Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan, amadadin sauran abokan aiki muke cewa mu kwana lafiya

  2. Saudiyya za ta zuba jarin biliyoyin dala a Siriya

    Yariman Saudiyya

    Asalin hoton, Reuters

    Saudiyya ta sanar da wani gagarumin zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a Syria, a yayin da ta ke jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Damascus.

    Ƙasar Saudiyyar ta sanya kuɗin da ya kai dala biliyan biyu wajen gina sabbin filayen tashi da saukar jirage biyu a birnin Aleppo, da kuma dala biliyan ɗaya domin inganta harkokin sadarwa na zamani a Syria.

    Akwai kuma wasu kuɗaɗen da za a sanya a fannin makamashi, da gina gidaje, da kuma samar da sabon kamfanin jirgin sama.

    Gwamnatin Saudiya ta goya wa shugaban Syria Ahmed Al-Sharaa baya, tun bayan da ya maye gurbin hamɓararren shugaba Bashar Al Assad a ƙarshen shekarar 2024.

  3. An kama mutum huɗu da ake zargi da kitsa harin Pakistan

    Ministan harkokin cikin gida na Pakistan ya ce an kama mutum huɗu, da ake zargi da kitsa harin ƙunar baƙin waƙen - da aka kai wani massallacin ƴanShia, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 30 a babban birnin ƙasar Islamabad.

    Mohsin Naqvi ya ce wani ɗan Afghanistan wanda ake ganin shi ne ya jagoranci kitsa harin na daga cikin waɗanda aka kama.

    Ƙungiyar IS, ta ɗauki alhakin kai harin kan masu sallar Juma'a.

    Mutum fiye da 160 ne suka jikkata a harin, wanda ake ganin ya fi kowanne muni a Islamabad tun wanda aka kai a 2008.

  4. Amurka ta ɗaure madugun adawar Sudan ta Kudu shekara 45

    Peter Bijar Ajak

    Asalin hoton, Family Photo

    Wata kotu a Amurka ta yanke wa fitaccen madugun adawar Sudan ta Kudu hukuncin ɗaurin kusan shekara 45 a gidan yari, saboda samunsa da laifin shirin kifar da gwamnatin ƙasarsa.

    An samu Peter Bijar Ajak - ƙwararren masanin tattalin arziki - wanda ya yi karatu a jami'o'in Cambridge da Harvard, da ke zaune a kusa da birnin Washington - da laifin safarar makamai.

    Jami'an Amurka sun ce Mista Ajak ya shirya saye makamai na dala miliyan huɗu daga Am jurka domin kai su Sudan ta Kudu don raba su ga ƙungiyoyin mayaƙa, domin cimma burinsa na zama shugaban ƙasar.

    An kam Ajak a shekarar 2018 a Sudan ta Kudu, inda aka tsare a gidan yari na wata 18.

  5. APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

    Masari

    Asalin hoton, Aminu Bello Masari/X

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa.

    Babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    Jam'iyyar ta saka ranakun 27 da 28 ga watan Maris na wannan shekarar a matsayin ranakun da za ta gudanar da babban taronta na ƙasa.

    Surajudeen Basiru ya ce a yanzu gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar zai yi aiki a matsayin ma'ajin kwamitin babban taron.

    Haka kuma jam'iyyar ta ƙara yawan mambobin kwamitin babban taron daga 73 zuwa 90, domin bai wa masu ruwa da tsaki damar shiga kwamitin.

  6. 'Kwamitin zaman lafiyar Gaza zai yi zamansa na farko'

    Firaministan ƙasar Hungary, Viktor Orban, ya ce kwamitin zaman lafiyar Gaza - ƙarƙashin jagorancin Trump zai yi zamansa na farko nan da mako biyu a birnin Washington.

    To sai fadar gwamnatin Amurka ba ta bayar da bayani game da yiwuwar ganarwa ba.

    An samar da kwamitin ne da nufin sanya idanu kan sake gina Gaza, to sai amma dokokin kwamitin bai ambaci yankin Falasɗinawa ba, a maimakon haka kwamitin ya ayyana kansa a matsayin kishiyar Majalisar Dinkin Dunkiya.

  7. 'Shugabannin Najeriya na samun kimantawa a ƙasashen waje amma an raina su a cikin gida'

    Matar shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Oluremi Tinubu

    Mai ɗakin shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta bayyana damuwa kan yadda ta ce ƴan ƙasar ba sa ƙimantawa da daraja jagororin ƙasar a cikin gida kamar yadda ake yi musu a ƙasashen waje idan sun fita.

    Ta ce abin takaici ne yadda ake zagi da sukar shugabanni a cikin Najeriya, yayin da kuma ake martaba su da kimanta su a ƙasashen waje, saboda irin gudunmowar da suke bayarwa.

    Mrs Remi Tinubu ta zargi ƴansiyasa ta haddasa hakan ta hanyar cusa ƙiyayyar aboikan adawa a zukatan ƴan ƙasar.

    Mai ɗakin shugaban Najeriya na waɗannan kalamai ne bayan da baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya karrama ta a wajen wani taron addu'o'i a birnin Washington DC

    A bainar jama'a Trump bayyana ta a matsayin wadda ake mutuntawa da kimantawa, kuam jagorar ɗaya daga cikin manyan cocin Najeriya.

  8. Attajirin da ya fara kasuwanci da jarin naira 20

    Bayanan bidiyo, Latrsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Yayin da ɗumbin mutane ke fafutikar yadda za su samu jari domin fara sana'a kuma su raine shi har ya bunƙasa, wani attajirin ɗan kasuwa a Abuja ya ce shi da N20 ya fara.

    Alhaji Halliru Buhari ya ce ya kwashe shekaru masu yawa yana ririta jarin nasa kafin ya bunƙasa.

    Cikin wata hira da BBC Alhaji Halliru ya ce ya fara kasuwancinsa ne a lokacin mulkin soji na tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo.

    ''Babban yayanmu ne ya ba ni naira 20 a matsayin jari, kuma wannan jari shi na ririta, inda yanzu nake da jarin fiye da naira miliyan 200'', kamar yadda ya shaida wa BBC

    Ya ƙara da cewa dama a gidansu ya taso ya tarar ana harkar kasuwancin koli.

    ''Tun da farko na fara kasuwanci da mahaifina, daga baya na tasho Kaduna cikin gari wajen babban yayanmu inda ya bani jarin'', in ji shi.

    Ya ce ya fara ne da yawo cikin gari yana tallan kayan kolin nasa a cikin tire, kafin daga baya ya riƙa zuwa garuruwan da ke gefen Kaduna irin su Zankuwa da sauran yankuna.

  9. Amurka na son a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da Rasha a watan Yuni - Zelensky

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Amurka na son kawo ƙarshen yaƙin ƙasarsa da Rasha a watan Yuni, inda ya ƙara da cewa an gayyaci ɓangarorin biyu zuwa Amurka domin tattaunawa a mako mai zuwa.

    "Amurka ta ba da shawarar cewa ɓangarorin biyu - Ukraine da Rasha - a karon farko su haɗu a Amurka, wataƙila a Miami, a cikin mako guda. ''Mun tabbatar da halartar mu," in ji shi.

    Kawo yanzu dai babu wani ƙarin haske daga Washington ko Moscow, amma shugaban Amurka Donald Trump ya yi ta ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikicin tun bayan hawansa karagar mulki sama da shekara guda da ta wuce.

    A halin da ake ciki kuma, Rasha na ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin samar da makamashin Ukraine - wanda ke haifar da rashin wutar lantarki a sassan ƙasar a daidai lokacin da ake fuskantar tsananin sanyin hunturu.

  10. Shettima ya kai ziyara Kwara bayan mummunan harin jihar

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Fadar Shugaban kasa

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Kwara inda mahara suka kashe gomman mutane cikin makon nan.

    Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ta ce Shettima ya kai ziyarar ce bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu.

    “Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa ya kai ziyarar jaje jihar da kuma duba halin da take ciki tare da miƙa sakon jaje a madadin gwamnatin tarayya,,' in ji sanarwar.

    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya tarbi mataimakin shugaban ƙasar a lokacin ziyarar.

    A ranar Talata da daddare ne wasu mahara suka far wa ƙauyen Woro da Nuku da ke yankin ƙaramar hukumar Kaiama tare da kashe fiye da mutum 70.

  11. MDD da Amurka sun yi alla-wadai da harin da aka kai wa ma'aikatan jin ƙai a Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da harin da wani jirgin sama mara matuƙi da aka kai kan motocin agaji ɗauke da abinci ga iyalan da suka rasa matsugunansu a jihar Kordofan ta Arewa a ƙasar Sudan a ranar Juma'a, wanda ya kashe aƙalla mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

    Ita ma Amurka ta yi tir da harin, tana mai cewa ba za ta lamunci kai hare-hare kan ma'aikatan jin ƙai da kuma tallafin abincin da Amurka ke bayarwa ba.

    Motocin na shirin samar da abinci na duniya WFP sun fito ne daga Kosti domin kai agajin abinci kusa da babban birnin jihar, El Obeid, lokacin da aka far musu.

    A cewar Majalisar Dinkin Duniya, motocin sun kama wuta, inda suka lalata kayan abinci da ake jigilar su domin kai ɗauki.

    Harin dai ya biyo bayan wani harin da aka kai a farkon makon nan kusa da wata cibiyar WFP da ke Yabus a jihar Blue Nile, inda aka jikkata wani ma'aikacin jin ƙai.

  12. Trump ya yi barazanar sanya haraji kan ƙasashen da ke hulɗa da Iran

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta yi barazanar sanya ƙarin haraji kan ƙasashen da ke ci gaba da kasuwanci da Iran.

    Dokar, wadda aka kafa ranar Juma'a, ba ta bayyana adadin harajin da za a iya sanyawa ba, amma yana amfani da kashi 25 cikin 100 a matsayin misali.

    Ta ce harajin zai shafi kayayyakin da ake shigowa da su Amurka daga kowace ƙasa da "ke saye ko shigar da kaya ko kuma shigo da su daga Iran." Trump dai bai ce uffan ba kai tsaye kan wannan umarni amma ya sake nanata cewa "babu makamin nukiliya" ga Iran a lokacin da yake magana daga jirgin saman 'Airfoce one' a daren Juma'a.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin manyan jami'an Amurka da na Iran a ƙasar Oman, biyo bayan makonnin da ɓangarorin biyu suka kwashe su na yi wa juna barazana.

  13. Mutum 24 sun mutu bayan harin RSF a yankin Kordofan na Sudan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla mutum 24 da suka haɗa da yara takwas ne dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kashe a wani hari da suka kai kan wata mota ɗauke da fararen hula da suka rasa matsugunansu a jihar Kordofan ta Arewa ta Sudan.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, kungiyar likitocin Sudan ta ce an kai hari kan motar ne a yankin Dubeiker yayin da fararen hula ke tserewa tashin hankali a Kordofan ta Kudu.

    Ƙungiyar likitocin ta ce a cikin yaran da aka kashe, akwai jarirai biyu, an kuma bayar da rahoton wasu mata da dama daga cikin waɗanda suka mutu.

    An kai waɗanda suka jikkata zuwa Al-Rahad domin yi musu magani, inda aka ce ma’aikatan lafiya na cikin mawuyacin hali saboda ƙarancin kayan aiki da kuma munanan yanayin jin kai.

    Likitocin Sudan sun bayyana harin a matsayin wanda ya saba wa dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa.

  14. Canada da Faransa sun buɗe ofishin diflomasiyya a Greenland

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Canada ta buɗe ofishin diflomasiyyanta na farko a tsibirin Greenland a wani gagarumin yunƙurin nuna goyon baya sakamakon barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na karɓe ikon yankin.

    Tawagar manyan jami'an ƙasar Canada da suka haɗa da Gwamna Janar Mary Simon, da ministar harkokin wajen ƙasar Anita Anand, sun yi tattaki zuwa Nuuk ranar Juma'a domin buɗe ƙaramin ofishin jakadancin Canada a hukumance.

    A wani bikin daga tuta, Anand ta ce ƙaramin ofishin na nuna alamar irin daɗewar da ƙasar Canada ta yi tana "tsaye tare da al'ummar Greenland da Denmark".

    Ziyarar tasu ta zo ne a daidai lokacin da jami'an Faransa suka yi irin wannan balaguron, inda suma suka buɗe na su ofishin jakadancinsu a yankin.

    Matakan na Canada da na Faransa dai na nuni ne da yanayin yadda ƙasashen duniya ke ƙara faɗaɗa ayyukan diflomasiyya a Greenland.

    Kafin zuwan waɗannan ƙasashen biyu, Iceland da Amurka ne kaɗai su ke da ofisoshin jakadancin a Nuuk.

  15. Gimbiyar masarautar Norway ta nemi afuwa kan alaƙarta da Epstein

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gimbiyar masarautar Norway Mette-Marit ta nemi ‘Cikakkiyar afuwa’ daga ƴan ƙasar game da alaƙar da ke tsakaninta da attajirin da aka samu da laifin lalata da ƙanana yara, marigayi Jeffrey Epstein, bayan da aka bankaɗo cewa sun yi musayar saƙonni na tsawon shekara uku.

    “Ina kuma ba da hakuri kan halin da na sanya gidan sarauta a ciki, musamman Sarki da Sarauniya,” in ji ta a wata sanarwa da ta fitar bayan kwanaki da dama na matsin lamba kan batun.

    Sarki Harald V da Sarauniya Sonja, ba su yi tsokaci ba kan lamarin ba.

    Ɗaruruwan saƙonnin imel da aka yi musaya daga 2011 zuwa 2014 tsakanin Epstein da gimbiyar sun fito fili ne a cikin tarin bayanan da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta fitar a makon da ya gabata.

    Wasu sakonnin sun ƙunshi shiye-shiyen ganawa ido da ido tsakaninsu, kuma sun bayyana cewa ta yi kwanaki huɗu a gidan Epstein na Palm Beach da ke jihar Florida a lokacin da ba ya nan.

    A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, fadar masarautar ta ce gimbiyar ta yi matuƙar baƙin cikin cewa ta kasa gane asalin halin Epstein tun da wuri.

  16. Trump ya cire bidiyon da ke nuna ɓatancin launin fata ga Obama

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya cire wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta wanda ke nuna wariyar launin fata ga Barack Obama da Uwargidansa Michelle inda aka nuna su a matsayin birai.

    Hotonunan sun kasance a ƙarshen wani bidiyo na daƙiƙa 62 da ke iƙirarin an tafka maguɗin zaɓe a zaben shugaban ƙasa na 2020.

    Da yake magana da manema labarai a ranar Juma'a, Trump ya ce: "Ban yi kuskure ba". Ya ƙara da cewa farkon bidiyonne kawai kafin wani ma’aikaci ya wallafa shi kuma bai san yana ɗauke da wannan hoton na Obama ba.

    Sanata Tim Scott na jam'iyyar Republican, ya yi kira ga shugaban kasar da ya cire bidiyon, yana mai bayyana shi a matsayin "abin nuna wariyar launin fata mafi muni da na gani daga fadar ta White House".

    Bayan sukar da fadar White House ta sha kan lamarin, ciki har da dsaga wasu ƴan majalisar dattawan ƴan jam'iyyar Republican, an cire bidiyon daga shafin Trump na dandalin ‘Truth Social’ inda aka ce wani jami’in gwamnatin ne ya wallafa bidiyon bisa ‘kuskure’.

  17. Za mu ci gaba da tattaunawa da Amurka – Gwamnatin Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan jami'an Amurka da na Iran na shirin ci gaba da tattaunawa bayan ganawar da suka yi ƙasar Oman kan batutuwan da ya haifar da fargabar ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen.

    Ministan harkokin waje na ƙasar Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar da aka shiga tsakani ta kasance "mafari mai kyau", kuma an mayar da hankali kan ''batun nukiliya ne kaɗai'' .

    Ya ƙara da cewa a yanzu masu tattaunawa za su koma manyan biranen ƙasashensu domin tuntubar gwamnatocinsu.

    Gabanin tattaunawar, jami'an Amurka sun ce suna son tattaunawa kan makamai masu linzami da Iran ke yi da kuma zargin da ta ke yi ma ta na goyon bayan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a yankin, wanda ya nuna gibin da ke tsakanin matsayin ƙasashen.

    Gwamnatin Amurka dai ba ta ce komai kan batutuwan da aka tattauna ba.

    Tattaunawar ta kai tsaye da aka yi a birnin Muscat ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jibge sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya domin mayar da martani ga mumunar murƙushe masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Iran a faɗin ƙasar a watan da ya gabata, wanda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka ce ya kashe dubban mutane.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.