Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Muktar Uba, Abdullahi Bello Diginza, Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Ƴar shekara takwas da aka yi wa fyaɗe a Bangladesh ta mutu

    Jami'ai a Bangladesh sun ce yarinyar nan ƴar shekara takwas da aka yi wa fyade a lokacin da ta kai ziyara gidan ƴar uwarta ta mutu.

    Likitoci sun ce yarinyar ta samu bugun zuciya ne a lokacin da ake yi mata aikin ciwon da aka ji mata.

    Wannan lamari da ya faru ya janyo zanga-zanga a faɗin ƙasar inda masu zanga-zangar ke buƙatar a yi wa waɗanda aka kama da aikata wannan aika aika hukunci mai tsanani da ma yi wa duk wanda aka samu da aikata irin wannan cin zarafi ga mata hukunci.

    An kama mutum huɗu da ake zargi da aikata wannan cin zarafi waɗanda wasu daga cikinsu ƴan-uwan yarinyar ne. Ƴan sanda sun dakatar da zanga-zangar a Dhaka.

  2. Ina nan daram a jam'iyyar APC mai mulki - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan APC ne, kuma ya fi so ana alaƙanta shi da ita.

    Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da tsohon kakakinsa, Garba Shehu ya fitar, inda ya ce ba ya so ya bar kowa a cikin ruɗani game da inda yake, domin a cewarsa ba zai taɓa juya wa jam'iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara har ya yi shugabancin ƙasa na wa'adi biyu ba.

    "Ni ɗan APC ne, kuma na fi so ana alƙanta da jam'iyyar, sannan zan yi duk mai yiwuwa wajen tallata jam'iyyar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Netanyahu ya soki rahoton cin zarafin Falasɗinawa a Gaza da Gaɓar Yamma

    Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya zargi rundunar sojin Isra'ila da aikata cin zarafi ta hanyar lalata ga Falasdinawan da ke Gaza da kuma Gabar Yamma da kogin Jordan.

    Cikin wata sanarwa, Mr Netanyahu, ya kira zarge zargen a matsayin zancen kanzon kurege.

    Wakiliyar BBC ta ce firaiminista Benjamin Netanyahu ya mayar da kakkausan martani a game da rahoton inda ya kira hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniyar a matsayin mai kin jinin Yahudawa kuma marar tasiri.

    Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na dauke da bayanan da ya samu daga wajen Falasdinawa maza da samari wadanda suka ce an tsare su tare da sanyasu sun yi tsirara inda aka tsare su tsawon kwanaki a cikin waje mai sanyin gaske.

    Wasu daga cikinsu sun bayar da rahoton cewa an yi musu fyade. break

  4. Al-Sharaa ya amince da sabbin dokokin mulkin ƙasar

    al-Sharaa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban riƙon ƙwarya na Syria ya rattaba hannu kan wata dokar kundin tsarin mulkin ƙasar da ke ɗauke da dokokin da za a tafiyar da gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar nan da shekara biyar masu zuwa.

    Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan kundin zai buɗe 'sabon babi a tarihi ga Siriya" wanda zai maye abin da ya kira ''zalunci da adalci".

    Dokoki za su kasance ƙarƙashin hukunce-hukuncen Musulunci.

    Kwamitin da aka kafa don tsara dokokin, ya ce ya ba da tabbacin ‘yancin faɗin albarkacin baki da yaɗa labarai.

    Kundin ya kuma tanadi walwala da ƴancin mata a fannin shugabanci da tattalin arziki.

    haka kuma a kundin zai maye gurbin tsarin mulkin gwamnatin Assad, wanda aka hamɓarar a watan Disamba.

  5. An kawar da cutar Marburg a Tanzaniya

    Tanzaniya ta ayyana kawo ƙarshen ɓarkewar ƙwayar cutar Marburg bayan shafe kwanaki 42 ba tare da samun ɓular cutar ba a ƙasar.

    Jami'an lafiya sun ce lamarin ya faru ne bayan mutuwar mutum na ƙarshe da aka tabbatar ya kamu da cutar a ranar 28 ga watan Janairu.

    Wannan ne karo na biyu da aka samu ɓarkewar Marburg cikin shekaru biyu. Hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba da haɗin kan da aka samu tsakanin hukumomin Tanzaniya da jami'an lafiya da kuma abokan aikinsu na duniya.

    Cutar Marburg mai kisa, da ke yi wa jijiyoyin jini illa, tana yaɗuwa idan aka taɓa gumin mai ɗauke da cutar.

  6. Peter Obi ya kai wa gwamnan Bauchi ziyarar tuntuɓa

    Gwamnan Bauchi

    Asalin hoton, Bala Mohammed/X

    Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya kai ziyarar tuntuɓa ga gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

    Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a lokacin ziyarar sun tattauna batutuwa da dama da suka danganci haɗin kai da yaƙi da rarrabuwar kawuna.

    Gwamnan ya ce tattaunawar tasu ta ƙara ƙarfafa kishin ƙasa domin shimfaɗa tafiyar da ya ce ''za ta kyautata makomar ƙasar''.

    Rahotonni sun ce ƴansiyasar biyu sun yi ganawar sirri a tsakaninsu, kafin daga baya a bar ƴanjarida su shiga.

    Peter Obi ya bayyana cewa ya kai ziyara zuwa Bauchi ne domin jaje da ta'aziyyar mace-macen da aka yi a jihar, tare da tattauna a batutuwan da suka shafi makomar Najeriya da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fagen siyasar ƙasar.

  7. Trump ya yi barazanar ƙara harajin kashi 200 kan barasar Turai

    Trump

    Asalin hoton, Trump

    Yayin da manyan ƙasashen duniya ke fama da yaƙin cacar baka kan ƙarin harajin kasuwanci tsakaninsu, Shugaban Amurka ya yi barazanar lafta ƙarin harajin kashi 200 kan barasar da aka shigar da ita Amurka daga Turai.

    Shugaba Trump ya yi barazanar ne bayan da ƙasashen Turai da Canada suka yi alƙawarin mayar da martani ta hanyar lafta haraji kan kayyakin Amurka bayan da Trump ya sanya ƙarin harajin kashi 25 kan ƙarafa da sanholon da ke shiga da su ƙasarsa.

    A lokacin d ayake jawabi ga manema labarai a fadar 'White House' kan barazanar ƙasashen, Mista Trump ya ce ''idan suka ɗora mana ƙarin haraji, mu ma za mu lafta musu, ka ga kenan babu batun ƙorafi kan wannan''.

    ''Harajin da za mu ɗora kan barasa sai ya fi muni - don za mu yi mata ƙarin kashi 200 domin mayar da martani,'' a cewar shugaban na Amurka.

    Tuni dai hannayen jarin kamfanonin sarrafa basara suka faɗi sakamakon kalaman na Mista Trump.

  8. Ƴanbindiga sun sace wanda ya lashe gasar karatun al-Qur’ani ta Najeriya

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴanbindiga sun sace mutumin da ya zama zakaran gasar karatun al'qur'ani ta bana tare da danginsa a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara a jihar Katsina.

    Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Hon Musa Ado Faskari ya shaida wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce ƴanbindigar sun sace Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da mahaifinsa da ƴan'uwansa a lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci fadar gwamnatin Katsina inda gwamna ya karrama gwarzon.

    Hon. Musa Faskari ya ce gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ne ya gayyaci , Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da iyalansa ciki har da mahaifinsa a ƴan'uwansa, domin karrama shi bisa nasarar da ya samu ta zama gwarzon gasar karatun al-qur'ani da aka kammala a jihar Kebbi.

    ''A kan hanyarsu ta komawa gida ne, sun baro Funtua a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara , ƴanbindiga suka tare su tare da yin garkuwa su duka, sai mutum guda da ya samu nasarar kuɓuta'', in ji shugaban ƙaramar hukumar.

    Ya ce lamarin ya rutsa da aƙalla mutum bakwai - waɗanda duka dangin juna ne, sai abokin gwarzon gasar guda, wanda shi ma ya halarci taron karramawar.

    Ya ƙara da cewa hukumomi na ci gaba da neman mutanen domin kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.

  9. Ƙaramar yarinyar da aka yi wa fyaɗe a Bangladesh ta rasu

    Jami'ai a Bangladesh sun ce ƙaramar yarinyar nan ƴar shekara takwas da aka yi wa fyaɗe a lkacin da ta kai wa yayarta ziyara ta mutu.

    Likitoci sun ce yarinyar ta samu bugun zuciya a yayin da ake yi mata maganin raunukan da ka ji mata.

    Cin zarafin lalatar ya haifar da mummunar zanga-zanga a ƙasar tsawon kwanaki, inda masu zanga-zangar ke buƙatar hukunta waɗanda aka samu da laifin kan mata da ƙananan yara a ƙasar.

    Tuni daia aka kama mutum huɗu, ciki har da dangin yarinyar, kan zargin hannu a laifin.

    Shugaban riƙo na ƙasar, Muhammad Yunus ya buƙaci a gaggauta gano waɗanda suka aikata laifin domin su girbi abin da suka shuka.

  10. An samu ƙaruwar cutar ƙyanda a Turai da Asiya - WHO

    Mai ƙyanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce adadin mutanen da suka kamu da cutar ƙyanda a Turai da tsakiyar Asiya ya kai matakin da ba a taɓa gani ba a cikin fiye da shekara 25.

    WHO ta ce an samu ninkuwar waɗanda suka kamu da cutar a 2024, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata zuwa mutum 128,000.

    Yara ƙananan ƴan ƙasa da shekara biyar ne suka fi yawa cikin waɗanda suka kamu da cutar da kashi 40 cikin 100 na ƙyandar da aka samu a yankin mai ƙunshe da ƙasashe fiye da 50.

    Daraktan WHO na yankin Turai, Hans Henri Kluge ya ce sabbin alƙaluman ƙaimi ne game da gargaɗin cewa rashin riga-kafi na barazana ga kiwon lafiyar duniya.

  11. Gwamnan Kebbi ya ce zai mayar da mutanen da Lakurawa suka raba da garuruwansu

    Gwamnan Kebbi

    Asalin hoton, Kebbi State Gov/X

    Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa ya raba da muhallansu a jihar cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suke dace domin mayar da su garuruwansu.

    Nasir Idris ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar.

    Gwamnan ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mutanen tare da ganewa idonsa halin da suke ciki, domin sanin matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka, a cewar wata sanarwar da gwamnatin ta fitar.

    Al'umomin da suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke da kuma Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin.

    A ranar Asabar ne wasu mahara da ake kayuatat zaton na ƙungiyar Lakurawa ne suka ƙaddamar da wasu hare-hare a kauyukan tare da kashe mutum 11 da ƙona ƙauyukan.

  12. Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SDP - El-Rufai

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam'iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam'iyyar APC da komawa jam'iyyar SDP.

    "Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma'a na faɗa masa cewa zan bar jam'iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba.

    Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa.

    Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi." In ji Malam El-Rufai.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  13. MDD ta zargi sojojin Isra'ila da cin zarafin Falasɗinawa ta hanyar lalata

    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi sojojin Isra'ila da cin zarafin Falasɗinawa ta hanyar lalata a Gaza da kuma Gaɓar Yamma.

    Rahoton ya bayyana mutanen da aka ci zarafinsu, inda wasu - maza da yara - suka bayyana a bainar jama'a, cewa an tsare su tare da ɗaure su tsirara na tsawon kwanaki a cikin yanayin sanyi.

    Da dama sun bayar da rahoton cewa an yi musu fyaɗe.

    Masu bincike n na Majalisar Dinkin Duniya sun ce cin zarafi ya yaɗu sosai kuma ya yi kama da ayyukan marasa tausayi, suna masu nuni da cewa ana aikata cin zarafin ne bisa umarni ko kuma ƙwarin gwiwar jagororin Isra'ila.

    Isra'ila dai ta musanta tare da yin watsi da rahoton - wanda ta bayyana a matsayin abin kunya kuma maras tushe.

  14. Firaministan Pakistan na ziyara a wurin da aka sace fasinjojin jirgin ƙasa

    Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif na ziyara a lardin Balochistan da ke kudu maso yammacin ƙasar, domin duba halin da tsaron da yankin ke ciki bayan mummunan harin jirgin ƙasa da ya haddasa asarar gomman rayuka.

    A ranar Laraba ne sojojin ƙasar suka ce sun kuɓutar da fasinjoji fiye da 300 - da maharan suka yi garkuwa dasu, bayan farmaki kan ƴantawayen - waɗanda suka tare jirgin, sannan suka sace ɗaruruwan fasinjoji.

    Fiye da mutum 50 aka kashe a lokacin harin, 33 daga cikinsu ƴantawayen ne na ƙungiyar 'Baloch Liberation Army'.

    Hukumomin ƙasar sun ce duka fasinjojin da aka kuɓutar da su an garzaya da su asibitin Quetta, babban birnin lardin.

  15. Majalisar Wakilan Najeriya za ta yi muhawara kan rahoton ƙudurin dokar haraji

    Majalisa

    Asalin hoton, NASS

    A yau ne Majalisar Wakilan Najeriya za ta fara tsefe rahoton kwamitin sauraron ra'ayin jama'a kan ƙudirin dokar haraji.

    Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba.

    Hon Tajudeen ya ce majalisar za ta ɗauki tsawon wunin yau, Alhamis tana nazari da muhawara kan sassan ƙudirin dokar daban-daban.

    Kakakin majalisar ya kuma yi kira ga duka mambobin majalisar su halarci zaman domin bayar da tasu gundonmawa kan rahoton kwamitin sauraron ra'ayin jama'ar.

    Tuni dai kwamitin sauraron ra'ayin jama'ar - ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin kuɗi na majalisar, Hon James Abiodun Faleke - ya kammala sauraron jin ra'ayin jama'a inda ya miƙa rahoton nasa a gaban majalisar a ranar Talata

    A watan Oktoban bara ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar da ƙudurori huɗu da suka shafi haraji a gaban majalisun dokokin ƙasar, domin amincewa da su.

  16. Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron ƙasar

    Manyan hafsoshin tsaro

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Majalisar Dattawan Najeriya ta sake buƙatar manyan hafsoshin tsaron ƙasar su bayyana a gabanta a mako mai zuwa, kan ƙaruwar matsalar tsaron ƙasar.

    Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar na ranar Laraba.

    A baya dai majalisar ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron, domin bayani kan matsalar tsaron ƙasar, sai dai ba su halarta ba, wani abu a Sanata Akpabio ya danganta da rashin samun lokaci.

    Shugaban majalisar ya ce a mako mai zuwa manyan hafsohin za su bayyana a gaban majalisar domin bayar da bahasi kan manyan matsalolin tsaro da ke damun ƙasar da irin matakan da suke ɗauka domin magance su.

    Waɗanda gayyatar ta shafa sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla da kuma babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar.

    Sauran sun haɗa da Babban Sifeton ƴansanda, da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya.

    Sojoji

    Asalin hoton, Nigerian Police

  17. Trump ya yi barazanar sake ɗora haraji ga ƙasashen da suka mayar da martani kan harajin ƙarafa

    Hoton Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ƙara ɗora haraji kan ƙasashen da suka mayar da martani kan harajin da ya sanya wa karafa da sanholo da ake shigar da su Amurka.

    Tuni dai Tarayyar Turai da Kanada suka sha alwashin ɗaukar matakan rumuwar gayya.

    Ministan harkokin kuɗin Canada, Dominic LeBlanc ya ce gwamnatin Canada za ta sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wasu kayayyaki da ake shiga ƙasar da su daga Amurka.

    Ƙungiyoyin kasuwanci a Amurka sun yi gargaɗi kan illar da matakan shugaban Amurkan za su iya haifar wa duniya.

  18. Jamus na fargabar faɗawa karayar tattalin arziki bayan matakan Amurka na ƙara haraji

    dd

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban babban bankin Jamus, Joachim Nagel, ya yi gargaɗin cewa matakin da Donald Trump ya ɗauka na sanya haraji kan kayayyakin da ake shigarwa Amurka na iya jefa Jamus cikin ƙangin karayar tattalin arziki.

    An shafe shekaru ana gina tattalin arzikin Jamus ne kan kayayakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare amma yanzu wannan tsarin na fuskantar barazana.

    Mista Nagel ya bayyana goyon bayansa ga shirin shugaban gwamnati mai jiran gado, Friedrich Merz na cire takunkumin ƙarbar bashi don samar da biliyoyin yuro na inganta ɓangaren tsaro da samar da ababen more rayuwa

  19. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.