KAI TSAYE, Gasar Kofin Duniya 2026 da sauran labaran wasannin BBC Hausa na wannan mako

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran Gasar Kofin Duniya 2026 da sauran labaran wasannin BBC Hausa na wannan mako 6-12 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ingila na shakku ko Guehi zai buga wasan Norway

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a duba lafiyar ɗan wasan baya na Ingila Marc Guehi a ranar Juma'a domin ganin ko zai iya buga wasan daf da na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya da za a yi ranar Asabar da Norway.

    Ɗan wasan yana da ɗan rauni a cinyarsa bayan nasarar da Ingila ta samu kan Mexico da ci 3-2 a zagayen ƴan 16 a filin wasan Azteca.

    A halin yanzu, ɗan wasan baya na dama Reece James ya koma atisaye kamar yadda aka zata a ranar Alhamis kuma yana cikin ƴan wasan da za su buga wasan, amma Declan Rice bai sake yin atisaye ba saboda rashin lafiya.

    Da farko an yi fatan Guehi yana ɗauke da gajiyar tsoka ce kawai kuma zai iya samun lafiya don fafatawa da Norway.

    Amma an fahimci cewa ɗan wasan baya na Manchester City yana da rauni a cinyarsa.

    Idan har bai iya yin atisaye da tawagar a ranar Juma'a ba to za a sami babban shakku kan shigarsa wasan da Norway.

  2. Palace ta ɗauki ɗan wasan bayan Spain kan cinikin kyauta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Crystal Palace ta sayi ɗan wasan baya na Celta Vigo Oscar Mingueza a kan cinikin kyauta bayan ƙarewar kwantiraginsa.

    Dan wasan na Spain mai shekaru 27 ya koma Palace kan kwantiragin shekaru huɗu kuma shine ɗan wasa na farko da koci Pierre Sage ya saya a wannan bazarar.

    Mingueza ya fito ne daga makarantar La Masia ta Barcelona kuma ya buga wasanni 66 a ƙungiyar bayan ya fara buga wasa a shekarar 2020.

    Ɗan wasan mai tsaron baya ya koma Celta Vigo ne a shekarar 2022, inda ya zura ƙwallaye bakwai sannan ya bayar da taimako aka ci 15 a wasanni 147.

    Mingueza ya ce komawarsa Palace "abin alfahari ne" kuma ya ƙara da cewa yana "matukar farin ciki" da kasancewa a Selhurst Park.

    An ya taɓa bugawa tawagar Spain wasa huɗu, duk da haka ba a saka shi cikin tawagar ƴan wasa 26 da kocin Luis de la Fuente ya kai gasar cin kofin duniya ta bana ba.

  3. An dakatar da Quansah na wasa biyu sakamakon jan katin da ya samu

    ...

    Asalin hoton, getty

    An dakatar da dan wasan baya na Ingila Jarell Quansah na wasanni biyu saboda jan katin da aka danna masa a wasan da suka yi da Mexico.

    An kori Quansah ne a minti na 54 na wasan da suka yi nasara da ci 3-2 bayan wani ƙeta da ya yi wa Jesus Gallardo.

    An bayyana ƙetar a matsayin 'mai matuƙar muni', wanda ke nufin kwamitin ladabtarwa na Fifa ya bai wa ɗan wasan na Bayer Leverkusen ƙarin dakatarwa ta wasanni biyu.

    Tsohon ɗan wasan Liverpool Quansah ba zai buga wasan kwata-fainal da Norway ba ranar Asabar da kuma wasan kusa da na ƙarshe da Argentina ko Switzerland.

    Quansah, mai shekaru 23, zai kasance a shirye ya buga wasa idan Ingila ta kai wasan ƙarshe a New Jersey a ranar 19 ga Yuli.

  4. Eriksen zai ci gaba da murmurewa a Denmark bayan ya yanki jiki ya faɗi a filin wasa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Christian Eriksen zai fara murmurewa a Denmark bayan ya yanki jiki ya faɗi a wani wasan sada zumunta a watan da ya gabata.

    Ya faɗi a lokacin wasan da suka yi da Ukraine a Odense a watan Yuni, inda aka dakatar da wasan a mintuna 65 daga baya kuma aka yi watsi da shi baki ɗaya.

    Ɗan wasan tsakiya mai shekaru 34 ya sami damar fita daga filin wasan da ƙafarsa.

    An sanya wa tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Tottenham na'urar magance bugun zuciya (ICD) -a zuciyarsa- bayan ya yi fama da bugun zuciya a lokacin wasan Euro 2020 da Finland a 2021.

    Bayan abin da ya faru a watan da ya gabata, ya ce "yanayi ne daban da abin da abin da ya faru a 2021" kuma ya bayyana cewa na'urar ICD ɗinsa "ya yi aikin da ya kamata ya yi: kare ni lokacin da nake buƙatarsa".

    Eriksen bai samu damar ci gaba da buga wa ƙungiyar Inter Milan ta gasar Serie A wasa ba bayan matsalar zuciyar da ya fuskanta a gasar Euro, saboda dokokin Italiya da suka hana ƴan wasa masu amfani da na'urar ICD shiga gasa; sai dai ya ci gaba da wasa tare da ƙungiyar Brentford a shekarar 2022.

    Daga nan ya shafe shekaru uku tare da Manchester United, kuma yana buga wa Wolfsburg wasa tun watan Satumbar 2025 — kasancewar gasar Premier League da Bundesliga duk suna ba wa ƴan wasa masu amfani da na'urar ICD damar shiga gasa.

  5. Newcastle ta ɗauki matashin ɗan wasa Steur daga Ajax kan fam miliyan 23

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle United ta ɗauki matashin ɗan wasan tsakiya Sean Steur daga Ajax, a yarjejeniyar da ta kai har fam miliyan 23.

    Matashin mai shekaru 18 ya isa Tyneside a yammacin ranar Laraba, inda ya fara gudanar da gwajin lafiya kafin kammala komawarsa ƙungiyar.

    Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar, wanda zai ƙare a shekarar 2031.

    An samu sauye-sauye da dama Newcastle a wannan bazarar, musamman a ɓangaren ƴan wasan tsakiya.

    Sandro Tonali ya koma Tottenham Hotspur a yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 100, yayin da kyaftin, Bruno Guimaraes, ya nuna cewa shi ma yana son barin ƙungiyar domin komawa Arsenal.

  6. Brentford ta kammala cinikin Wilson daga West Ham

    Wilson

    Asalin hoton, gett

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brentford ta ɗauki tsohon ɗan wasan gaba na Ingila, Callum Wilson, kan kwantiragin watanni 12.

    Wilson ya kasance ɗan wasa mai zaman kansa bayan barin kungiyar ta London Stadium sakamakon faɗuwarta daga gasar Premier League.

    Zuwan ɗan wasan mai shekaru 34 ya biyo bayan shigowar Jaidon Anthony daga Burnley a wannan makon.

    Wilson yana da gogewa sosai a gasar Premier League, kasancewar ya buga wa ƙungiyoyin West Ham da Newcastle United da Bournemouth wasanni a wannan babban mataki.

    Haka kuma, ya wakilci tawagar ƙasar Ingila sau tara tsakanin shekarar 2018 da 2023, inda ya zura ƙwallaye biyu tare da halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.

    Ya zura kwallaye bakwai a wasanni 32 da ya buga wa West Ham a kakar wasan da ta gabata.

  7. Meslier ya koma Arsenal kan cinikin kyauta bayan barin Leeds

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta kammala cik=nikin ɗaukar mai tsaron gida Illan Meslier a kan yarjejeniyar kyauta daga Leeds akan kwantiragin shekarua biyu tare da zaɓin tsawaitawa ta shekara guda.

    Meslier ya buga wasanni 215 a cikin shekaru bakwai tare da ƙungiyar ta Yorkshire, inda ya hana a zura masa ƙwallaye a wasa 70.

    Mai tsaron gida na Faransa, mai shekaru 26, ya ce "yana jiran lashe kofuna" tare da "babbar ƙungiya a Ingila". BBC Sport ita ce ta fara bayyana sha'awar Gunners a kan Meslier a ranar 30 ga Yuni kuma yanzu an kammala cinikin.

    Meslier zai zo ne a matsayin mai tsaron gida na uku bayan Raya da Arrizabalaga, amma idan har Arrizabalaga ya bar ƙungiyar, to za a iya daga matsayin Meslier zuwa na mai tsaron gida na biyu.

  8. Man Utd ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 50 da Chelsea kan Santos

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta amince da yarjejeniyar £50m da Chelsea don siyan ɗan wasan tsakiya na Brazil Andrey Santos.

    An kammala cinikin cikin sauri a cikin ƴan dsa'o'in da suka gabata bayan da United ta bayyana sha'awarta a \ƙarshen mako.

    Tashin farko United za ta biya £48m, tare da ƙarin £2m bvayan an cika wasu sharuɗɗa da aka bayyana a matsayin 'masu sauƙin cikawa'. Chelsea kuma za ta samu kashi 10 cikin 100 na kudin da United za ta sayar da Santos nan gaba.

    Yanzu Santos zai je a gwada lafiyarsa, yadda aka shirya shi ma dan ƙasarsu Ederson zai yi na shi gwajin kafin ya kammala komawarsa daga ƙungiyar Italiya ta Atalanta bayan fitar da Brazil daga gasar cin kofin duniya.

    Labarin ya zo ne yayin da manyan ƴan wasan United ke shirin dawowa don atisayen shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa a ranar Alhamis.

  9. Guimaraes ya nemi barin Newcastle

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bruno Guimaraes ya nemi barin ƙungiyar Newcastle, yayin da Arsenal ke ƙara nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar.

    Ɗan wasan na tawagar ƙasar Brazil, wanda ya koma ƙungiyar daga Lyon a shekarar 2022, ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da zakarun gasar Premier ke zawarci a wannan bazara.

    Ƙungiyar ta Arsenal ta na duba yiwuwar ɗaukar Guimaraes ko kuma tsohon abokin wasansa Sandro Tonali — wanda yanzu ya koma Tottenham kan kudi da ya kai fam miliyan 92.5 , yayin da suke ƙoƙarin ƙarfafa ɓangaren ƴan wasan tsakiyarsu.

    A yayin tattaunawar da aka yi domin duba sharuɗɗan kuɗi na cinikin Guimaraes, an fahimci cewa wakilan ɗan wasan mai shekaru 28 sun fara ambaton kuɗi da ya kai kimanin fam miliyan 60.

    Duk da cewa babu wata tattaunawa ta kai-tsaye tsakanin Newcastle da Arsenal, yanzu haka tawagar Mikel Arteta na shirin gabatar da sabon tayi kan Guimaraes—wanda ya ɓarar da fenariti a wasan da Brazil ta yi rashin nasara a hannun Norway a zagayen ƴan 16 na gasar cin kofin duniya a ranar Lahadi.

    A halin yanzu, na fahimtaci cewa Arsenal na son ɗaukar babban ɗan wasan tsakiya guda ɗaya ne kawai, inda ake kuma duba yiwuwar ɗaukar Alex Scott na Bournemouth da Ayyoub Bouaddi na Lille.

  10. Amorim ya nemi afuwar magoya bayan Man United

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ruben Amorim ya nemi afuwa saboda rashin yin magana da magoya bayan Manchester United tun bayan korarsa da aka yi a watan Janairu, amma ya ce yana "alfahari" da kasancewa kocinsu.

    Amorim ya yi tsit da bakinsa tun bayan barin Old Trafford kuma ya zaɓi kin yin duk wani bayani game da watanni 14 da ya yi a Old Trafford a shafukan sada zumunta.

    Kocin mai shekaru 41 yanzu ya kawo ƙarshen hutunsa daga wasa ta hanyar sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku da AC Milan.

    An gabatar da Amorim a ranar Laraba a babbar ƙungiyar ta Serie A - amma a wani taron manema labarai na mintuna 35 ba a nemi ya yi magana game da lokacinsa a United ba har sai da tambaya ta ƙarshe.

    A lokacin, tsohon kocin Sporting ya riga ya amince cewa ya yi wasu kurakurai a United kuma yana matuƙar sha'awar samun nasara saboda yadda "aikinsa na ƙarshe" ya kasance.

    Lokacin da aka tambaye shi ko waɗanne kura-kurai ya ke nufi, Amorim bai amsa tambayar kai-tsaye ba amma ya bayyana nadamarsa ga magoya bayan United saboda rashin magana da su.

  11. Ƙungiyar London City ta ɗauki Alexia Putellas

    Alexia Putellas

    Asalin hoton, London City Lionesses

    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta London City Lionesses ta sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru uku da Alexia Putellas, wadda ta lashe kyautar Ballon d'Or sau biyu, a wani lamari da ya zama ɗaya daga cikin ciniki mafi ban mamaki a fagen wasan ƙwallon ƙafar mata.

    Ana yi wa ƴar wasan tsakiyar ta Spain Putellas kallon ɗaya daga cikin manyan ƴan wasa, ta bar Barcelona bayan shekaru 14 a watan Mayu kuma ya jawo hankalin kusan dukkan manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan mata a duniya.

    Ƴan wasan mai shekaru 32 ta lashe kofuna 38 tare da Barcelona, ​​ciki har da kofuna 10 na lig ɗin Spain.

    An gabatar da ita a birnin New York tare da mai hamshaƙiyar mamallakiyar ƙungiyar ta London City Michele Kang.

  12. Kocin Croatia ya yi murabus bayan jagorantar tawagar ƙasar na shekara tara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Zlatko Dalic ya yi murabus bayan shekaru tara a matsayin kocin Croatia bayan shan kaye a hannun Portugal a gasar cin kofin duniya.

    Kocin mai shekaru 59 ya karɓi ragamar horas da tawagar ƙasar a shekarar 2017 kuma ya jagoranci Croatia zuwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2018 da kuma matsayi na uku shekaru huɗu bayan haka.

    Ƙasar Croatia ta fice daga gasar cin kofin Turai ta 2020 da aka jinkirta a zagaye na 16 kuma ta kasa kai wa matakin kifa-ɗaya-ƙwala na gasar Euro 2024, duk da cewa sun zo na biyu a gasar cin kofin ƙasashen Turai (Nations League) ta 2023.

    "Bayan kusan shekaru tara, babban koci Zlatko Dalic ya yanke shawarar rufe babinsa mai matuƙar nasara tare da Croatia," in ji wata sanarwa daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Croatia.

  13. Hukumar ƙwallon ƙafar Masar ta shigar da ƙara kan alƙalan wasanta da Argentina

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Masar ta ce ta yi kira ga FIFA da ta kori alƙalan wasan da suka yi aiki a wasan da ta yi rashin nasara a hannun Argentina a gasar cin kofin duniya a zagaye na ƴan 16.

    Hukumar ta ce ta shigar da ƙara ga hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya kuma tana son a gudanar da bincike kan abin da ta bayyana a matsayin "rashin daidaito" a yadda aka yi alƙalanci wasan.

    Mataimakin alƙalin wasa na bidiyo (VAR) ya soke ƙwallo na biyu da Mostafa Zico ya ci saboda ƙeta da ɗan wasan tsakiya Marwan Attia ya yi wa Lisandro Martinez kafin aka ci ƙwallon.

    Kuma sun dage cewa an yi wa Mohamed Salah ƙeta ƴan daƙiƙa kaɗan kafin Argentina ta farke ƙwallo na biyu.

  14. Switzerland ta kai zagayen kwata fainal bayan doke Colombia a bugun fenariti

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Switzerland ta tsallake zuwa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1954 bayan ta doke Colombia a bugun fenariti a ranar Talata a zagaye na ƴan 16.

    Wasan ya ƙare 0-0 bayan mintuna 120, amma Switzerland ta yi nasara da ci 4-3 a bugun fenarirti, kuma yanzu za ta fafata da Argentina a daren Asabar a Kansas City.

    Davinson Sanchez ne ya ɓarar wa Colombia fenariti na biyu, kuma Switzerland ta yi amfani da damar, bayan Cucho Hernandez ɓarar da fenaritin Colombia na huɗu. Ruben Vargas ya zura Fenarirtin Swtzerland na ƙarshe da ya bai wa ƙasarsa nasara.

  15. Ɗan wasan Aston Villa Amadou Onana ya ji mummunan rauni a gwiwarsa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tsakiya na Aston Villa Amadou Onana ya ji mummunan rauni a gwiwarsa ta dama a lokacin da yake bugawa Belgium wasa a gasar cin kofin duniya.

    An maye gurbin ɗan wasan mai shekaru 24 a minti 21 a wasan da tawagar ƙasarsa ta doke Amurka da ci 4-1 a zagaye na ƴan 16 na ƙarshe.

    Onana ya riƙe da gwiwarsa ta dama yayin da suke rige-rigen kai wa ga ƙwallon da shi da Christian Pulisic.

    Bayan an yi masa jinya a filin wasa, daga baya an gan shi a riƙe sanduna kuma yana sanye da takalmin gyaran gwiwa.

    A cikin wata sanarwa, likitan tawagar Belgium Brahim Hacene ya ce "rauni ne mai muni".

    Belgium ta ce Onana zai ci gaba da kasancewa tare da tawagar don karawar da za su yi da Spain a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a Los Angeles ranar Juma'a.

    Irin wannan raunin yawanci yana sa ƴan wasa su yi jinya na tsawon wata shida zuwa tara.

  16. Arsenal na shirin ɗaukar Meslier kan cinikin kyauta bayan barinsa Leeds United

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta kusa kammala cinikin ɗaukar mai tsaron gida Illan Meslier a kyauta daga Leeds.

    BBC Sport ita ce ta farko da ta bayyana sha'awar Gunners kan Meslier a ranar 30 ga Yuni kuma yanzu an cimma yarjejeniya.

    Meslier da wakilansa sun kasance a cibiyar horas da kulob ɗin da ke Hertfordshire don kammala cikakkun bayanai game da cinikin kuma a yi masa gwajin lafiya a ranar Talata.

    Ɗan wasan mai shekara 26, wanda ya rasa matsayinsa na lamba ɗaya a Leeds, kwantiraginsa zai ƙare a wannan bazarar kuma don haka zai zo ne kan kyauta.

    Akwai shakku kan makomar mai tsaron gida na yanzu Kepa Arrizabalaga a kakar wasa mai zuwa, wanda hakan zai sa Arsenal ta fara neman wanda zai maye gurbinsa.

    A halin da ake ciki yanzu dai, Meslier zai zo ne a matsayin mai tsaron gida na uku a bayan David Raya da Arrizabalaga.

  17. Za a hana ƴan wasan Ingila tsallaka allunan talla

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a shawarci 'yan wasan Ingila da su guji tsallake allunan talla bayan da Jordan Henderson ya samu rauni jim kaɗan bayan nasarar da suka samu kan Mexico a gasar cin kofin duniya.

    Ana sa ran za a yi wa ɗan wasan tsakiya na Brentford Henderson tiyata a kan raunin da ya samu a wuyan hannunsa yayin murnar nasarar da Ingila ta samu da ci 3-2 a filin wasa na Azteca.

    Wannan yana nufin cewa akwai babban shakku game yiwuwar fafatawarsa a sauran wasannin gasar.

    An fahimci cewa koci Thomas Tuchel na shirin umartar ƴan wasansa da su guji tsallake allunan talla domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.

    Wani ɗan tawagar likitocin Ingila ya raka Henderson inda ya ci gaba da zama a asibitin da ke Mexico City a yammacin ranar Lahadi, kuma bai dawo tare da sauran ƴan tawagar zuwa sansaninsu da ke Kansas City ba.

  18. Iraola ya kama aikin horas da Liverpool a hukumance

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon kocin Liverpool Andoni Iraola ya isa cibiyar horaswar ƙungiyar ta AXA , inda yawancin ƴan wasa da ma'aikatan ƙungiyar za su koma Merseyside a mako mai zuwa a ranar 14 ga Yuli.

    Wannan zai bai wa ɗan ƙasar Spain ɗin fiye da wata guda tare da tawagarsa kafin wasan farko na Premier League da Liverpool za ta kara da Newcastle a ranar 23 ga watan Agusta.

    To yaya zai kasance ga Iraola da Liverpool a wata mai zuwa?

    Daya daga cikin abubuwan farko da za su faru shine nazarin ƴan wasan da suka dawo kafin fara aikin tukuru.

    Babban abin da za a mayar da hankali a kai shi ne salon wasan ƙwallon ƙafa mai zafi da saurin gaske, kuma babu makawa za a sami sauye-sauye, a ɓangaren tawagar masu horaswa.

    Iraola zai yi aiki tare da Tommy Elphick da Shaun Cooper - waɗanda suka kasance tare da shi a Bournemouth - a matsayin masu horar da ƙungiyar farko.

  19. Akwai yiwuwar Rasha za ta iya shiga gasar Olympics ta 2028

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a iya ba wa ƴan wasan Rasha damar shiga gasar Olympics ta 2028 a Los Angeles bayan da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya ɗage dakatarwar da aka yi musu na wucin gadi.

    Hukumar ta IOC ta dakatar da kwamitin wasannin Olympics na Rasha a shekarar 2023 a matsayin martani ga yaƙin da ake yi a Ukraine.

    Amma ya ce an dakatar da haramcin kuma ƴan wasa daga Rasha za su iya sake yin gasa muddin suka "cika ƙa'idojin hana shan magungunan ƙara kuzari".

    Har yanzu ba a yanke shawara kan ko Rasha za ta iya nuna tutarta da launukanta da kuma takenta a wasannin Olympics ba.

    IOC ta ce ba za ta ci gaba da "da ƙin shirya taron na IOC a Rasha ko kuma gayyatar jami'an gwamnatin Rasha zuwa abubuwan da hukumar ta shirya".

    Wasu ƴan wasan Rasha sun shiga gasar Olympics ta Paris ta shekarar 2024 da kuma gasar Olympics hunturu ta shekarar nan a Milan a matsayin masu zaman kansu.

  20. Martinez ya yi murabus daga muƙaminsa na kocin Portugal

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Roberto Martinez ya tabbatar da cewa zai ajiye aikin koci bayan da Portugal ta fice daga gasar cin kofin duniya a zagaye na ƴan 16 a hannun Spain.

    Ɗan ƙasar Spain mai shekaru 52 ya ga tawagarsa ta sha kashi da ci 1-0 a wasan da aka buga a filin wasan Dallas Cowboys da ke jihar Texas.

    Rashin nasarar da portugal ta yi ya sa ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa zai yi ritaya ba tare da ya lashe babbar ƙyautar wasan ta duniya ba,bayan da wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya na Cristiano Ronaldo da Portugal ya ƙare da shan kashi a hannun Spain da ci 1-0 a zagaye na ƴan 16.

    Ronaldo ya fashe da kuka yayin da labarinsa na gasar cin kofin duniya ya ƙare a Dallas inda Mikel Merino ya zura ƙwallon da ya tabbatar da ficewar Ronaldo da tawagarsa.

    Wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar kuma zakaran gasar Euro 2016 ya zura ƙwallaye 976 a duk wasannin da ya bugawa ƙungoyoyinsa da kuma tawagar ƙasarsa.

    Ya zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya sau shida. Amma mafi kusancin da ya taɓa yi da lashe gasar shine lokacin da Portugal ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasarsa ta farko a 2006.

    Ya riga ya sanar da cewa wannan zai zama gasar cin kofin duniya ta ƙarshe - amma daga baya ya ce "Zan haɗu da iyalina kuma in yanke shawara cikin natsuwa" lokacin da aka tambaye shi ko zai ci gaba da bugawa ƙasarsa wasa.

    Amma tambayar da aka kasa amsawa ita ce ko da Portugal za ta sami damar lashe wannan gasar cin kofin duniya da kocin bai fuskanci matsin lambar farawa da Ronaldo a kowane wasa ba?