta ci ƙwallo ɗaya kacal daga wasannin Premier League huɗu da Pedro bai buga mata ba, kuma ba tare da shi ba, Cole Palmer da Morgan Rogers sun fi fuskantar matsala wajen yin tasiri a wasanni.

    Saboda rashin ɗan wasan da zai jagoranci gurbin kai hari a matsayin lamba tara, Palmer da Rogers sun sha wahala wajen hadin kai a tsakaninsu, kuma yawan ƙwallayen da Chelsea ke ci ya ragu matuƙa.

    Yayin da Blues ta sauka zuwa matsayi na biyar a teburin gasar, kuma ta sha kashi sau biyu cikin wasanni uku na baya-bayan nan, ciki har da rashin nasara 1-0 a hannun Sunderland wadda a lokacin ke ƙarshen teburin gasar, Alonso ya jaddada cewa ba za su iya zama suna jiran ɗan wasan gaban nasu ya murmure ba.

  2. Babban jami'in Man United ya yi bayani kan yawan korar koci a kungiyar, Manchester United

    Omar Berrada

    Babban jami'in gudanarwa na Manchester United, Omar Berrada, ya kare yawan sauye-sauyen kociyoyi da kuma dabarun sayen 'yan wasan kungiyar, yana mai jaddada cewa kungiyar ta Premier League har yanzu tana da cikakken kudurin mayar da kungiyar kan ganiya duk da cewa ta sauya manyan kociyoyi uku cikin kasa da kakar wasa uku.

    Sabon koci, Mauricio Pochettino, wanda aka nada bayan sallamar Michael Carrick a farkon wannan watan, zai jagoranci wasansa na farko ne da Liverpool ranar Lahadi.

    Sai dai har yanzu ana ci gaba da tambayar ko matsalolin Manchester United sun wuce abin da ke faruwa a kujerar koci.

    Carrick ya zama koci na bakwai da United ta sallama tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya, wanda ya jagoranci lashe kofin lig na 20 a shekarar 2013.

    Haka kuma shi ne koci na uku da aka sallama tun bayan da Jim Ratcliffe ya zama mai mallakar wani kaso na kungiyar a shekarar 2024.

  3. Matsalar da ke kewaye da Man City ba ta shafar sakamakonmu in ji Maresca, Manchester City

    Enzo Maresca

    Kocin Manchester City, Enzo Maresca, ya ce ce-ce-ku-cen da ke kewaye da kungiyar ba su ne dalilin koma-bayan da ƙungiyar ke fuskanta a baya-bayan nan ba.

    City ta yi rashin nasara a wasanninta uku a Premier League, lamarin da ya sa ta fara ja da baya a gasar bayan ta fara kakar bana da nasarori bakwai a jere.

    Wannan jerin sakamako ya zo ne a yayin da ake ci gaba da rashin tabbas bayan an sami City da laifin karya dokokin kuɗi na gasar, wanda ka iya haifar da tsauraran hukunci.

    City ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma har yanzu ana jiran wani sabon hukunci kan lamarin, amma Maresca ba ya ganin cewa wannan yanayi na shafar yadda ƙungiyar ke taka leda ko sakamakon wasanninta.

  4. Nottingham Forest: Oliver Glasner na son Liam Delap ya kara ƙaimi, Nottingham Forest

    Oliver Glasner

    Kocin Forest, Oliver Glasner, ya ce Liam Delap na iya cin ƙwallaye 20 a kakar wasa bana, idan ya inganta sauran ɓangarorin wasansa.

    Sabon ɗan wasan da Forest ta saya daga Chelsea kan fam miliyan 50 ya ci ƙwallaye biyu a wasan da suka doke Manchester City a farkon wannan watan.

    Glasner ya ce: "Ina ganin wasan City ya nuna gogewarsa da yadda yake da sauri da gudu da ƙarfin da yake da shi. Kuma tabbas yana iya cin ƙwallo da ƙafar dama da hagu.

    "Amma muna aiki tare da shi kan inganta amfani da damar a cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida saboda yake fahimtar yadda zai ke cin kwallaye a kowanne wasanni.''

  5. Leeds United: Daniel Farke na son kafa tarihi a Stamford Bridge, Leeds United

    Daniel Falke

    Kocin Leeds, Daniel Farke na son ƙungiyarsa ta kawo ƙarshen shekara 27 ba tare da nasara a filin Stamford Bridge ba lokacin da za ta kara da Chelsea ranar Asabar a gasar Premier League.

    Leeds, wadda ta samu nasararta ta farko a kan Manchester United a Old Trafford cikin shekara 45 a watan Afrilu, ba ta taba komawa gida da maki uku ba a gidan Chelsea tun bayan shekarar 1999 kuma ta sha kashi sau tara a ziyara 11 da ta yi a baya bayan nan.

    Chelsea tana matsayi na biyar a teburin gasar Premier League da maki biyu kacal a gaban Leeds mai matsayi na tara, bayan wasanni 10 da fara kakar bana a ƙarƙashin kocinta Xabi Alonso.

  6. An ci tarar Chelsea saboda kalaman cin zarafi da nuna wariya, Chelsea

    Chelsea

    An ci tarar Chelsea fam 150,000 ($196,600), saboda kalaman cin zarafi da nuna wariya da magoya bayanta suka yi a lokacin nasarar da ta samu a gasar FA Cup a kan Charlton Athletic a watan Janairu.

    Kungiyar ta Premier League ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi, sannan kuma an yi mata gargadi tare da kakaba mata wani shirin daukar mataki da wani kwamitin sa ido mai zaman kansa aka tsara, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta sanar.

    An ji kalaman cin zarafin ne kusan a minti na 56 a wasan zagaye na uku a FA Cup.

    Chelsea ta tabbatar da hukuncin sannan ta yi Allah wadai da kalaman batanci da aka yi a cikin wata sanarwa.

    Chelsea ta ce za ta dauki matakan gano mutanen da suka aikata wannan dabi'a tare da daukar matakin da ya dace a kansu idan bukatar hakan ta taso.

  7. Bris ya ce doke Chelsea da Sunderland ta yi ya kara musu kwarin gwiwa, Sunderland

    Le Bris

    Kociyan Sunderland, Regis Le Bris ya ce nasarar da Sunderland ta samu da ci 1-0 a kan Chelsea ta kara musu kwarin gwiwa.

    Kafin hutun wasannin ƙasa da ƙasa, Black Cats ta samu nasara mai wahala a kan Blues a Stadium of Light, inda bugun fenareti da Enzo Le Fee ya ci kwallon da suka samu maki uku a karawar.

    Nasarar ta kawo ƙarshen mummunan jerin wasannin da Sunderland ta yi ba tare da cin wasa ba, inda wasan ƙarshe da ta sami maki uku a Premier League tun bayan doke Fulham a watan Agusta, kuma Le Bris ya bayyana yadda wasan ya ƙara masa ƙwarin gwiwa kafin fafatawar da za su yi ranar Asabar da Aston Villa.

    Sunderland tana matsayi na biyu daga ƙasan teburi kafin wasan da za ta yi da Villa ranar Asabar, yayin da Villa take matsayi na 10, kuma Le Bris ya yaba wa aikin da kocin Villa Unai Emery yake yi.

  8. Arab Football tana goyon bayan takarar Infantino, Fifa

    Infantino

    Kungiyar Union of Arab Football Associations (UAFA) ta sanar cewa tana goyon bayan takarar Gianni Infantino domin sake zama shugaban FIFA.

    UAFA ta ce goyon bayan nata ya samo asali ne daga ƙoƙari da gudunmawar da Infantino ya bayar wajen bunƙasa da haɓaka ƙwallon ƙafa a lokacin mulkinsa.

    Shi dai Infantino na shan suka daga hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, tun daga shirin da shugaban ya yi na tallata wasanni Fifa har da gasar cin kofin duniya ga masu zuba zari masu zaman kansu bayan gasar cin kofin duniya.

  9. George Russell

    Dan tseren Mercedes, George Russell, ya kafa tarihin lokaci mafi sauri a atisaye na biyu a Las Vegas Grand Prix ranar Alhamis, bayan yanayin ya inganta sakamakon ruwan sama da ya hana direbobin yin bajinta a atisaye na farko.

    Russell, wanda ya lashe tseren a titin Strip a shekarar 2024, ya zagayen titin birnin mai nisan kilomita 6.2 cikin minti 1 da dakika 47.272 a ƙarshen atisaye na biyu, yayin da fili ke ƙara bushewa.

  10. Shelton ya sha wahala kafin ya buge Jodar a ATP Finals, Kwallon tennis ATP Finals

    Tennis

    Ben Shelton ya sha wahala wajen doke Jodar domin matsowa kusa da wasan kusa da na ƙarshe a ATP Finals.

    Dan wasa mai matsayi na huɗu a duniya, ya yi fafatawa sama da sa’o’i biyu kafin ya doke ɗan ƙasar Spain, Rafael Jodar da ci 7-6(8), 7-5 a ATP Finals ranar Alhamis domin matsowa kusa da samun gurbi a cikin huɗun ƙarshe.

    Dan wasan da ya kai karawar ƙarshe a US Open ya kuma amfana daga nasarar da Alexander Zverev, wanda ya riga ya tabbatar da tsallakewa, wanda ya samu nasara a kan ɗan ƙasar Faransa, Arthur Fils, da ci 6-4, 7-6(6). Fils ya kasance yana buƙatar nasara biyu kai tsaye domin ya tsallake a madadin Shelton.

  11. Farashin tikitin kallon tseren Las Vegas Grand Prix ya fadi wanwar, Formula 1

    Formula 1

    Farashin tikitin gasar Las Vegas Grand Prix da za a yi a ranar Asabar na kan hanyar zama mafi ƙasa tun bayan da Formula One ta fara zuwa Strip a shekarar 2023, kamar yadda dandalin sayar da tikiti na TickPick ya bayyana, yayin da rashin gasa mai zafi ta neman lashe kofin duniya da kuma sanyin yanayi suka rage buƙata.

    Matsakaicin farashin tikitin ranar tseren ya kai dala 781, ƙasa da dala 889 da aka biya a bara da kuma ƙasa da dala 1,214 da aka biya a karon farko a shekarar 2023, a cewar TickPick.

  12. Tashima ya soke Fifa kan yadda ta soke jan katin Balogun na Amurka, Fifa

    Tashima

    Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Japan, Kozo Tashima, ya sanar a ranar Juma’a cewa yadda aka tafiyar da batun jan katin Folarin Balogun a World Cup ne ya sa ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban FIFA don kalubalantar Gianni Infantino.

    FIFA ta dakatar da hukuncin hutun wasa ɗaya da aka yi wa Balogun bayan jan katin da ya samu a watan Yuli, wanda ya ba ɗan wasan Amurka damar buga karawa da Belgium, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya roƙi Shugaba Infantino da kansa ya sake duba hukuncin.

  13. Wanda ya dauki bidiyon atisayen Man United ya bayar da hakuri, Manchester United

    Pochettino

    Matukin jirgi maras matuƙi (drone) da ya ɗauki bidiyon atisayen Manchester United a wannan makon ya ba da haƙuri, yana mai cewa "babban kuskure ne kan abinda ya aikata", kuma ya cire bidiyon daga tasharsa ta YouTube.

    Ya ce manufarsa ita ce ɗaukar hoton Mauricio Pochettino cikin kayan atisaye na United domin magoya baya su gan shi a karon farko.

    Yanzu ya ce duk da cewa ɗaukar bidiyon ba laifi bane, amma ya kasance "ba daidai bane a ɗabi'ance".

  14. Watakila Saliba ya buga wa Arsenal wasan Newcastle United, Arsenal

    Willima Saliba

    Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya tabbatar da cewa mai tsaron baya, William Saliba zai kasance a shirye domin buga wa kungiyar tamaula a karon farko a wannan kakar yayin da zakarun Premier League za su je gidan Newcastle a wasan mako na 11 a St James Park.

    Saliba ya yi jinya saboda raunin ciwon baya tun bayan da ya buga wa Faransa wasa a karawar kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a watan Yuli.

  15. An raba jadawalin kwata fainal a Nations League, Nations League

    Harry Kane

    An raba jadawalin wasannin kwata-fainal na Nations League na bana.

    Ingila za ta kara da Norway a watan Maris, inda za a buga wasa na biyu a Wembley.

    Wanda ya yi nasara daga wannan karawa zai haɗu da Belgium ko Jamus a wasan kusa da na ƙarshe a watan Yuni.

    Wales za ta fafata a wasan neman tsira daga faɗuwa a matakin gida da waje da Slovenia domin sanin ko za ta ci gaba da zama a mataki na farko a Nations League, kuma tawagar Craig Bellamy za ta karɓi baƙuncin wasa na biyu.

    Jamhuriyar Ireland kuma za ta kara da Croatia a wasan neman tsira daga faduwa.

    Ga yadda aka raba jadawalin:

    Nations League quarter-finals:

    • Spain v France
    • Norway v England
    • Netherlands v Portugal
    • Belgium v Germany

    Nations League semi-finals:

    • Netherlands/Portugal v Spain/France
    • Belgium/Germany v Norway/England

    Group A/B play-offs:

    • Bosnia and Herzegovina v Denmark
    • Hungary v Serbia
    • Republic of Ireland v Croatia
    • Slovenia v Wales

    Group B/C play-offs:

    • Cyprus v North Macedonia
    • Estonia v Romania
    • Faroe Islands v Georgia
    • Belarus v Israel

    .

  16. Wasannin damben gargajiya na Ado Bayero Square, Damben gargajiya

    Damben gargajiya

    Sakamakon damben gargajiya da aka dambata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

    A damben mazaje an sha kasa, inda Dogon Messi ya buge Mai Karfin Ebola, Bille ya yi nasara a kan Shagon Cika, Mai Karfin Aliyu ya doke Autan Ebola, Mai Karfin Ebola ya buge Bahagon Raamadan.

    Sauran sakamakon wasannin Shagon Dogon Messi ya doke Bisallah, Mai Karfin Ebola ya buge Dogon Shagon Audu da kuma canjaras tsakanin Mahaukacin Shagon Babba da Mai Karfin Ali Zuma

  17. Tvhouameni zai ci gaba da taka leda a Real Madrid zuwa 2032, Real Madrid

    Dan wasan Real Madrid, Aurelien Tchouameni ya amince da sabon kwantiragin shekara shida, kamar yadda kungiyar Sifaniya ta sanar ranar Alhamis.

    Kenan zai ci gaba da taka leda har zuwa karshen kakar 2032, wanda tun farko yarjejeniyarsa za ta kare a 2028.

    Ya buga wasa 10 a Real Madrid a wannan kakar, wanda ya yi jinya da ta kai bai yi wasa hudu ba.

    Dan kwallon tawagar Faransa ya koma Real Madrid daga AS Monaco a shekarar 2022 kan yarjejeniyar Euro miliyan 80 ($88m).

    Haka shima Arda Guler dan wasan tawagar Turkiya ya sanya hannu kan sabon kwantiragin a Real Madrid zuwa shekara shida a ranar Laraba.

  18. Kompany zai koma jan ragamar Bayern Munich ranar Juma'a, Vincent Kompany

    Vicent Kompany

    Kocin Bayern Munich, Vincent Kompany, ya yi godiya ga goyon bayan da ya samu, bayan rashin lafiyar da ta same shi a ƙarshen watan Oktoba.

    Mai shekaru 40 ya faɗi a lokacin atisayen matasan Bayern Munich ranar 23 ga watan Oktoba, daga baya aka tabbatar yana fama da matsalar kumburin membrane da ke rufe kwakwalwa.

    Kompany ya rasa wasa biyar da Bayern ta buga, amma an gan shi a cibiyar horaswa ta kungiyar a ranar Talatar da ta gabata, kuma ana sa ran zai dawo bakin aiki a wasan gida da Cologne ranar Juma’a.

    Bayern ta dawo daga hutun wasannin ƙasa da ƙasa tana jan ragamar teburin Bundesliga da maki 21, inda take gaban Borussia Dortmund da bambancin ƙwallaye, yayin da yanzu za ta kara da Cologne wadda ke ɗan sama da yankin faɗuwa.

  19. Pochettino ya bukaci yan wasa su dawo da martabar Man United, Manchester United

    Mauricio Pochettino

    Mauricio Pochettino ya kalubalanci Manchester United da ta dawo da ɗabi’ar yin nasara, bayan da zai fara aikinsa a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar.

    Dan ƙasar Argentina ya karɓi aiki ne a lokacin da United ke cikin ukun ƙarshe a teburin Premier League, amma ya jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali kan damar da kungiyar keda ita maimakon halin da take ciki a yanzu.

    Pochettino zai jagoranci wasansa na farko ne lokacin da United za ta je gidan babbar abokiyar hamayyarta, Liverpoolr anar Lahadi a wasan Premier League mako na 10.

    United ta samu nasara ɗaya kacal a karawa 10 da fara babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, kuma ƙungiyar ta fuskanci suka a fannoni da dama.

    An danganta kungiyar da yiwuwar sayen sabbin 'yan wasa a kasuwar cinikayyar yan wasa da za ta ci a cikin watan Janairu, amma Pochettino ya ce zai ba yan wasan da ake da su a yanzu haka cikakken goyon baya.

    Ya ce sha'awarsa ga Manchester United ta samo asali ne tun wasan ƙarshe a Champions League a 1999, wanda ya halarta a matsayin masoyin ƙwallon ƙafa.

    .

  20. Ba Infantino ne kadai zai yi takarar kujerar shugabancin Fifa ba, Gianni Infantiono

    Gianni Infantino

    Shugaban FIFA, Gianni Infantino zai fuskanci ƙalubale a yaƙin neman sake zaɓe daga shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na Faransa, Philippe Diallo da na Japan, Kozo Tashima, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta sanar a ranar Alhamis.

    Tsohon mai tsaron bayan tawagar Switzerland, Ramon Vega, wanda ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a watan da ya gabata, bai kasance cikin jerin 'yan takarar da FIFA ta ambata ba.

    Zaɓen, wanda aka shirya gudanarwa a watan Maris a shekarar 2027, zai kasance karo na farko da Infantino zai fuskanci kalubale, bayan da aka sake zaɓarsa ba tare da hamayya ba a shekarar 2023.

    Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa (FFF), Philippe Diallo, ya sanar da takararsa a ranar Litinin tare da goyon bayan hukumonin tamaula da suke mambobin UEFA da ke cikin kwamitin zartarwa a Majalisar FIFA.