An kashe sama da ƴandaba 30 a Haiti
Yan sanda a Haiti sun ce sun kashe fiye da mutum 30 da ake zargin mambobin ƙungiyoyin masu aikata laifuka ne, yayin wani samamen tsaro da suka gudanar a yammacin babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.
Jami’an tsaron sun fitar da wani bidiyo da ke nuna jirage marasa matuƙa suna kai hare-hare kan wuraren da ake zargin sansanonin ’yan daba ne, da kuma wuraren da ake karɓar kuɗaɗen haraji ba bisa ƙa’ida ba a Martissant.
Martissant wata muhimmiyar hanya ce da ta haɗa babban birnin ƙasar da yankunan yamma da kudancin Haiti.
Wannan shi ne babban samame na farko da aka gudanar a yankin cikin shekaru biyar, tun bayan da ƙungiyoyin masu aikata laifuka suka ƙwace iko da shi.
A halin yanzu, akwai jami’an tsaro da dama da ke gudanar da ayyuka a Haiti, ciki har da rundunar ƙasashe da dama da Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya, da kuma kamfanonin tsaro masu zaman kansu.
Mahukuntan ƙasar dai sun daɗe suna neman ƙarin tallafin tsaro domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar.



























