Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Za a gudanar da zanga-zangar adawa da yi wa kundin mulkin ƙasar Togo garambawul

    Jam'iyyun hamayya da ƙungiyoyin fararen hula a Togo sun haɗe kai tare da alƙawarin gudanar da zanga-zanga, bayan majalisar ƙasar ta sahale a yi wa kundin mulkin ƙasar garambawul.

    Gamayyyar ta ce nan da kwanaki masu zuwa za ta dauki mataki domin nuna ƙin amincewa da ƙudurin majalisar, wanda suka alaƙanta da juyin mulki.

    Kudurin dai na son Togo ta tashi daga kasar da ke bin tsarin mulkin shugaban ƙasa mai cikakken iko ta koma na Firaiminista.

    'Yan hammaya sun ce wannan matakin share fage ne ga shugaba Faure Gnassingbe domin ya ci gaba da zama kan iko.

    Jam'iyyarsa ce ke da rinjaye a majalisar ƙasar, kuma ko shakka babu za a iya sake zaɓensa a matsayin shugaba.

  3. Labarai da dumi-dumi, Majalisar Amurka ta amince a bai wa Ukraine taimakon dala biliyan 60

    Majalisar wakilan Amurka

    Asalin hoton, House of Representatives

    Majalisar wakilan Amurka ta kaɗa kuri'ar amincewa da bai wa Ukraine taimakon dala biliyan 60.8.

    Taimakon ya kunshi tallafin soji da harsasai da kuma makaman kare sararin samaniya da Ukraine ke buƙata.

    Ƴan majalisa 311 suka amince, yayin da 112 kuma suka ki.

    Wannan dai wani muhimmin lokaci ne ga Ukraine, wadda ke matukar buƙatar taimakon soji, a daidai lokacin da take fafutukar yaƙi da mamayar Rasha.

    Ana sa ran majalisar dattijan ƙasar za ta amince da matakin nan da kwanaki masu zuwa, kafin shugaba Biden ya sanya hannu.

    Jami'ai sun shaida wa kafafen yaɗa labaran Amurka cewa wasu makamai na iya isa Ukraine cikin mako ɗaya.

  4. Mutum 60 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

    Hatsarin kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Kimanin mutum 60 ne suka mutu a wani hatsari kwale-kwale da ya kife da su a tekun Mpoko da ke kusa da Bangui babban birnin Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya.

    Hukumomi sun ce mafi yawan fasinjojin 300 da ke cikin jirgin, na kan hanyar su ne ta zuwa wata jana'iza lokacin da ya fara nutsewa.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka riƙa faɗawa cikin tekun domin su isa gaɓar ruwan.

  5. NAFDAC ta ƙwace jabun kayayyaki da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 50 a kantunan Abuja

    NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC NIGERIA/X

    Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta kai samame a manyan kantunan babban birnin Najeriya Abuja, inda ta ƙwace jabun kayayyakin da dama.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce sun kai samamen ne a kasuwannin Garki, Wuse, Utako, Kugbo, Nyanya, da kuma Mararaba, inda suka kwace jabun kayan kwalliya da magunguna.

    NAFDAC ta ce ta gano jabun kayan kwalliya tare da kama su a Shagunan Sahad, H-Medix, da kuma kasuwanni daban-daban, yayin da aka ƙwace jabun magunguna kuma a kasuwar Utako.

    Sauran kayayyakin da hukumar ta ƙwace sun haɗa da mayukan shafawa na NIVEA, abubuwan tsabtace bayan gida na Harpic, da kuma turaren kamshi na ɗaki.

    NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC NIGERIA/X

    NAFDAC ta ce kuɗin jabun kayayyakin da ta ƙwace ya kai Naira miliyan 50, inda ta ce kuɗin mayukan shafawa na NIVEA kaɗai ya kai Naira miliyan 45.

    Mista Embugushiki-Musa Godiya, shugaban sashen bincike na hukumar a birnin Abuja, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake sayar da kayayyakin da ba su da inganci, musamman ma jabun mayukan shafawa irin NIVEA da ake sayarwa da tsada fiye da na kayayyakin da aka amince da su.

    "Waɗannan jabun kayayyaki na da illa sosai ga lafiyar lafiyar jiki, akwai yiwuwar kamuwa da cutar daji, da lalacewar koda, da kuma fatar jiki," in ji shi.

    Hukumar ta sake jaddada aniyar ta na kawar da jabun kayayyaki da kuma kare lafiyar al’umma.

    NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC NIGERIA/X

    NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC NIGERIA/X

  6. An rufe Jami'ar Jihar Plateau bayan mutuwar wani ɗalibi

    Jami'ar jihar Plateau

    Asalin hoton, PLATEAU STATE UNIVERSITY, BOKKOS/ FACEBOOK

    Jami’ar Jihar Filato, da ke Bokkos, ta dakatar da dukkan harkokin koyarwa a makarantar har na tsawon kwanaki goma, bayan wani hari da aka kai da ya hallaka wani ɗalibi.

    Ɗalibin wanda ke matakin aji biyu (200 level) a fannin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma'a a harin da wasu suka kai harabra jami'ar.

    Wani malamin jami'ar, Yakubu Ayuba, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce, “Bayan wani abin bakin ciki da ya faru a jami’ar Jihar Filato, Bokkos, da kewaye a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, 2024; kuma bisa la’akari da illolin da wannan al'amari zai yi wa ɗalibai da ma’aikatan jami’ar, hukumar gudnarwa ta ɗauki matakin rufe jami’ar na tsawon kwanaki 10 daga ranar 19 ga Afrilu, 2024.

    Yakubu ya ce an yi haka ne don ba da dama na ganin yanayin tsaro ya inganta a jama'ar.

    "Don haka, an dakatar da jarabawar zangon karatu na farko da ake ci gaba da yi, inda za a koma rubuta ta ranar Alhamis 2 ga watan Mayu, 2024," in ji shi.

    Bugu da kari, jami'ar ta kuma samar da motocin bas don kai ɗaliban da za su maƙale zuwa Barikin Ladi.

    Idan za a iya tunawa, a ranar Juma'a ne, wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Mangu da Bokkos inda aka ce an kashe mutane 15 a yankunan.

  7. Hotuna bayan harin Isra'ila a birnin Rafah

    Sojojin Isra'ila na ci gaba da lugudan wuta a wasu sassan Zirin Gaza.

    Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza ta ce aƙalla mutum tara aka kashe a wani hari da aka kai kudancin birnin Rafah.

    Ga wasu hotuna na yadda wajen da aka kai wa harin yake.

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Zaftarewar ƙasa ta hallaka ɗaya, ta ɗaiɗaita sama da 2,000 a Burundi

    Zaftarewar ƙasa

    Asalin hoton, DMICOM SEED

    Wani yaro ɗan shekara biyar ya rasa ransa, sannan sama da mutane 2,400 ne suka rasa muhallansu sakamakon zaftarewar ƙasa da ta afku a daren Juma'a a Burundi.

    Zaftarewar ƙasar ta afku ne a tsaunin Gabaniro a yankin Gitaza da ke lardin Rumonge a yammacin ƙasar.

    A cewar shugaban yankin, Muhuta Niyonsavye Scholastique, ya ce yanzu haka iyalai 350 ne suka ɓace bayan faruwar lamarin.

    "Gaba-ɗaya dutsen Gabaniro ya ruguje" kuma sama da hekta 500 na gonaki sun tafi, kamar yadda ya shaida wa tashar tashar BBC ta Great Lakes.

    Zaftarewar ƙasa

    Asalin hoton, ADDMICOM SEED

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mazauna yankin ke ta kukan neman taimako.

    Shugaban lardin Muhuta ya ce a halin yanzu mutum 2,485 sun sami mafaka a makarantar Ecofo Kirasa ba tare da wani abu da za su kai bakin salati ba, inda suke jiran taimako.

    Zaftarewar ƙasa

    Asalin hoton, DMICOM SEED

  9. Za a kawo wa Najeriya jiragen yaƙi shida daga Italiya a ƙarshen 2024

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya na sa ran karɓar jiragen yaƙi shida ƙirar M-346 daga Italiya zuwa ƙarshen shekarar 2024.

    A watan Nuwamban 2023 me rundunar sojin saman Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar sayen jiragen yaƙi 24 daga wani kamfani a Italiya.

    Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito cewa a ranar Laraba, mataimakin shugaban kamfanin Claudio Sabatino ya ziyarci shalkwatar sojojin saman Najeriya inda ya gana babban hafsan sojin saman ƙasar.

    Jaridar ta ambato wata sanarwa da aciki mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet, na cewa Sabatino ya tabbatar wa da babban hafsan sojin saman ƙasar cewa za a kawo rukunin farko na jiragen a kan lokaci.

  10. Amurka ta amince ta kwashe dakarunta daga Nijar

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Amurka na shirin kwashe duka dakarunta daga Jamhuriyar Nijar, domin kawo ƙarshen yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi.

    A ranar Juma'a ne Amurka ta bayyana cewa za ta rufe sansanin jiragenta marasa matuƙa a kusa da Agadez.

    Shugabannin mulkin sojin Nijar sun ƙulla sabon ƙawance da ƙasar Rasha, bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum a shekarar da ta gabata.

    Nijar ta kasance ƙasar da Amurka ta dogara da ita wajen gudanar da ayyukanta na yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

    Nan gaba kaɗan ne tawagar wakilan Amurka za su je birnin Yamai domin shirya yadda za su kwashe dakarun ƙasar fiye da 1,000.

    Hakan na zuwa ne bayan tattaunawar da ta gudana a birnin Washington tsakanin mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell, da firaministan Nijar ɗin Ali Lamine Zeine.

  11. 'Sabon faɗan da ya ɓarke tsakanin Tigray da Amhara ya raba mutum 29,000 da muhallansu'

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin da ya ɓarke baya-bayan nan a ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da tashin hankali a kan iyakar arewacin yankin Tigray da yankin Amhara a ƙasar Habasha ya yi sanadin raba kusan mutum 29,000 da gidajensu.

    Faɗan ya ɓarke a makon da ya gabata a gundumar Raya Alamata, tsakanin sojojin yankunan biyu, duka yankunan biyu dai na iƙirarin mallakar gundumar.

    Gundumar ta kasance ƙarƙashin ikon Tigray har zuwa ɓarkewar rikicin 2020, inda dakarun Amraha suka ƙwace iko da ita.

    Bayan ɓarkewar sabon faɗan ne dakarun Tigray suka yi yunƙurin kutsawa wani ɓangare na gundumar da nufin ƙwace ta.

    Tuni dai ofisoshin jakadun ƙasashen Yamma ciki har da Birtaniya da Amurka suka fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa domin nuna damuwa kan ɓarkewar sabon rikicin, suna masu kiran a dakatar da faɗan.

    A ƙarshen shekarar 2022 ne aka kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka kwashe aƙalla shekara biyu aka gwabzawa tsakanin sojojin gwamnatin Habasha dakarun Tigray.

  12. Lafiya Zinariya kan cutar shawara tsakanin jarirai

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  13. Yara takwas sun mutu bayan ƙasa ta rufta musu a wata mahaƙa a Kebbi

    .

    Asalin hoton, Engr. Adamu Attahiru

    Kimanin yara takwas sun mutun bayan ƙasar gini ta rufta musu a mahaƙar ƙasar ginin ta Dustin Dukku da ke unguwar Badariya a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi.

    Shugaban ƙaramar hukumar Hon. Muhammad Dahiru Ambursa, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara shirye-shiryen yi wa yaran jana'iza.

    Ya kuma ce akwai wasu ƙarin yara biyu da suka jikkata ciki har da wanda ya karye a ƙafa.

    To sai dai wani mutum da abin ya faru a gaban idonsa ya shaida wa BBC cewa yara tara ne suka rasu, lokacin iftila'in da ya faru da safiyar ranar Asabar

    Shugaban karamar hukumar ya ce mafi yawa daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su almajirai ne waɗanda ke aikin haƙar ƙasar gini a yankin.

    Honarabul Ambursa ya ce ya bayar da umarnin dakatar da haƙar ƙasar gini a wurin.

    ''Mun bayar da umarnin killace wurin da waya tare da saka alamar da ke nuna cewa an hana haƙar ƙasar gini a wurin, mun kuma buƙaci hakimai da sauran iyayen ƙasa da su saka a yi shela, don hana mutane haƙar ƙasar gini a wannan wuri'', in ji shi.

    Masu ƙaramin ƙarfi dai kan yi amfani da ƙasa wajen yin bulon ƙasa da za su yi amfani da shi wajen yin gine-ginen musamman a garuruwa da ƙauyuka a Najeriya.

    ..

    Asalin hoton, Engr. Adamu Attahiru

  14. Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ta shirya bikin yaye ɗalibai

    ..

    Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ta shirya bikin yaye ɗalibai kimanin 22,932.

    ..

    Shugaban jami'ar Farfesa Suleiman Bilbis ne ya bayyana haka a yayin taron yaye ɗaliban da jami'ar ta shirya, a babban ɗakin taron jami'ar.

    Ya ƙara da cewa daga cikin ɗaliban, akwai waɗanda za su samu digirin digirgir, da digiri na biyu, da kuma digiri na farko.

    Wakilin BBC da ke wurin ya ce taron ya samu halartar manyan baƙi daga cikin wajen jihar Sokoto.

    .
    Bayanan hoto, Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya tare da sarkin Kano na daga cikin baƙin da suka halarci taron
    ..
    .
    Bayanan hoto, Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero na daga cikin mutanen daaka karrama a taron
    ..
    Bayanan hoto, An kuma ɗaga darajar Farfesa Toyin Falola a lokacin taron
    .
    Bayanan hoto, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar lll (a tsakiya), mai martaba sarkin Kano Alhaji (DR) Aminu Ado Bayero (dama), sai Sheikh Mallam Bello na Mallam Boyi (hagu), wanda aka karamma da digirin girmamawa.
  15. Gane Mini Hanya kan cutar hanta

    Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) a baya-bayan nan, ta bayyana matuƙar damuwa a kan ƙaruwar mutanen da ke mutuwa sanadin cutar hanta, inda ta ce a kullum mutum 3,500 ne ke mutuwa dalilin cutar.

    Sabbin alƙaluma, a cewar rahoton cutar hanta na duniya a 2024, daga ƙasa 187, ya nuna cewa ƙiyasin mutum miliyan ɗaya da 300,000 ne cutar hanta ta yi sanadin mutuwarsu a 2022, idan aka kwatanta da mutum miliyan ɗaya da 100,000 a 2019.

    Ƙiyasin na WHO ya nuna cewa mutum miliyan 254 ne ke fama da cutar hanta nau'in B, sai kuma wasu miliyan 50 da ke fama da nau'in cutar hanta ta C a 2022.

    Rahoton ya ce kashi biyu cikin uku na masu cutar hanta nau'in B da C suna ƙasashe 10 a ciki har da Nijeriya da Habasha da Indiya da Rasha.

    Kan haka ne, Mukhtari Adamu Bawa ya zanta da Dr. Hajara Ɗalhatu Musa, likita a babban asibitin Wuse na Abuja, kuma ta fara da bayani a kan ko mece ce cutar hanta?

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  16. Tunde Onakoya: Dan Najeriya ya kafa tarihi a wasan dara

    .

    Asalin hoton, AP

    Ɗan Najeriyar nan da ya ƙware a wasan dara, Tunde Onakoya ya kafa tarihin daɗewa yana wasan dara a duniya.

    Mista Tunde ya kafa tarihin ne ranar Juma'a da daddare bayan shafe sa'o'i 58 yana wasan ba tare da gajiyawa ba, a gaban ɗimbin magoya bayansa a fitaccen dandalin Time Square da ke birnin New York na ƙasar Amurka.

    Waɗanda ke riƙe da kambun, Hallvard Haug Flatebo da Sjury Ferkinstad sun shafe sa'a 56 da minti tara da sakanni 37 suna wasan dara a 2018.

    Onakoya na fatan tara dala miliyan ɗaya da zai zuba a gidauniya koyar da wasan dara ga kananna yara.

    Kuɗin, a cewarsa, zai taimaka wa ilimin wasan dara ga miliyoyin yara.

    Ɗaruruwan magoya baya sun yi dafifi a dandalin Times Square da ke New York a Amurka domin nuna masa goyon baya ciki har da fitaccen mawaƙin Najeriya, Davido.

    An yi ta kiɗe-kiɗe da bushe-bushe domin ƙara masa ƙwarin gwiwa, tare da kai nai'ikan abincin Najeriya wajen da yake wasan, cikin har da shinkafar dafa-duka mai ɗimbin farin jini a ƙasar.

    A Najeriya ma, mutane na nuna goyon bayansu ga Onakoya yayin da suke kallon yadda yake nuna bajinta a ƙoƙarin kafa tarihi ta manhajar Twitch.

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya wallafa saƙon goyon baya ga Mista Onakoya a shafinsa na intanet inda ya ƙara ƙarfafa masa gwiwa da neman ya ƙara fito da Najeriya a idon duniya.

    Shi ma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya faɗa wa Onakoya cewa yunƙurin da yake "babbar manuniya ce cewa ɗaukaka na iya zuwa daga ko ina."

  17. 'Hari ta sama da Isra'ila ta kai Rafah ya kashe aƙalla mutum tara'

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce aƙalla mutum tara aka kashe, yayin da wasu gommai suka jikkata a wani hari da aka kai kudancin birnin Rafah, bayan da jiragen saman Isra'ila da tankokin yaƙin suka farwa wasu sassan yankin cikin dare.

    Ma'aikatar ta ce wani harin ya faɗa kan ginin wani gida a birnin.

    Lamarin na zuwa ne bayan da jami'an Amurka suka nuna damuwa kan yadda Isra'ila ke shirin ɗaukar matakin soji a Rafah.

    Fadar White House ta ce wakilan firministan Isra'ila sun amince da yin duba kan damuwar da Amurkan ke nunawa.

    Amurka ta sha kiran Isra'ila da kada ta ƙaddamar da mummanan hari a Rafah, domin kauce wa cutar da fararen hula a Gaza.

    Haka kuma an samu rahoton cewa wani hari ta sama ya faɗa kan sansanin 'yan gudun hijira na Al-NuseiratAl-Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

  18. Mutumin da ya cinna wa kansa wuta a wajen kotu a Amurka ya mutu

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Mutumin nan da ya cinna wa kansa wuta a wajen kotun Manhattan - da ke sauraron karar da ake yi wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump - ya mutu

    A ranar Juma'a ne Maxwell Azzarello, mai shekara 37, ya watsa wa kansa wani abu mai ruwa-ruwa kafin ya cinna wa kansa wuta a wajen harabar kotun.

    Lamarin ya faru ne a lokaci da ake dab da kammala sauraron ƙarar da ake yi Donald Trump.

    Daga baya kuma tsohon shugaban MAurkan ya fice daga harabar kotun jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

    Tuni jami'an 'yan sanda suka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, inda daga baya hukumomin asibitin suka bayyana rasuwarsa.

    Kawo yanzu dai ba a san dalilin mutumin na aikata hakan ba

  19. 'An raunata masu goyon bayan Iran a Iraƙi'

    Gamayyar ƙungiyoyi masu goyon bayan Iran a Iraki sun ce membobinsu da dama sun jikkata sakamakon harin da aka kai sansaninta da bama-bamai.

    Hotunan bidiyo internet sun nuna tashin wata mummunar gobara a yankin da ke makwabtaka da Iskandariya.

    Majiyoyin tsaron Iraqi sun bayyana lamarin a matsayin wani harin bam da ya rutsa da makamai da motoci. Ya yinda ake ci gaba da laluben wadanda suka samu muggan raunuka.

    A baya-bayan wata 'kungiyar dakarun sa kai ta kaiwa jami'an Amurka hari, sai dai cibiyar tsaro ta Pentagon ta ce ba ta da hannu a harin da ba wanda ya ɗauki alhakin kaddamar da shi.

  20. Iran ta ce za ta mayar da mummunan martani idan Isra'ila ta takaleta

    ,

    Asalin hoton, ,

    Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amirabdollahian, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da mummunan martani cikin gaggawa idan Isra'ila ta yi abin da ya saɓa wa muradunta.

    Mista Amirabdollahian ya shaida wa kafar yaɗa labaran NBC ta Amurka kasa da kwana guda bayan wani harin da ake kyautata zaton jiragen yakin Isra'ila ne suka kai Isfahan da ke tsakiyar kasar Iran.

    Wakiliyar BBC ta ce takaitaccen harin isra'ila, wanda ba ta ɗauki alhaki ba a hukumance, ya ba Iran damar sassautawa kafin daukar mataki.

    Martanin da Tehran ta yi a ranar Juma'a - wanda ta yi watsi da al'amuran da suka faru a safiyar Juma'a - ya nuna alamun za a iya kwantar da tarzoma tsakanin ɓangarorin biyu masu rikici da juna