Labarin wasanni daga 7 zuwa 12 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 7 zuwa 12 ga watan Satumbar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Christian Eriksen ya koma Wolfsburg bayan barin Man United

    Christian Eriksen

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan tsakiyar Manchester United da Denmark, Christian Eriksen, ya koma kulob ɗin Wolfsburg ta ƙasar Jamus bayan barin United ɗin a ƙarshen kakar bara.

    Ɗanwasan mai shekara 33 ya koma gasar Bundesliga ne kan yarjejeniyar da za ta ƙare a 2027.

    Eriksen ya buga wa United wasa 107 tare da cin ƙwallo takwas a kakar wasa uku da ya yi, inda ya lashe kofin Carabao a 2023 da FA a 2024.

    "Wolfsburg ne kulob ɗina na farko a Bundesliga - na ƙagu na fara taka leda a wannan sabuwar ƙunbgiya. Ina da tabbas za mu iya cim ma nasara tare," in ji Eriksen.

  2. Shekaru lambobi ne kawai, in ji Jamie Vardy

    Jamie Vardy

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗanwasan Leicester City Jamie Vardy ya ce "shekaru adadi ne kawai" yayin da yake fara sabuwar rayuwa a ƙungiyar Cremonese ta Italiya.

    Ɗanƙwallon mai shekara 38 ya bar Leicester ne a ƙarshen kakar da aka kammala bayana shekara 13 da ya shafe a kulob ɗin. Ya ci ƙwallo 200 cikin wasa 500.

    Ya ci 24 daga cikinsu ne a shekarar da suka ɗauki kofin gasar Premier League na shekarar 2015-16.

    Vardy ya koma Cremonese a kyauta a farkon watan nan bayan ƙungiyar kuma zai iya fara taka leda a ranar Litinin a wasa da Verona.

    Da aka tambaye shi ko shi da tsofaffin 'yanwasa irinsu Kevin de Bruyne da Luka Modric, waɗanda suka koma gasar Serie A ta Italiya a kakar nan, suna samun ƙwarin gwiwar ci gaba da buga wa manyan ƙungiyoyi wasa, sai ya ce:

    "Ni a wajena shekaru lambobi ne kawai. Matuƙar ƙafafuwana suna yin abin da suka saba kuma suna nan da ƙwarinsu ni ma zan ci gaba."

  3. Osimhen zai dawo taka leda nan gaba kaɗan - Galatasaray

    Victor Osimhen

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce ɗanwasan gabanta kuma ɗan Najeriya Victor Osimhen zai koma taka leda nan ba da jimawa ba bayan raunin da ya ji yayin buga wa Super Eagles wasa.

    Wata sanarwa da kulob ɗin ya wallafa a shafinsa na intanet ta ce gwajin da likitoci suka yi masa ya nuna cewa ya ji ɗan rauni ne a idon sawunsa.

    "An gano wani rauni maras girma a idon sawunsa kuma tuni aka fara yi masa magani domin ya koma taka leda da wurwuri," a cewar sanarwar.

    Osimhen ya ji raunin ne yayin da Najeriya bayan ya ci karo da ɗanwasan bayan Rwanda Claude Niyomugabo ranar Asabar a wasan neman gurbin Kofin Duniya.

    Raunin ya sa Osimhen bai buga kararwar Najeriya da Afirka ta Kudu ba ranar Talata.

  4. Ana tuhumar Chelsea da karya dokokin biyan wakilan 'yanwasa

    Roman Abramovich

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Roman Abramovich ne ke mallakar ƙungiyar a lokacin tun daga 2003 zuwa 2022

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Birtaniya ta tuhumi Chelsea da laifuka 74 da suka shafi karya dokokin biyan wakilan 'yanwasa tsakanin 2009 zuwa 2022.

    Tuhume-tuhumen sun fi shafar abubuwan da suka faru ne a kakannin wasa na 2010-11 da kuma 2015-16.

    Roman Abramovich ne ke mallakar ƙungiyar a lokacin tun daga 2003 zuwa 2022, kafin ya sayar da ita ga ɗn Amurka odd Boehly da kamfanin Clearlake Capital.

    Dokokin da ake zargin an karya sun shafi wakilan 'yanwasa, da dillalai, da kamfanoni masu zuba jari a kan 'yanwasa.

    Chelsea wadda ta ce ita ce da kanta ta kai wa FA rahoton saɓa dokokin, tana da damar mayar da martani zuwa 19 ga watan Satumba.

    Cikin horarwar da Chelsea za ta iya fuskanta akwai tara, ko hana su sayen 'yanwasa, ko kuma rage musu maki.

  5. Fabianski ya sake komawa West Ham United

    Fabianski

    Asalin hoton, Getty Images

    Golan tawagar Poland, Lukasz Fabianski ya sake komawa West Ham kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana, bayan da mai shekara 40 ya bar ƙungiyar sakamakon da ƙwantiraginsa ya kare a karshen kakar da ta wuce.

    Fabianski, wanda ya yi wa West Ham wasa 216 a kaka bakwai, ɗaya ne daga manyan ƴan wasan da aka ƙi tsawaita yarjejeniyarsu, bayan da ta karkare a karshen 2024/25.

    West Ham ta ƙulla yarjejeniya da tsohon golan nata, saboda yanzu masu tsaron raga biyu ne suka rage mata, wato Mads Hermansen da Alphonse Areola, inda Wes Foderingham ya koma Aris Limassol ta Cyprus ranar Talata.

    An zura ƙwallo takwas a ragar West Ham karkashin sabon mai tsaron raga, Hermansen.

    Hakan ya sa tana ta 16 a kasan teburi, za kuma ta kece raini da Tottenham a wasan hamayya ranar Asabar a gasar Premier League.

  6. Postecoglou zai ja ragamar Forest da mataimakan da ya yi aiki da su a Tottenham

    Postecoglou

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest ta sanar cewar Mile Jedinak da Nick Montgomery da Sergio Raimundo da kuma Rob Burch za su yi wa Ange Postecoglou mataimaka a ƙungiyar.

    Dukkansu huɗun sun yi aikin horar da Tottenham, za kuma su kara aiki tare a Forest da Postecoglou, bayan da ya maye gurbin Nuno Espirito Santo, wanda aka sallama.

    Jedinak, wanda ya buga gasar Premier League kusan karawa 100, shi ne mataimaki tare da Montgomery da Raimundo da kuma Burch a matakin kociyan masu tsare raga, kamar dai yadda suka yi a Tottenham.

    Tottenham ta kori Postecoglou cikin watan Yuni, kwana 16 tsakani da ya lashe Europa League.

    Mai shekara 60 ɗan kasar Australia ya yi kaka biyu a Tottenham, wanda ya kare a mataki na 17 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila a kakar da ta wuce.

  7. An zargi tsohon rafli, Coote da cin zarafin yaro

    Coote

    Asalin hoton, PA Media

    An tuhumi tsohon alkalin wasan Premier David Coote da fitar da hoton da ya zama cin zarafin yaro.

    Tsohon jami'in, mai shekaru 43 kuma daga Collingham, zai gurfana a gaban Kotun Majistare ta Nottingham ranar Alhamis.

    Laifin ya shafi rabawa ko adana hotuna ko bidiyo cin zarafin da ya shafi faifan bidiyo da jami’an ‘yan sandan Nottinghamshire suka kwaso a watan Fabrairu, in ji rundunar.

    An gurfanar da Coote a ranar 12 ga watan Agusta kuma yana kan beli.

    Mahukutan kwamitin rafli sun kori Coote a watan Disamba, bayan wani faifan bidiyo na kalaman batanci da ya yi kan tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp a shekarar 2020 da ya fito fili.

    Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da shi har zuwa ranar 30 ga watan Yuni 2026 bayan wani faifan bidiyo daban da ya fito na nuna shi yana shekar foda, yayin da yake Jamus don gasar Euro 2024.

    A cikin Janairu Coote ya fito ya bayyana kansa a matsayin ɗan luwaɗi, kuma ya ce gwagwarmayar rayuwa ya sa ya ɓoye, hakan ya bayar da gudummawa da ɓacin rai game da Klopp da kuma amfani da muggan ƙwayoyi.

    A watan Agustan bana kuma hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da shi na tsawon makonni takwas saboda faifan da ya yi kan Klopp. Mai magana da yawun Coote ya ki cewa komai lokacin da aka tuntuɓe shi.

  8. Fitattun ƴan wasa na fama da ciwon damuwa, amma suna yin shiru - Mbappe

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Kylian Mbappe Kylian Mbappe ya ce har yanzu manyan 'yan wasa ba sa son yin magana cikin walwala game da lafiyar kwakwalwa, saboda suna tsoron kada a yi musu mummunan fahimta, ya kara da cewa sha'awar wasan ya sa ya shaku da kwallon kafa.

    A wata tattaunawa da ya yi da Mujallar L’Equipe ranar Laraba, dan wasan mai shekara 26 ya yi magana kan matsin lambar da yake fuskanta da kuma fahimtar cewa fitattun ‘yan wasa ba za su iya nuna rauni ba.

    "Mai rikitarwa shine mutane suna fama da shi. Bai kamata ku nuna shi ba, "in ji Mbappe, lokacin da aka tambaye shi game da masu tseren kekuna irin su zakaran Tour de France sau hudu Tadej Pogacar ya ce lallai yayi fama da damuwa a lokacin gasar.

    "Idan da ya fadi hakan tun da farko, da an samu sauki da mafita. Amma idan kun ci nasara, ba za ku iya cewa komai ba. Idan kun yi rashin nasara kuma kuka ce kun gaji daga nan matasala za ta kunno, mutane suna cewa saboda kun kasa yin abin kirki ne.

    Dan wasan gaban na Real Madrid, wanda ya zura kwallaye biyu a wasanni biyu na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da suka yi da Ukraine da Iceland, ya ce ya rike kansa a matsayin da ya fi bukata.

    "Ban taɓa yarda da gazawa ba, don haka ban damu ba idan mutane za su zarge ni, Ina iya kokarina saboda haka bana bari wani karamin abun ya ɗauke min hankalina ba.

  9. Za a fara sayar da tikitin kallon gasar kofin duniya daga ranar Laraba

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Daga ranar Laraba za a fara sayar da tikitin kallon gasar cin kofin duniya, kasa da shekara ɗaya da za a yi bikin buɗe wasannin a birnin Mexico.

    Ana sa ran kuɗin tikitin zai kama daga matsaikaicin kuɗi dalar Amurka 60 zuwa wasan karshe dalar Amurka 6,730.

    Za a fara gasar cin kofin duniya daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin baɗi.

    Kimanin ƴan kallo miliyan 6.5 ake sa ran za su halarci gasar cin kofin duniya da tawaga 48 za ta kece raini a wasa 104 da za a buga tsakanin Mexico da Canada da kuma Amurka

    Ranar 5 ga watan Disamba za a fitar da jadawalin gasar cin kofin duniya a Kennedy Center.

  10. Marmoush ba zai buga wa City karawa da United ba, saboda rauni

    Cherki

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City za ta kara da Manchester City ranar Lahadi a gasar Premier League wasan hamayya ba tare da Omar Marmoush ba, sakamakon raunin da ya ji.

    An sauya mai shekara 26 a minti na tara da take leda a wasan da Masar ta tashi ba ci da Burkina Faso a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ranar Talata.

    Marmoush, wanda ya koma Etihad daga Eintracht Frankfurt kan fam miliyan 59 a watan Janairu, ya koma cikin fili, bayan da likitoci suka duba shi daga baya Osama Faisal ya canje shi, bayan da raunin ya yi tsami.

    Ɗan wasan ya ci ƙwallo 28 a City, tun bayan da ya koma ƙungiyar da taka leda.

    City na fama da ƴan wasan gaba dake jinya ciki har da Rayan Cherki da Phil Foden da bai buga wa City karawar da Brighton ta doke ta ba a Premier League.

  11. Ronaldo ya yi kan-kan-kan a cin ƙwallaye a neman shiga gasar kofin duniya

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Cristiano Ronaldo ya yi kan-kan-kan a cin ƙwallaye a lokacin da Portugal ta doke Hungary a wasan neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Mexico da Canada.

    Ronaldo ya zura ƙwallo na 39 a raga, hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da ɗan wasan Guatemala, Carlos Ruiz, da tazarar uku tsakani da ƙyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi.

    Mai shekara 40, ya ci wa Portugal ƙwallo 141 a wasa 223, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon a kasar.

  12. Har yanzu da sauran aiki a gaban Super Eagles

    Super Eagles

    Asalin hoton, Getty Images

    Super Eagles ta je ta tashi 1-1 da Afirka ta Kudu a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka fafata ranar Talata a birnin Bloemfontein.

    Afirka ta Kudu ce ta fara zura ƙwallo a raga, bayan da mai tsaron bayan Najeriya, William Troost-Ekong ya ci gida a minti na 25.

    Sai dai daf da za su je hutu ne Super Eagles ta farke ta hannun Calvin Bassey, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.

    Da wannan sakamakon Afirka ta Kudu ta ci gaba da zama a matakin farko da maki 17, sai Najeriya ta biyu da maki 11 da kuma Benin da Rwanda da kowacce keda maki 11.

    Sai dai a daren nan Benin za ta karɓi bakuncin Lesotho - Lesotho maki shida ne da ita a mataki na biyar ɗin teburi da kuma Zimbabwe ta karshe ta shida da makinta huɗu.

  13. An kara hukuncin dakatar da Luis Suarez, saboda tofa yawu

    Luis Suarez

    Asalin hoton, Getty Images

    An kara hukuncin dakatar da Luis Suarez wasa uku kan na farko da aka yi masa, saboda tofa yawu da ya yiwa wani mamba na ƙungiyar Seattle Sounders.

    Ƙwamitin ladabtarwa na League Cup ne ya fara dakatar da Suarez wasa shida, bayan tashi daga wasan da suka fafata ranar 31 ga watan Agusta, inda Inter Miami ta yi rashin nasara 3-0.

    Yanzu kuma mahukuntan Major League Soccer ne suka kara dakatar da Suarez karawa uku, kenan ba zai fuskanci Charlotte FC da DC United da kuma Seattle in Miami a gasar tamaula ta Amurka.

    Hukumar ƙwallon kafar Ingila ta taɓa dakatar da Suarez wasa takwas a 2011, bayan da aka same shi da laifin kalamun wariya ga ɗan wasan Manchester United, Patrice Evra.

    An dakatar da shi wasa uku a Ajax da tawagar Uruguay da Liverpool -saboda cizon abokin wasa.

  14. Forest ta naɗa Postecoglou sabon kociyanta

    Postecoglo

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest ta sanar da naɗa Ange Postecoglou a matakin sabon kociyanta, bayan da ta kori Nuno Espirito Santo.

    Nuno ya bar City Ground a tsakar daren Litinin, bayan wata 21 yana jan ragama da yin wasa uku da fara kakar bana ta Premier League.

    Postecoglou ya koma aikin horar da tamaula a Premier League, bayan wata uku da Tottenham ta kore shi, sakamakon da ta kare a mataki na 17 a kasan teburin Premier League.

    Sai dai mai shekara 60 ya lashe Europa League a karshen kakar da ta wuce, hakan ya kawo karshen tsawon shekaru ba tare da babban kofi ba.

    Yanzu dai Forest tana mataki na 10 a teburin Premier League, bayan wasa uku da fara kakar nan.

    Wasan karshe da Nuno ya ja ragama shi ne wanda West Ham ta je ta doke Forest 3-0 a cikin watan Satumba a Premier League.

    Mai shekara 51 ya karɓi aikin horar da Forest a cikin Disambar 2023, wanda ya maye gurbin Steve Cooper.

    A kakar da ta wuce ya kai Forest mataki na bakwai a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila - mataki mai ƙyau tun bayan 1994/95 da samun tikitin shiga gasar zakarun Turai - karon farko cikin shekara 30.

  15. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Aston Villa da Leeds United da Newcastle United na zawarcin dan wasan mai kai hari na Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, kuma za su iya siyan sa a watan Janairu.(Caught Offside), external

    Birmingham City da Wrexham da kuma West Brom duk suna sha'awar siyan dan wasan tsakiya na Ingila Dele Alli . Kwanan nan dan wasan mai shekaru 29 ya soke yarjejeniyarsa da kulob din Como na Italiya.(Mail), external

    Golan Lazio Christos Mandas, mai shekara 23, zai yi nazari kan makomarsa a kungiyar a watan Janairun badi, bayan da ya rasa matsayinsa a jerin 'yan wasan da suka buga wasan farko , inda Wolves ta nuna sha'awar siyan dan wasan kasar Girka kan kudi fan miliyan 17 a lokacin bazara. (Corriere dello Sport), external

    Dan wasan bayan Inter Milan Denzel Dumfries ya ce zai ji dadin samun damar taka leda a gasar firimiya bayan bazara inda aka alakanta dan wasan na Netherlands, mai shekara 29 da Manchester United.(Metro), external

    Real Betis ta sake tattaunawa da Manchester United kan batun cinikin dan wasan Brazil Antony, mai shekara 25, (Express), external

  16. Ekitike ya yi wa Isak maraba kuma a shirye yake ya kalubalance shi

    Ekitike

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon ɗan wasan Liverpool, Hugo Ekitike ya yi wa Alexander Isak maraba, ya kuma ce a shirye yake domin yin takara da shi don samun gurbin buga wa ƙungiyar Anfield wasa a koda yaushe.

    Ekitike shi ne na uku mafi tsada da Liverpool ta ɗauka a bana, bayan Isak daga Newcastle da Florian Wirtz daga Bayern Leverkusen.

    Tuni Ekitike ya fara nuna kansa, wanda kawo yanzu ya ci ƙwallo uku a wasa huɗun da ya buga wa ƙungiyar dake rike da kofin Premier League.

    Ekitike ya koma Liverpool, bayan rawar da ya taka a kakar 2024/25 a Eintranch Frankfurt, wanda ya ci ƙwallo 15 a Bundesliga a wasa 33.

  17. Azerbaijan ta kori kociyanta Fernando Santo

    Azerbaijan ta kori kociyan tawagarta, Fernando Santos kamar yadda hukumar ƙwallon kafar ta sanar ranar Litinin.

    Ta raba gari da kociyan kwana ɗaya tsakani da Iceland ta caskara ta 5-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ranar Juma'a.

    Santos, wanda ya ja ragamar Portugal ta lashe kofin zakarun Turai da na Nations League, ya kasa cin wasa daga karawa 11 tun daga lokacin da aka damka masa ragamar tawagar a Yunin 2024 da yin rashin nasara tara daga ciki.

    Tun a minti 30 da take leda aka ɗura ƙwallo 5-0 a ragar Azerbaijan a wasan farko a rukuni na huɗu ranar Juma'a a karawar ta neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

    An bai wa Ayxan Abbasov kociyan matasa ƴan kasa da shekara 21 aikin riƙon ƙwarya, zai ja ragamar Azerbaijan a wasan da za ta fuskanci Ukraine ranar Talata.

  18. Guehi

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta fasa daukar dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi a watan Janairun badi. Kungiyar ta Reds ta kasa biyan fam miliyan 35 kan dan wasan na Ingila mai shekara 25 a makon da ya gabata, kuma za ta saye shi ne kawai idan kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa.(Times - subscription required), external

    Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin dan wasan bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate kan sabon kwantaragi tare da dan wasan mai shekaru 26 wanda ke cikin jerin 'yan wasan da Real Madrid ke zawarcinsu. (Fabrizio Romano via Givemesport), external

    Dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 26, ya fadawa dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya koma Real Madrid. Dan wasan na Masar, mai shekara 33, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragin shekaru biyu a Anfield a watan Afrilu amma watakila zai zo komawa Bernabeu.(Teamtalk), external

    Golan Manchester United Andre Onana ya amince ya koma kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya a matsayin aro amma babu zabin siyan dan wasan na Kamaru mai shekara 29.(Fabrizio Romano), external

  19. Leverkusen ta ɗauki Hjulmand sabon kociyanta

    Leverkusen

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayer Leverkusen ta ɗauki tsohon kociyan tawagar Denmark, Kasper Hjulmand a matakin sabon wanda zai horar da ita, wanda ya amince da yarjejeniyar kaka biyu, ya kuma maye gurbin Erik Ten Hag, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Litinin.

    Hjulmand, mai shekara 53, ya kai Denmark daf da karshe a Euro 2020, inda suka yi rashin nasara a hannun Ingila, ya kuma ajiye aikin bayan doke su 2-0 da Jamus ta yi a Euro 2024, wanda ya yi kaka huɗu yana jan ragama.

    Ɗan kasar Denmark ya horar da tamaula a Mainz 05 a kakar 2014/15, yanzu kuma zai ja ragamar Leverkusen.

    Leverkusen ta kori Ten Hag bayan jan ragama karawa biyu da fara Bundesliga a kakar nan, ya maye gurbin Xabi Alonso, wanda ya koma jan ragamar Real Madrid.

  20. An dakatar da ɗan wasan Bilbao, Alvarez wato 10 kan shan abubuwan kuzarin wasa

    Alvaraz

    Asalin hoton, Getty Images

    An dakatar da ɗan wasan Athletic Bilbao, Yeray Alvarez wata 10, saboda amfani shan abinda aka haramta, wanda ya yi amfani da shi na hana zubewar gashi lokacin da ya yi jinyar daji.

    An samu mai shekara 30 da laifi, bayan tashi wasan da Manchester United ta ci 3-0 a zagayen daf da karshe a Europa League a watan Mayu.

    Uefa ta amince da korafin Alvaraz kan dalilinsa na amfani da kwayar, wadda take da nau'in Canrenone.

    Alvarez wanda ya kamu da cutar daji a 2016 ya ce ya yi amfani da kwayar don magance zubewar gashi a lokacin.

    Ko da yake Uefa ta amince da bayanin Alvarez kuma ta ce bai yi niyyar shan haramtaccen abu ba, ''amma an same shi da laifin karya ka'idojin amfani da kwayoyi masu kara kuzari ba da gangan ba".

    Ganin cewa Alvarez ya amince da dakatarwar na wucin gadi a watan Yuni. Zai iya sake buga wasa daga 2 ga Afrilu 2026 kuma zai iya komawa ɗaukar horo daga 2 ga Fabrairu.

    Alvarez ya buga wa Bilbao wasanni 257 tun lokacin da ya shiga makarantar.