Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Harin Isra'ila ya kashe Falasɗinawa takwas a lokacin jana'iza a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce hare-haren sama da Isra'ila ta kai sun kashe aƙalla Falasɗinawa takwas.

    Shaidu sun ce an kai harin ne a lokacin da ake gudanar da jana'iza a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat.

    Mai magana da yawun asibitin yankin ya ce kimanin mutum 20 ne suka jikkata sakamakon harin, inda ya ƙara da cewa wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

  2. Kuwait ta ce hare-haren Iran sun jikkata jami'anta

    Kuwait

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Kuwait ta ce hare-haren jirage marasa matuƙa da Iran ta kai ƙasar sun jikkata jami'anta da dama.

    Tun da farko gwamnatin Kuwait ta ce hare-haren sun lalata wata tashar samar da wutar lantarki da kuma wasu cibiyoyin samar da ruwa a ƙasar.

    A nata ɓangaren, Iran ta ce hare-haren da ta kai sun yi niyyar kaisu ne kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Bahrain da Jordan, da kuma Siriya.

    Hare-haren na zuwa ne yayin da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari, inda ɓangarorin biyu ke ci gaba da musayar hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya.

  3. Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP ɓangaren Turaki

    Tanimu Turaki

    Asalin hoton, PDP/X

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin jam'iyyar PDP suka shigar domin tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC, ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Alƙali Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ƙarar. Saboda haka kotun ta ce ba ta da ikon sauraron shari'ar.

    Alƙalin ya ce masu ƙarar sun kasa tabbatar wa kotu cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a madadin jam'iyyar PDP.

    Shugaban kwamitin amintattu na PDP tsagin Turaki ƙarƙashin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin kwamitin ne suka garzaya kotu suna neman a umarci INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Sun kuma buƙaci kotun ta umarci hukumar zaɓen ta wallafa sunayen shugabannin riƙon ƙwaryar a shafinta na intanet.

    Sai dai wani tsagin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shiga shari'ar tare da ƙalubalantar ikon kotun, inda ya ce shi ne shugabancin PDP halastacce, kuma masu ƙarar ba su da hurumin shigar da ita a madadin jam'iyyar.

  4. Sabbin sharuɗɗan da Amurka ta gindaya wa ɗaliban ƙasashen ƙetare

    Sabbin sharuɗɗan da Amurka ta gindaya wa ɗaliban ƙasashen ƙetare

    Asalin hoton, Joe Sohm/Visions of America/Universal Images Group via Getty Images

    Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Shugaba Donald Trump ta sanar da sabbin ƙa'idoji da za su tsaurara dokokin zama ga ɗaliban ƙasashen waje a Amurka.

    Sabbin dokokin, waɗanda za su fara aiki daga watan Satumba, za su kuma taƙaita damar ɗalibai su sauya fannin karatu ko kuma su canza daga wata jami'a zuwa wata.

    A baya jami'o'i na da ikon tsawaita wa ɗalibai izinin zamansu a ƙasar ta Amurka.

    Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ce sabbin matakan za su taimaka wajen daƙile yadda ake amfani da bizar ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba, tare da ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar ci gaba da tantance masu bizar.

    A baya, ɗaliban da ke da biza ajin F-1 da J-1 suna da damar zama a Amurka har sai sun kammala karatunsu, ba tare da ƙayyade musu lokacin zama a ƙasar ba.

    Ga wasu daga cikin sabbin sharuɗɗan da gwamnatin Amurka ta gindaya wa ɗaliban ƙasashen ƙetare:

    • Ba za su iya zama a Amurka fiye da shekara huɗu ba sai sun samu izini daga gwamnatin tarayya
    • Za a takaita damar sauya fannin karatu ko kuma canza jami'a ko kwaleji
    • Ba jami'o'i ne za su yanke shawarar tsawaita wa'adin bizar ɗalibai ba, gwamnatin tarayya ce za ta riƙe wannan iko
    • Bayan kammala karatu, za a bai wa ɗalibi kwana 30 kacal ya bar Amurka ko ya nemi sauyin biza, maimakon kwana 60 da ake bayarwa a baya
    • Za a riƙa sake tantance ɗaliban ƙasashen waje akai-akai
    • Sabbin ƙa'idojin za su fara aiki daga watan Satumba

    Sakataren Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida, Markwayne Mullin, ya ce tsawon shekaru ana bai wa ɗaliban ƙasashen waje damar zama ba tare da wa'adi ba, lamarin da ya ba wasu damar amfani da tsarin wajen ci gaba da yin rajistar kwasa-kwasai domin ƙin barin ƙasar.

    Sai dai yawancin shirye-shiryen karatun digiri na farko a Amurka na ɗaukar shekara huɗu, yayin da karatun digiri na biyu da na digirgir kan ɗauki lokaci mai tsawo.

    Ƙungiyar da ke bai wa jami'o'i shawara kan harkokin ɗaliban ƙasashen waje, ta soki matakin.

  5. An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

    An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutum uku a gaban babbar kotun Ttarayya bisa zarginsu da hannu a sace ɗalibai da malamai daga wasu makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

    Waɗanda ake zargin sun haɗa da Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa, wanda aka fi sani da Yunusa bin Musa, da kuma Shamsu Adamu Sani, wanda ake kira Abu Itisar.

    A ranar 15 ga Mayun 2026 ne wasu masu ɗauke da makamai suka kai hari makarantu uku a jihar Oyo, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai, kuma sun kashe ɗaya daga cikin malaman makarantar, Michael Oyedokun.

    Bayan shafe kwanaki 56 a cikin daji, jami'an tsaro suka kuɓutar da su.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Juma'ar nan ne gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 10 a kan waɗanda ake zargin a gaban kotun da ke Abuja.

    Takardar ƙarar ta ce mutanen uku, waɗanda dukkansu ƴan ƙaramar hukumar Suleja ne a jihar Neja, sun haɗa baki da wasu mutane Muhammad Sani da Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab tsakanin watan Janairu da Mayun 2026 domin yin garkuwa da ɗalibai da malamai a jihar Oyo.

    Ana kuma zarginsu da ɓoye bayanai kan waɗanda ake zargin su ne suka shirya lamarin, da alaƙa da ƙungiyar Darul Salam, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Ansaru, da gwamnatin ƙasar ta ayyana a matsayin ta ta'addanci.

  6. MDD ta yi suka game da hare-haren da aka kai kan gine-ginen a Iran

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana cewa "bai dace" a kai hare-hare kan gine-ginen fararen hula a Iran ba

    Iran ta zargi Amurka da kai hare-hare kan gadoji da cibiyoyin sufuri a ƙasar.

    Mai magana da yawun Sakatare Janar na MDD, Farhan Haq, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa Mista Guterres na ci gaba da nuna matuƙar damuwa kan yadda rikicin tsakanin Iran da Amurka ke ƙara ta'azzara.

    Ya ce Sakatare Janar ɗin ya fi nuna damuwa musamman kan hare-haren da ake kai wa gine-ginen fararen hula a Iran da sauran sassan yankin.

    "Kai hare-hare kan gine-ginen fararen hula ba abin da za a amince da shi ba ne," in ji Farhan Haq.

    Sai dai har yanzu Amurka ba ta tabbatar da zargin da Iran ke yi na cewa ta kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula ba.

  7. Kotun ƙoli ta kwace wasu manyan kadarorin Emefiele

    Godwin Emefiele.

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin ƙwace wasu manyan kadarori bakwai da ake alaƙanta su da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar (CBN), Godwin Emefiele.

    Wannan shari'ar ta soke wani hukunci da Kotun Ɗaukaka Ƙara a Legas ta yanke a baya, inda ta bada umarnin a sake sauraron shari'ar.

    Sai dai kwamitin alƙalai biyar na Kotun Koli ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ibrahim Saulawa ne ya yanke hukuncin, inda ya amince da buƙatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar na soke hukuncin.

    Da wannan hukunci, Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, wanda tun a ranar 1 ga Nuwamban 2024 ya ba da umarnin a ƙwace kadarorin ga gwamnatin tarayya bayan ta ce akwai gamsassun hujjojin da ke nuna cewa an mallake su ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

    Emefiele dai ya ƙalubalanci umarnin ƙwace kadarorin a lokacin, amma EFCC ta ɗaukaka ƙara.

    Kadarorin da kotun ta ƙwace sun haɗa da gidaje biyu da ke kan titin Hakeem Odumosu a Lekki Phase 1 a Legas, wani fili mai faɗin murabba'in mita 1,919.592 a titin Oyinkan Abayomi da ke Ikoyi, wani ƙasaitaccen gida mai lamba 65A Oyinkan Abayomi Drive, da wani gida mai ɗakuna huɗu a Probyn Road da ke Ikoyi.

    Akwai kuma wani katafaren ginin masana'antu da ake ginawa a kan fili mai lamba 22 a Agbor, jihar Delta, da wasu rukunin gidaje takwas na haya a Adekunle Lawal Road da ke Ikoyi, da kuma wani gida da aka gina a kan fili mai faɗin murabba'in mita 2,217.87 a Bank Road da ke Ikoyi.

    Babbar Kotun Tarayya ta kuma ba da umarnin ƙwace dala miliyan 2.45 da takardun hannun jari mallakin kamfanin Queensdorf Global Fund Limited Trust daga gareshi.

  8. Ƙungiyar Kurɗawa a Iraƙi ta zargi Iran da kashe mata mayaƙa tara

    Wata ƙungiyar Kurɗawa a Iraƙi mai adawa da Iran ta ce wani harin jirgi maras matuƙi da roka ya kashe mambobinta tara.

    Ƙungiyar Komola na da mazauni a kusa da arewacin Iraƙi kusa da birnin Sulaymaniyah.

    Mai magana da yawun ƙungiyar ya ce an kai harin ne da sanyin safiyar yau Juma'a kuma gwamnatin Iran ce ke da alhakin kai harin.

    A baya dai Iran ta sha kai hare-hare kan ƙungiyoyin da take adawa da su a Iraƙi sai dai kashe mutanen tara ka iya zama silar da rikicin zai iya caɓewa tsakanin ɓangarorin.

  9. Hare-haren Iran sun lalata tashar lantarkin Kuwait

    ....

    Asalin hoton, ....

    Ƙasar Kuwait ta ce hare-hare ta sama da Iran ta kai ƙasar ya lalata tashar samar da wutar lantari da kuma cibiyoyin ruwa a ƙasar.

    Tehran ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin martanin munanan hare-haren da Amurka ta kai kan gadoji biyar da hanyoyin sufurin jiragen ƙasa da kuma filin jirgi cikin dare.

    Iran ta kuma ce ta kai hare-haren kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Bahrain da Jordan da kuma Siriya.

    Idan har hakan ta tabbata, zai zama karon farko da Iran ta kai babban hari Siriya ƙarƙashin mulkin shugaba Ahmed al-Sharaa, wanda ke ƙoƙarin ganin Siriya ba ta shiga cikin rikicin ba.

  10. An sanya wa sabon babban titin Legas zuwa Calabar sunan Tinubu

    Babban titi

    Asalin hoton, Dr Dípò Awójídé/X

    Gwamnatin Najeriya ta sanya wa babban titin gaɓar teku - da ya tashi daga Legas zuwa Calaba - sunan shugabana ƙasar Bola Tinubu.

    Ministan ayyuka na ƙasar, David Umahi ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne domin nuna yabo ga hangan nesan shugaban ƙasar game da aiki.

    Ya ce ma'aikatar ayyuka ta ƙasar ce ta yanke shawarar sanya wa titin sunan shugaban ƙasar, bayan tuntuɓar jagororin ma'aikatar.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, David Umahi ya ce Shugaba Tinubu ya amince da faɗaɗa aikin titin da kilomita 400.

    Babban titin wanda ya ratsa jihohin Najeriya aƙalla tara ke bakin gaɓar ruwa zai an tsara zai laƙume kuɗi naira tiriliyan 15.

    Titin mai tsawon kilomita fiye da 700 zai tashi daga Legas da kudu maso yammcin ƙasar, zuwa Kalaba da ke kudu maso kudancin ƙasar.

  11. Iran ta gargaɗi ƙasashen Gulf kan bai wa Amurka damar kai mata har

    Abbas Araghchi

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta gargaɗi ƙasashen yankin Gulf kada su bari Amurka ta yi amfani da yankunansu ko sararin samaniyarsu ko kuma gaɓoɓin ruwansu wajen kai hari cikin ƙasar.

    Tehran ta ce irin wannan mataki zai janyo mummunan sakamako ga waɗannan ƙasashe.

    Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Saleh Jokar, ya ce idan Amurka ta yi amfani da yankunan waɗannan ƙasashe wajen kai hari kan Iran, to za su fuskanci mummunar asara.

    A wani ɓangaren kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce sake kakaba takunkumi kan harkokin sufurin ruwa zai zama saɓa wa yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Tehran da Washington.

    Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kuma zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi, tana mai nuni da hare-haren da aka kai wa muhimman cibiyoyin fararen hula da kuma wuraren samar da ayyukan jama’a a matsayin misalai.

    Iran ta ce wuraren da aka kai wa hari sun haɗa da cibiyar lafiya ta rundunar soji ta Brigade na 388 da cibiyar ajiye kayayyaki da Hoveizeh da kuma wasu wurare daban.

    Tehran ta ce wannan ne karo na uku cikin shekara guda da Amurka ta kai mata hari alhali ana tsakan da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.

  12. INEC za ta shirya zaɓen shugaban ƙasa na gwaji

    Shugaban INEC

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana duba yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasar na gwaji, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

    Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar hukumar zaɓen da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

    Farfesa Amupitan ya ce hukumar na wannan shiri ne domin tabbatar da sahihanci da ingancin na'urorin zaɓen, la'akari da ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓukan 2023.

    Ya ƙara da cewa INEC na duba yiwuwar gwada kayayyakin hukumar zaɓen gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe.

    “Muna duba yiwuwar gwada duka kayyaki da na'urorin zaɓenmu, gabanin babban zaɓen da ke tafe, da kuma yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasa na gwaji, domin gwaja ingancin kayayyaki da na'urorin namu,'' in ji shi Farfesa Amupitan.

    Ya ƙara da cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen hukumar na inganta tsarin fasahar hukumar ciki har da tsarin tantance masu zaɓe da hanyar na'ura da amfani da shafin IRev wajen tura sakamakon zaɓe, da tsarin tsaron shafin.

  13. Hukumar tace fina-finai da hisbar Kano sun samu saɓani kan masu dawulodin

    Kano

    Asalin hoton, Abba El-Mustapha/FB

    A jihar Kano, takaddama ta kaure tsakanin hukumar Hisba da kuma hukumar Tace Fina-Finai game da sana'ar tura fina-finai wato downloading.

    Tun da farko dai hukumar Hisbah ce ta fara sanar da haramta sana'ar bisa zargin cewa ana amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.

    To sai dai hukumar Tace Fina-Finai ta yi fatali da wannan matakin tana mai cewa sana'ar halastacciya ce kuma ita ce ke da ikon yi ko hana sana'ar.

    ''Wannan mataki abu da ya kamata a ce mu da su mun zauna mun tattauna a kan makomar yin haka kasancewar mu ke da hurumi da doka ta ba mu na kula da masu wannan sana'a'', a cewar Abdullahi Sani Sulaiman kakakin hukumar.

    ''Akwai wani tsari da muka yi musu na rigima da suke samu tsakaninsu da masu shirya fina-finai da cewa ba za su sake ɗaukar fim ba, sai da sahalewar masu fina- finai,'' in ji shi.

    A nata ɓangare, hukumar Hisba ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-ƙorafe da dama da hukumar ta samu daga al'umma.

    Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen ya shaida wa BBC cewa akwai masu fakewa da sana'ar suna tura wa jama'a hotuna da bidiyon tsiraici, lamarin da ya ce na matuƙar gurɓata tarbiya.

    ''Ana samun wasu ɓata-gari masu sana'ar dowulodin da ke tura wasu fina finai na batsa'', in ji shi.

  14. Iran ta yi iƙirarin lalata wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf

    Ɓarna

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun juyin juya halin Iran sun bayyana cewa sun lalata na;urorin sadarwar Amurka biyu a ƙasar Oman.

    Cikin wata sanarwar da rundunra ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce rundunar sojin ruwanta ta lalata na'urar da ke kula da sadarwar jirage a tashar ruwa ta Salalah da kuma wadda ke tashar Ghanem duka a Oman da safiyar yau Juma'a.

    Sanarwar ta jaddada cewa Iran za ta ci gaba da ɗaukar matakan martani, kuma mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon dakarun sojin ruwa na rundunar juyin juya halin.

    IRGC ta kuma ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al-Tanf da ke kudancin Siriya.

    Rundunar ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga kisan sojojinta a harin Iranshahr.

    ''Dakarun sojin sama na rundunar IRGC sun kai hari kan sansanin sojojin Amurka na musamman a Al-Tanf, da na'urorin sadarwar jirage da kan jirage na musamman masu saukar ungulu da wasu sojojin na Amurka'', in ji sanarwar ta IRGC.

    To sai dai kakakin rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM ya shaida wa kafar yaɗa labarai na Al Jazeera cewa hare-haren an Iran kan ƙasashen yankin Gulf ''ba su haifar da wani lahani da ayyukan sojojin ba''.

  15. Amurka ta ce ta kai hari kan ɗaya daga cikin tasoshin ruwan Iran

    Tashar ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya bayar da rahoton cewa Amurka ta kai hare-hare kan na'urar lura da zirga-zirgar jirage a tashar ruwa ta Chabahar har sau uku da safiyar yau Juma'a.

    Rahoton ya ce hare-haren sun lalata ilahirin na'urar, amma ba a samu wata ɓarna ga jiragen ruwan ko sauran kayyakin da ke tashar ba

    Majiyoyi sun ce ƙarar manyan abubuwan fashewa ne suka lalata na'urar.

    IRNA ya ce tawagogin masana da masu bincike na auna yanayin, da nufin gyara na'urar domin ci gaba da gudanar da ayyuka a tashar.

    Babu dai labarin jikkata ko rasa rai a lokacin harin.

  16. Trump ya zargi China ta yin katsalandan a zaɓen Amurka na 2020

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi China da yin katsalandan mai yawa a zaɓen shekarar 2020, tare da iƙirarin cewa hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi ƙoƙarin ɓoye abin da ya bayyana a matsayin yunƙurin Beijing na cutar da shi a siyasance a zaɓen wancan lokaci.

    A wani jawabi da ya yi wa al'ummar ƙasar, Mista Trump ɗin, wanda ya sha kaye a zaɓen a hannun Joe Biden, ya sake nanata zarginsa cewa an tafka maguɗi a zaɓen domin hana shi samun nasara.

    Gwamnatin China ta mayar da martani a sanarwar da ofishin jakadancinta da ke birnin Washington ya fitar tana mai cewa babu wani kutsen da ta yi a harkar zaɓen Amurka.

    Haka kuma bincike da shari'o'i da dama da aka gudanar a matakai daban-daban sun kasa gano wata hujja da ke tabbatar da zargin maguɗi a zaɓen.

  17. An ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran da Amurka

    hari

    Asalin hoton, Reuters

    An kwana na shida a jere na musayar wuta tsakanin Amurka d Iran bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin biyu suka cimma.

    Amurka na kai hare-hare a wasu yankuna na ƙasar Iran, yayin da a nata ɓangare, ita ma Iran ɗin ke ci gaba da mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wasu cibiyoyin Amurka a yankin Gulf.

    Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ce an ji fashe-fashe a birnin Bushehr, inda a nan ne tashar nukiliya ƙasar take.

    Haka kuma suna bayar da rahoton cewa mutum uku sun mutu, yayin da wasu tara suka jikkata, sakamakon hare-haren da aka kai kan wasu gadoji a wani gari da ke kusa da mashigin ruwan Hormuz.

    A farkon makon da muke ciki ne shugaba Trump ya yi barazanar kai wa gadoji da tashoshin wutar lantarkin ƙasar hari idan Iran ta ƙi ba da ikon Mashigin ruwa na Hormuz.

    Rundunar sojin Kuwait ta ce ta girke na'urar kare sararin samaniyarta domin tunkarar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ke kaiwa.

  18. Assalamu alaikum

    Mabiya shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yui mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.