Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 2 zuwa 8 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 2 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Agusta 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu, Abdulrazzaq Kumo, da Umar Mikail

  1. Chelsea ta amince Jackson ya bar ƙungiyar

    Nicolas Jackson

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan gaba na Chelsea Nicolas Jackson ya cimma yarjejeniya da kulob ɗin domin komawa wata ƙungiyar.

    Ɗanƙwallon na ƙasar Senegal ya yi atasaye shi kaɗai a yau Juma'a yayin da ake bayar da rahoton Newcastle na sha'awar ɗaukar sa saboda gaza samun Benjamin Sesko.

    Ba a saka shi cikin tawagar da za ta kara da Bayer Leverkusen a wasan sada zumunta.

    Tuni Chelsea ta ɗauki 'yanwsan gaba biyu a bazarar nan - Joao Pedro daga Brighton da kuma Liam Delap daga Ipswich Town.

    Ƙungiyar na fatan samun ninki biyu na fan miliyan 32 da ta kashe waje sayensa a 2023 daga Villareal ta Sifaniya, kuma a watan Satumban 2024 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara tara.

  2. Burnley ta sayi Broja daga Chelsea

    Armando Broja

    Asalin hoton, EPA

    Burnley ta kammala ɗaukar Armando Broja daga Chelsea kan adadin kuɗin da ba a bayyana ba, amma an yi imanin sun kai fan miliyan 20.

    Ɗanwasan na ƙasar Albania mai shekara 23 ya amince da kwantaragin shekara biyar kuma shi ne na biyu da ta ɗauika a makon nan daga Chelsea bayan Lesley Ugochukwu.

    "Lokaci ne da ya dace na dawo wannan kulob ɗin kafin fara kakar wasa ta bana. Na ƙagu na fara taka leda," in ji Broja.

    "Ina jin daɗi, kuma a shirye nake game da ƙalubalen da ke tattare da taka wa ƙungiyar leda."

    Burnley za ta fara wasan Premeir League da Tottenham ranar 16 ga watan Agusta.

  3. El-Kanemi ta garin Maiduguri ta sayi 'yanwasa 17

    El-Kanemi Warriors

    Asalin hoton, NPFL

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafga ta El-Kanemi mai buga gasar firimiyar Najeriya ta NPFL ta ɗauki 'yanwasa 17 a shirye-shiryen fara kakar wasa ta 2025-26.

    A makon da ya gabata ne aka ƙaddamar da tawagar 'yanwasan a birnin Maidguri na jihar Borno.

    Mai magana da yawun kulob ɗin ya ce tuni aka kammala yi wa 'yanwasan rajista kuma suka zama 'yan gida kafin fara gasar ranar 22 ga watan Agusta.

    El-Kanemi ta ƙare a mataki 16 a kakar wasa ta 2024-25 da aka kammala, inda ta ci wasa 12 da rashin nasaea 13 da kuma canjaras 13.

    Jerin 'yanwasan da ta saya:

    Daddy Abdulrahman - daga Shooting Stars Sports Club

    Habila David – daga Hapoel Ramat Gan (Israel)

    Iddrisu Ibrahim (gola) – daga Kano Pillars FC

    Lawal Tosin – daga Shooting Stars FC

    Abbas Yakubu – daga ABS FC, Ilorin

    David Idaiye – daga Barau FC

    Akinyemi Ayodele – daga Legacy FC

    Sule Kabiru John – daga Turbo Touch FC

    Muritala Dagbo – daga ASVO

    Otuyiga Hakeem (gola) – daga Akwa United

    Akekoromowei Godspower – daga Inter Lagos

    Salisu Ibrahim (Nasara) – daga FC Sumorgan

    Suleiman Badaru – daga FC Geshwills

    Zakka John – daga Doma United

    Mas’ud Danjuma – daga Remo Stars FC

    Sale Bunu – daga Setraco FC

    Jonas Emmanuel – daga Niger Tornadoes FC, Minna

  4. Matashiya Mboko ta lashe Canadian Open a hannun Naomi Osaka

    Mboko

    Asalin hoton, EPA

    Matashiya Victoria Mboko ta lashe gasar Canadian Open ta ƙwallon Tannis a karon farko bayan ta doke tauraruwar wasa Naomi Osaka a wasan ƙarshe.

    Wasa biyu a jere kenan 'yar shekara 18 ɗin tana nuna bajintar farfaɗowa daga rashin nasara, inda ta doke Osaka da ci 2-6 6-4 6-1 da tsakar dare.

    Mboko ta shiga 2025 a matsayi na 333 a jerin mafiya ƙwarewa a ƙwallon Tennis amma ta koma ta 24 bayan samun nasarar a ƙasarta ta haihuwa.

    "Na ji daɗi matuƙa da na samu damar buga wasa a Montreal karon farko. Na ɗan ji tsoro da farko, amma kuma ban yi ƙasa a gwiwa ba," in ji Mboko.

  5. Nwaneri ya tsawaita zamansa da shekara biyar a Arsenal

    Ethan Nwaneri

    Asalin hoton, PA Media

    Matashin ɗanwasan Arsenal Ethan Nwaneri ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekara biyar da za ta riƙe shi a gasar ta Premier League har zuwa 2030.

    Asalin kwantaragin mai shekara 18 ɗin zai ƙare ne a watan Yunin 2026.

    "Hakan abu ne muhimmi a wajena, na yi matuƙar farin ciki da samun kwantaragin. Ina ɗaukar Arsenal kamar gidanna kuma inda zan samu cigaba sosai," a cewarsa.

    "Ina cikin farin ciki sosai. Ina kallon wannan a matsayin cikakkiyar kakata ta farko a tawagar."

    Nwaneri ya ja hankali lokacin da ya zama mafi ƙanƙantar shekaru da ya buga wasa a gasar Premier League yana da shekara 15 da kwana 181 a karawa da Brentford a watan Satumban 2022.

  6. Aston Villa ta kammala ɗaukar Guessand daga Nice ta Faransa

    Evann Guessand

    Asalin hoton, Getty Images

    Aston Villa ta kammala ɗaukar ɗanwasan gaba Evann Guessand daga ƙungiyar Nice ta Faransa kan yuro miliyan 26 da kuma miliyan 4.3 na tsarabe-tsarabe.

    Ɗan ƙasar Ivory Coast ɗin mai shekara 24 ya ci ƙwallo 12 a kakar da aka kammala kuma shi ne ma gwarzon ɗanwasan ƙungiyar na kakar bayan ta ƙare a matsayi na huɗu a teburin Ligue 1.

    Ɗanƙwallon zai ƙatrfafa tawagar Unai Emery, yayin da ake kallon Ollie Watkins a matsayin mai zira ƙwallo tilo a tawagar kafin yanzu.

    "Lokacin da na ji kulob ɗin na nema na ban yi wata-wata ba," in ji Guessand.

    "A shirye nake na bayar da cikakkiyar gudummawata. A kowane wasa, a kowane lokaci."

  7. Maddison zai shafe akasarin kaka mai zuwa yana jinya

    Maddison

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan tsakiya na Tottenham James Maddison zai yi jinyar watanni da dama sakamakon raunin da ya ji a ƙoƙon gwiwarsa.

    Majiyoyin sun shaida wa BBC cewa za a yi wa ɗan ƙasar Ingilan tiyata da za ta sa ya shafe mafi yawan kakar baɗi yana jinya.

    Ɗanƙwallon mai shekara 28 ya ji raunin ne a wasan sada zumunta da suka kara da Newcastle a Koriya ta Kudu ƙarshen makon da ya gabata.

    Mai horarwa Thomas Frank ya tabbatar bayan tashi daga wasan cewa Maddison ya sake turguɗe gwiwar da ta hana shi buga wasan ƙarshe na gasar Europa da suka lashe a watan Mayu.

    Maddiosn ya koma Tottenham daga Leicester City a 2023, inda ya ci ƙwallo 12 cikin wasa 45 a kakar da aka kammala.

  8. Man United ta amince da biyan fan miliyan 73 don ɗaukar Sesko

    Benjamin Sesko

    Asalin hoton, EPA

    Manchester United ta amince da biyan fan miliyan 73.7 (yuro miliyan 85) domin ɗaukar ɗanwasan gaba Benjamin Sesko daga ƙungiyar Red Bull Leipzig.

    Yarjejeniyar ta tanadi biyan miliyan 66.3 nan take, yayin da za a biya sauran a matsayin tsarabe-tsarabe.

    Sesko mai shekara 22 zai kammala komawa filin wasa na Old Trafford bayan gwada lafiyarsa.

    Ya ci wa RB Leipzig ƙwallo 39 cikin wasa 87, kuma komawarsa United rashi ne babba ga Newcastle wadda take ƙoƙarin rasa ɗanwasan gabanta Alexender Issak zuwa Liverpool.

    Tuni Man United ta sayi 'yanwasa kamar Matheus Cunha da Bryan Mbeomo a wannan bazarar kan jimillar kuɗi fan miliyan 130.

    Yanzu haka ta saka ɗanwasan gabanta Rasmus Hojlund a kasuwa kan fan miliyan 30 bayan ya zira ƙwallo 14 kacal cikin kakar wasa biyu.

  9. Kocin Super Falcons Justin Madugu na cikin 'yantakarar Ballon d'Or

    Justin Madugu

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin tawagar mata ta ƙwallon Najeriya, Justin Madugu, ya shiga jerin masu takarar neman kyautar Ballon d'Or ta gwarzon koci ɓangaren mata na 2025.

    Kociyan ya samu shiga jerin ne bayan da ya jagoranci tawagar ta Super Falcons lashe kofin ƙasashen Afirka Wafcon 2024 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci.

    Shi ne karo na 10 da 'yanmatan na Najeriya suke jinjina kofin a tarihi.

  10. Shugaban LAFC ne ya sauya ra'ayina zuwa kulob ɗin - Son

    Son

    Asalin hoton, Reuters

    Son Heung-min ya ce kulbo ɗin Los Angeles FC da ya koma ba shi ne zaɓinsa na farko ba amma "maganar da ya yi" da shugaban ƙungiyar ce ta sauya ra'ayinsa.

    BBC ta fahimci cewa LAFC ta biya kuɗin da ya kai fan miliyan 20 kan tsohon ɗanwasan na Tottenham Hotspur bisa yarjejeniyar shekara biyu da zaɓin tsawaita ta da shekara biyu.

    Kuɗin da aka biya na ɗaukar Son ya zarta mafi yawa a tarihi na fan miliyan 16 da Atlanta United ta biya domin ɗaukar Emmanuel Lath daga Middlesbrough a watan Fabrairu.

    "Burina ne ya cika. LA - gari mai daɗi," a cewar ɗan ƙasar Koriya ta Kudun ranar Laraba.

  11. Al-Hilal ta amince da sayen Nunez daga Liverpool

    Darwin Nunez

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Al-Hilal ta ƙasar Saudiyya ta amince da ɗaukar ɗanwasan gaba na Liverpool Darwin Nunez kan kuɗi yuro miliyan 53.

    Ana sa ran za a gwada lafiyar Nunez nan gaba kafin kammala komawa gasar ta Saudi Pro League.

    Ɗanƙwallon Uruguay mai shekara 26 ya koma Liverpool ne a watan Yunin 2022 daga kulbo ɗin Benfica na Portugal kan fan miliyan 64.

    Nunez ya ci wa Liverpool ƙwallo 40 cikin wasa 143 da ya buga, amma wasa takwas kacal aka fara da shi a gasar Premier League ta kakar da ta gabata, wadda Liverpool ɗin ta lashe.

    Cefanar da Nunez zai bai wa Liverpool damar samun kuɗin sayo ɗanwasan gaba Alexander Isak daga Newcastle a wannan kasuwar.

    Sai dai Newcastle ɗin ta yi watsi da tayin farko na fan miliyan 110 da Liverpool ta miƙa mata a makon da ya gabata kan ɗan ƙasar Sweden ɗin mai shekara 25, yayin da ta yi masa farashi na kusan fan miliyan 150.

  12. Greenwood zai koma taka wa Jamaica leda

    Greenwood

    Asalin hoton, Getty Images

    Mason Greenwood zai daina taka wa Ingila leda domin komawa buga wa Jamaica.

    Greenwood bai buga wa Ingila wasa ba tun Satumban 2020 inda ya buga wasansa kaɗai a fafatawarsu da Ingila. A lokacin an tura shi gida tare da Phil Foden bayan sun saɓa wa dokokin kewaye kai daga cutar korona.

    Bayan Jamaica ta riga ta ba shi fasfo, abin da Greenwood ke jira shi ne amincewar hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila da ta Jamaica domin ya samu buga wa Jamaica a wasanninsu na neman gurbin zuwa kofin duniya a watan Satumba.

    Hakan na cikin tsarin Jamaica da kocinta Steve McClaren ke jagoranta na dawo da duk ƴan ƙasar da suka tashi a Ingila su koma taka wa Jamaica leda.

  13. Ƴan wasan da Chelsea ta yi cinikinsu tun buɗe kasuwa

    Waɗanda ta saya

    Joao Pedro (Ɗan wasan gaba) - £55m

    Jamie Gittens (Ɗan wasan gaba) - £48.5m

    Jorrel Hato (Ɗan wasan baya) - £38m

    Liam Delap (Ɗan wasan gaba) - £30m

    Estevao (Ɗan wasan gaba) - £29.5m

    Dario Essugo (Ɗan wasan tsakiya) - £19.3m

    Waɗanda ta sayar:

    Noni Madueke (Ɗan wasan gaba) - £48.5m

    Joao Felix (Ɗan wasan gaba) - £26m

    Djordje Petrovic (Mai tsaron raga) - £25m

    Bashir Humphrys (Ɗan wasan baya) - £12m

    Kepa Arrizabalaga (Mai tsaron raga) - £5m

    Marcus Bettinelli (Mai tsaron raga) - £2m

  14. 'Sesko ya amince da komawa Man United'

    Benjamin Sesko

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitattun ƴan jaridar wasanni kamar Fabrizio Romano da David Ornstein sun tabbatar da cewa Benjamin Sesko ya amince da komawa Manchester United kuma yanzu haka ƙungiyar na ciniki da RB Leipzig.

    United na yi wa Sesko tayin kwantiragin da shekara shida da zai kai har zuwa 2030.

    A halin yanzu abin da ya rage shi ne Man U ta kammala ciniki da Leipzig.

  15. Tsohon ɗan wasan FC Porto ya rasu

    Jorge Costa

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan FC Porto kuma kyaftin ɗin ta, Jorge Costa ya rasu ranar Talata a filin atisayen ƙungiyar bayan ya samu bugun zuciya.

    Costa wanda ya mutu yana da shekara 53 shi ne ya jagoranci tawagar Porto ta Mourinho wajen lashe kofin zakarun Turai ta Champions League a 2004 sannan ya buga wa Portugal wasanni 50.

    Ɗan wasan na baya ya samu aiki a ƙungiyar, inda ya riƙe matsayi har 16 kafin ya zama daraktan wasanni a kakar wasan da aka kammala.

  16. Gasar CHAN: Senegal ta doke Najeriya

    Eric Chelle

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya ta fara gasar cin kofin ƴan wasan ƙasashen Afirka na cikin gida - CHAN da ƙafar hagu yayin da Senegal ta doke ta da ci 1-0 ranar Talata bayan Cristian Gomis ya zura ƙwallo a minti na 75.

    Hakan na nufin akwai bukatar Najeriya ta taka rawar gani a wasanta da Sudan da kuma Congo a gaba domin cancanta zuwa mataki na gaba daga rukunnin B.

  17. Ruben Dias zai tsawaita yarjejeniyarsa da Manchester City

    Ruben Dias

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan wasan Manchester City Ruben Dias da Nico O'Reilly za su tsawaita yarjejeniyar zamansu a Manchester City.

    A halin yanzu, kwantiragin Dias zai ƙare ne a shekarar 2027 yayin da na O'Reilly zai ƙare a 2028.

    Ruben Dias mai shekara 28 ya koma Man City daga Benfica kan fam miliyan 65 a shekarar 2020 yayin da shi kuwa O'Reilly, mai shekara 20 ya fara taka leda wa Man City ne a kakar wasan da aka kammala.

    City na kuma sa ran sayar da wasu ƴan wasa kafin watan Satumba yayin da Jack Grealish da Kalvin Phillips ke kasuwa.

  18. Wacce rawa Sesko ya taka a kakar wasa da ta gabata?

    Sesko

    Asalin hoton, Getty Images

    Shekaru da dama kenan yanzu Benjamin Sesko na ɗaukar hankalin masoya kwallon ƙafa, amma kakar wasan 2024/2025 ce ya fi rawar gani.

    Ɗan wasan mai shekara 22 ya zura ƙwallo 21 cikin wasa 45 a tsakanin duka gasannin da Leipzig ta buga, sannan ya bayar aka ci shida.

    Huɗu daga cikin ƙwallayen ya zura su ne a Champions League duk da cewa Leipzig ta gaza wuce matakin farko.

    Sesko ya zura ƙwallo 13 cikin wasa 31 a Bundesliga, inda alƙaluma ke nuna cewa yana zura ƙwallo ɗaya bayan kowane minti 184.

  19. United ta gabatar da tayin fam miliyan 74 kan Sesko

    Sesko

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta gabatar da tayin fam miliyan miliyan 65, da za ta iya tashi zuwa miliyan 73.8 idan ɗan wasan ya cimma wasu sharuɗan kwantiragin da zai sanya hannu a kai.

    Zuwa yanzu Leipzig ba ta mayar da martani ba, amma United ta yi imanin cewa wannan kuɗin shi ne ya dace da Sesko, kuma tana ganin cewa ɗan wasan na sha'awar zuwa Old Trafford.

    Ita ma Newcastle ta gabatar da nata tayin kan Sesko kuma tana jiran martani daga ƙungiyarsa.

  20. Kotu ta bayar da belin Thomas Partey

    Thomas Partey

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Ingila ta bayar da belin tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey bayan shigar da ƙararsa bisa zargin laifukan cin zarafi ta hanyar lalata da fyaɗe.

    An zargi ɗan wasan na Ghana da yi wa wasu mata biyu fyaɗe tare da cin zarafin wata daban.

    Lamarin da ake zargi ya faru tsakanin 2021 zuwa 2022 lokacin da yake taka leda a Arsenal.

    Daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ta yanke masa, ta hana Partey yi wa kowace daga cikin matan magana, sannan dole ya sanar da ƴansanda idan zai canja gida ko zai yi tafiya ƙasar waje.

    Mai shekara 32 ya ce ya amince da hukuncin da kotun ta yanke.

    Partey zai sake gurfana a gaban wata kotu a Ingila ranar 2 ga watan Satumba kan wannan zargin.