Majalisar riƙon ƙwarya ta Burkina Faso ta amince da dokar rusa dukkan jam’iyyun siyasa a ƙasar, matakin da ake ganin yana ƙara ƙarfafa ikon gwamnatin soji da ta karɓi mulki bayan juyin mulki.
A zaman majalisa da aka gudanar ranar Litinin, ‘yan majalisa 69 da suka halarta sun kaɗa ƙuri’a baki ɗaya domin goyon bayan kudurin da gwamnati ta gabatar.
Ƙudurin dokar ya kuma soke dokar da ke tsara yadda ake ba da kuɗade ga jam’iyyun siyasa da kamfen din zaɓe.
Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar, Émile Zerbo, ya ce an ɗauki matakin ne domin sake tsara yanayin siyasar kasa, bayan da ya zargi yawaitar jam’iyyu da haddasa rarrabuwar kai da tashin hankali a tsakanin al’umma.
Matakin ya biyo bayan dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa tun shekarar 2022, lokacin da sojoji suka kwace iko ta hanyar juyin mulki.
Jim kadan bayan amincewa da ƙudurin a majalisa, Minista Zerbo ya ce jama’ar Burkina Faso za su yi maraba da wannan mataki, yana mai cewa an ɗauke shi bisa tsarin doka.
Sai dai masana na ganin cewa wannan dokar ta buɗe wa gwamnatin soji damar gudanar da mulki ba tare da wata adawa ba, lamarin da ƙungiyoyin kare haƙƙin dan Adam da dama suka yi Allah-wadai da shi.
A makon da ya gabata, Babban Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkin Dan Adam, Volker Türk, ya bayyana haramta jam’iyyun siyasa a matsayin mataki mara kyau, yana mai kira ga mahukunta su janye wannan hukunci.
Ya kara da cewa maimakon haramta jam’iyyun siyasa da ɗaure mutane saboda fadin ra’ayoyinsu, ya dace gwamnati ta bude fili ga ƙungiyoyin farar hula, ciki har da kungiyoyin jin kai.