Sai da safe
Nan muka zo ƙarshen rahotonni a wanna shafi na yau Juma'a.
Muna tafe da wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.
Kafin lokacin, Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 17 ga watan Mayun, 2024.
Abdullahi Bello Diginza, Usman Minjibir and Umar Mikail
Nan muka zo ƙarshen rahotonni a wanna shafi na yau Juma'a.
Muna tafe da wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.
Kafin lokacin, Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Kotu ta yanke wa mutumin nan da ya kai wa mijin tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi hari hukuncin shekara 30 a gidan yari.
An kama David DePape da laifin kai hari da kuma yunƙurin yin garkuwa da jami'in gwamnatin Amurka a watan Nuwamban 2023 bayan shafe mako guda ana shari'a a San Fransisco.
Harin ya sa an kwantar da Paul Pelosi, mai shekara 84 a yanzu, a asibiti tsawon kwana shida sakamakon tsagewar ƙashin kai da kuma sauran raunuka.
Nancy ta so a yanke wa DePape "hukunci mai tsawo sosai".
Mai magana da yawunta ya ce iyalan Pelosi "suna alfahari sosai da jagoransu bisa ƙarfin halinsa" a daren da aka kai masa hari da kuma ƙoƙarin da ya yi wajen ba da shaida a kotu.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Shugaba Zelensky na Ukraine ya sanya hannu kan wasu sabbin dokoki biyu da za su taimaka wajen daukar karin soji yayin da Ukraine din ke fama da ƙarancin mayaka a filin daga.
An amince fursunoni su shiga aikin soji, kuma an ƙara yawan tarar da za a ci mutanen da suka ƙi amincewa su yi yaki.
Wakiliyar BBC ta ce ba kowane fursuna ba ne yake da wannan dama, wadanda aka kama da cin zarafi ta hanyar lalata, da wadanda suka kashe mutum biyu ko sama da kuma wadanda aka kama da laifin ta'addanci ba su cikin wannan dama.
Daga ranar Asabar duka mazan da suka haura shekara 18 za su sabunta bayanansu domin su yi daidai da sabbin dokokin ma'aikatar tsaron kasar.

Asalin hoton, Facebook/Abba El-Mustapha
Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta bayyana shirinta na fara shirya fim ɗin kurame a jihar.
Abba El-Mustapha, shugaban hukumar, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ƙungiyar kurame ta kai masa ziyara a ofishinsa.
El-mustapha "ya yi wa mambobin ƙungiyar alƙawarin haɗa su da dukkan wani da ake tunanin zai iya taimaka musu a ciki da wajen masana'antar Kannywood," a cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar.
Da yake magana yayin ganawarsu, jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar Kurame Rabi'u Aliyu Adam ya ce suna da gudummawar da za su iya bai wa al'umma musamman masu buƙata ta musamman.
"Manufar fara shirya finafinan ita ce samar da aiki ga kurame baya ga ilimantarwa tare da nishaɗantar da sauran masu buƙata ta musamman," in ji shi.
Rabi'u ya faɗa wa El-Mustapha da cewa tuni suka fara shirya wasu finafinai na kurame ta hanyar amfani da wayar salula, kamar yadda sanarwar ta bayyana, kuma ya nemi taimakon gwamnatin Kano wajen cikar burinsu.
Hukumomin Taliban a Afghanistan sun ce wani harin bindiga da aka kai a Bamiyan ya yi ajalin wasu 'yan kasar waje uku da wani ɗan Afghanistan ɗaya.
Wasu da dama kuma sun jikkata, bayan wasu 'yan bindiga biyu sun shiga kasuwa a mota sun kama harbin kan mai uwa da wabi.
Hotunan bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna mutane kwance a kan titi.
Kakakin Taliban ya ce an kama mutane hudu da ake zargi da hannu cikin harin.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta ta kori kocinta Massimiliano Allegri kwana biyu bayan ya jagoranci 'yan wasanta sun lashe kofin gasar Coppa Italia.
Juve ta doke Atalanta 1-0 a birnin Rome, amma an bai wa Allegri jan kati saboda hayagaga da ya yi wa alƙalan wasa.
Tuni mahukuntan gasar ƙwallon Italiya suka ƙaddamar da bincike a kan Mista Allegri.
"Korar ta biyo bayan wasu ɗabi'u a lokacin da kuma bayan tashi daga wasan Coppa Italia wanda kulob ɗin ke ganin sun saɓa da al'adun Juventus," a cewar sanarwar da kulob ɗin ya fitar.
Nasarar lashe kofin a ranar Talata ta sa Allegri ya kafa tarihin cin kofin har sau biyar a matsayin mai horarwa.

Asalin hoton, bringhomenow on Instagram
Dakarun sojin Isra'ila sun ce sun gano gawar mutum uku da ake garkuwa da su a Zirin Gaza, a cewar rundunar sojin ƙasar ta IDF.
Mutanen su ne Shani Louk, da Amit Buskila, da Itzhak Gelerenter, in ji ta. IDF ta ce an kashe su ne tun ranar 7 ga watan Oktoba kuma aka ɗauki gawar tasu zuwa Gaza.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito cewa an gano gawarwakin ne cikin wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hamas.
Mutum aƙalla 1,200 aka kashe lokacin da 'yan gwagwarmyar Falasɗinawa suka auka Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, sannan suka yi garkuwa da aƙalla mutum 252.
A matsayin martani, Isra'ila ta kashe sama da mutum 35,000, kamar yadda ma'ikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana labarin da "mai karya zuciya".
"Za mu dawo da dukkan mutanenmu da aka yi garkuwa da su, masu rai da matattu," in ji shi.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Hukumar ƙwallon kafa ta duniya Fifa ta ce tana son 'yan wasa su dinga ɗaga hannunsu sannan su haɗa su wuri guda a matsayin wata alama da za ta nuna an yi wariyar launin fata yayin wasa.
Manufar daga hannun ita ce shaida wa alkalin wasa an yi abin da ya saba ka'ida domin ya dauki mataki.
Wannan daya ne daga cikin matakan da Fifa take dauka domin yaki da nuna wariyar launin fata.
Shugaban Fifa Gianni Infantino ya ce "babu wani dalili da zai sa mu nuna wariya ga wani saboda launin fatarsa, idan kasashen duniya ba za su iya magance hakan ba to mu za mu yi kokarinmu a fannin kwallon kafa".

Asalin hoton, PA Media
Wata kotu a birnin Manchester ta samu wata malamar makaranta da laifin yin lalata da wasu ɗalibanta maza guda biyu.
An samu Rebecca Joynes, mai shekara 30, da laifukan lalata da ƙananan yaran har sau bibbiyu kowannesu.
An shaida wa alƙalin cewa hukumar makarantar ta kori malamar, saboda yin lalata da yaro na farko, sai kuma ta sake yi da yaro na biyu a lokacin da ake tsaka da tuhumarta.
Malama Joynes ta samu juna-biyu sakamakon lalata da yaron na biyun duk da cewa yana da ƙananan shekaru.
Malamar ta faɗa wa yaron cewa ba ta tsammanin za ta ɗauki ciki sakamakon lalatar.
An shaida wa kotun cewa malamar ta ja hankalin yaron ne mai shekara 15, ta hanyar saya masa wata belet (belt) mai ɗan karen tsada da ta kai fam 345, kafin ta yi lalata da shi a gidanta.
Ƙwararrun masu binciken kimiyya sun gano ƙwararan hujjojin aikata lalata a kan gadon malamar.
A lokacin da lamarin ya faru hukumar makarantar da takadar da malamar, yayin da 'yan sandasuka ƙaddamar da bincike.
Da farko an bayar da belinta sakamakon gaza samun hujjar alaƙarta da yaron da bai kai shekara 18 ba.
To amma daga bisani sai 'yan sanda suka gano cewa ta jima tana alaƙa da wani ɗalibin da suka ayyana a matsayin yaro.
A karon farko yaron ya taɓa zuwa gidanta a lokacin yana mai shekara 15, haka kuma bayan ya cika 16, ya sake komawa gidan suka sake aikata lalata da malamar, lamarin da ya sa ta samu juna-biyu.

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani matashi ya cinna wa wani masallaci a jihar.
A yau ƙarin mutum huɗu sun mutu a jiya adadin waɗanda suka mutun ya kai 11.
Sauran mutanen da suka jikkatan na kwance a asibiti, inda suke samun kulawar likitoci.
A ranar Laraba da asuba ne matashin ya cinna wa masallacin wuta bayan ya yayyafa wa masallacin fetur tare da kulle duka ƙofofin masallacin.
Rundunar 'yan sandan jihar dai na ci gaba da gudanar da bincike kan faruwar lamarin.
Ga Rahotan Zahraddeen Lawan daga Kano
Mai shigar da ƙara na musamman na ƙasar Ghana da ke yaƙi da cin hanci, Kiss Agyebeng na fuskantar tsigewa kan ƙarya ƙa'idar sayen motoci na musamman na ofishinsa.
Tsohon mai shighar da ƙara na ƙasar, Martin Amidu ya shigar da ƙorafin, sannan kuma ya zargi saɓa ƙa'idar aiki daga ɓangaren alƙalai da hukumomin shari'a, wani batu da Kiss Agyebeng ya bijiro da shi a baya.
Haka kuma mista Amidu ya yi zargin keta haƙƙin bil-adama a lokacin kamawa da tsare 'yan siyasar da ake zargi da aikata laifukan cin hanci, da tauye 'yancin labarai, da rashin bin ƙa'ida wajen naɗe-naɗen muƙamai.
Mai shigar da ƙarar ya ce ya buƙaci samun jawadlin sunayen duka ma'aikatan ofishin mai shigar da ƙarar na musamman da kuma albashinsu, amma sai aka hana shi saboda dalilai na tsaro.
Shugaban ƙasar, Nana Akufo Addo ya miƙa ƙorafin zuwa ga alƙalin alƙan ƙasar, Gertrude Torkonoo, wanda zai sake nazarinsa tare da ɗauka matakin gudanar da bincike ko akasin hakan.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin mulkin sojin Gabon sun musanta zargin da lauyoyin iyalan hamɓararren shugaban ƙasar suka yi na cewa ana azabtar da matarsa Sylvia Bongo da baban ɗansa Noureddin a inda ake tsare da su.
A ranar Talata ne lauyan ya ce hamɓararren shugaban ƙasar tare da 'ya'yansa biyu sun fara yajin cin abinci, domin nuna rashin jin daɗinsu kan zargin azabtarwa ciki har da duka da jona musu wayar lantarki.
Sun ƙara da cewa za su gabatar da ƙorafinsu a kotun birnin Paris game da zarge-zargen.
To sai dai yayin da take gabatar da jawabi a gidan talbijin na ƙasar, kakakin gwamnatin ƙasar, Laurence Ndong ta ce zarge-zargen ''karairayi ne kawai da aka ƙirƙira don a ɓata wa gwamnatin ƙasar suna''.
"Gwamnati na sanar da jama'a cewa waɗannan mutane ba sa fuskantar kowane irin nau'in azabtarwa ko cutarwa kamar yadda lauyansu yake iƙirari,'' inji kakakin gwamnatin.
Ta kuma musanta batun cewa hukumomin ƙasar sun hana Bongo ficewa daga ƙasar ko karɓar baƙi, ciki har da lauyoyinsa da iyalansa a gidan da yake zaune.
A watan Agustan shekarar da ta gabata ne sojoji suka kifar da gwamnati Bongo, mai shekara 65, jim kaɗan bayan lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da taƙaddama.
Ali Bongo ya kasance shugaban ƙasar tun 2009 lokacin da ya gaji mahaifinsa da ya mulki ƙasar na fiye da shekara 40.

Asalin hoton, AFP
Al'ummar Afirka ta Kudu mazauna ƙasashen waje sun fara kaɗa ƙuri'unsu a yau Juma'a, gabanin ranar babban zaɓen ƙasar na 29 ga watan Mayu.
'Yan ƙasar mazauna ƙasashen Aljeriya da Masar da Iran da Jordan da Saudiyya da kuma Siriya za su kaɗa ƙuri'unsu a ofisoshin jaƙadun ƙasar tsakanin ƙarfe 7:00 na safe zuwa 7:00 na maraice agagon ƙasashen.
Haka kuma a ranar Asabar 'yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen duniya fiye da 100 za su kaɗa nasu ƙuri'un.
Za kuma a faɗaɗa ƙuri'ar zuwa ranar Lahadi a London, inda kusan 'yan ƙasar 76,580 watau kimanin kashi ɗaya bisa uku na adadin 'yan ƙasar mazauna ƙetare.
Sai dai 'yan ƙasar mazauna Isra'ila da Ukraine da Sudan da ke fama da rikice-ikice, ba za su samu damar yin zaɓen ba

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami'in kamfanin kuɗin kirifto na Binance, Tigran Gambaryan wanda ya shafe fiye da kwana 40 a tsare a gidan yarin Kuje da birnin tarayyar.
Yayin da yake gabatar da hukuncin, mai shari'a Emeka Nwite ya ce ya yi nazarin takardar neman belin da aka gabatar masa, sai dai ya ce akwai yiwar mista Gambaryan zai iya tserewa idan aka bayar da belinsa.
Hukumar EFCC ce gurfanar da jami'in tare da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla, da kuma kamfanin Binance a gaban kotun bisa zarge-zarge biyar masu alaƙa da almundahanar kuɗi da ya kai kimanin dala miliyan 35.4 a shafin kamfanin.
Hama ma hukumar tara haraji ta ƙasar, FIRS na zargin mutanen uku da laifuka hudu da suka jiɓanci ƙin biyan haraji.
Waɗanda ake zargin dai sun musanta duka zarge-zargen.
An dai fara shari'ar ta yau ne kan almundahanar kuɗi, ta hanayr gabatar da shaida daga hukumar kula da hannayen jari ta ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai shugaban kamfanin na Binance, Richard Teng ya zargi wasu jami'an gwamnatin Najeriya da neman a ba su cin hancin dala miliyan 150, domin kashe maganar.
Zargin da hukumomin ƙasar suka musanta, suna masu bayyana shi da ''ɓata suna'' da kuma kawar da hankalin mutane kan shari'ar da ke gudana.
Kawo yanzu dai ba a san inda Nadeem Anjarwalla yake ba bayan tserewarsa daga hannun hukumomin Najeriya.
To sai dai hukumomin ƙasar sun ce suna aiki da jami'an 'yan sandan ƙasa da ƙasa, a wani mataki na samun sammacin ƙasa da ƙasa a ƙasa domin kama shi a duk inda yake.

Asalin hoton, Press Association
Gwamnan yankin Darfur da ke yammacin Sudan, Minni Minnawi ya buƙaci fararen hula su ɗauki makamai domin kare kansu da kuma birnin El-Fasher daga harin mayaƙan RSF da suka yi wa birnin ƙawanya.
Fiye da mutum 60 ne suka mutu yayin da ɗaruruwa suka jikkata tun bayan ɓarkewar sabon faɗa a yankin ranar 10 ga watan Mayu, kamar yadda ƙungiyar likitoci da DWB ta bayyana.
"Muna ankarar da mutane da su kare rayukansu da dukiyoyinsu a birnin El Fasher,''kamar yadda mista Minnawi ya wallafa a shafinsa na X.
Kiran da gwamnan ya yi martani ga wani kira da ake zargin RSF ta yi na cewa na ''ƙaddamar da gangamin ɗaukar mayaƙa a duka yankunan ƙasar'', domin far wa birnin.
To sai dai RSF din ta musanta zargin, inda ta zargi gwamnatin ƙasar da ''haifar da yamutsi a yankin Darfur''.
Mayaƙan RSF da sojojin Sudan, da ke samun goyon bayan ƙungiyoyin masu ɗaukie da makamai na yankin Darfur na ci gaba da ɗora wa juna alhakin rura wutar rikici a birnin El Fasher.
Kodinetar MDD a Sudan, Clementine Nkweta-Salami, ta yi gargaɗin cewa ci gaba da rikici a yankin na yin barazana ka rayukan fararen hula fiye da 800,000.
A watan Afirlun shekarar da ta gabata ne Sudan ta sake faɗawa yaƙin basasa, kuma duk wani yunƙurin na shiga tsakani da ƙasashen duniya suka yi bai yi nasara ba.

Asalin hoton, ..
Kotun Duniya na ci gaba da sauraron martanin Isra'ila kan zargin da Afirka ta Kudu ke yi wa ƙasar da na aikata kisan ƙare-dangi a Rafah.
Isra'ila ta kare matakin kai hare-haren da cewa tana yi domin cin galaba kan ƙungiyar Hamas.
Isra'ilar ta ce hujjojin da aka gabarta wa kotun karairayi ne da aka samu da ƙungiyar Hamas
Wannan ce rana ta biyu na sauraron ƙarar da Kotun Duniya ke yi kan batun, yayin da lauyoyin Afirka ta Kudu suka gabatar da hujjojinsu ranar Alhamis.
Afirka ta Kudu ta ce dole ne Isra'ila ta dakatar da ayyukan soji a yankin Gaza cikin gaggawa, ciki har da Rafah inda fiye da Falasɗinawa miliyan guda da suka rasa muhallansu ke gudun hijira a wurin