Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Rufewa

    To masu bibiyar mu sai da safe. Da fatan za a kasance da mu gobe da misalin karfe 8:00 na safen. Mun gode.

  2. Sudan ta dakatar da gidajen Talbijin na Larabawa saboda rashin jituwa a tsakaninsu

    Sudan ta dakatar da wasu gidajen Talbijin na ƙasashen Larabawa guda uku, inda ta zarge su da "rahoton da ba su dace ba da kuma wallafa labarai masu illa".

    Gidajen talabijin ɗin sun haɗa da Sky News Arabia Mallakar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Al Arabiya da Al Hadath mallakar Saudiyya, sun yi rahoto sosai kan yaƙin basasa da rikicin siyasa a Sudan.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar, Graham Abdel Gader, ya ce dakatarwar ta biyo bayan sakamakon "rashin kwarewa da aiki da gaskiya da ake bukata wajen ba da rahoto da kuma rashin sabunta lasisin su.

    Dakatar da Sky News Arabia ta UAE kuma ta samo asali ne daga "wallafa rahoton da bai kamata ba, da kuma labarai masu illa a cewar kafofin watsa labarai na cikin gida.

    Gidajen talabijin na Al Hadath da Al Arabiya sun ce ba a sanar da su kan dakatarwar a hukumance ba kuma sun saba sabunta lasisin su.

    Dakatarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta zargi Sky News Arabia da yaɗa wani jabun rahoton 'yan bindiga.

    Tashar ta yi amfani da faifan bidiyon harin da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabab ta kai a Somaliya a shekarar 2016 a wani labari na kungiyoyin 'yan ta'adda da ake zargin suna yaƙi tare da sojojin kasar Sudan.

    Dangantaka tsakanin Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi tsami ne bayan da sojojin Sudan da kafafen yaɗa labaran ƙasashen Yamma suka zargi UAE da samar da makamai ga dakarun RSF a rikicin da aka kwashe kusan shekara guda ana gwabzawa.

    Kungiyar 'yan jarida ta Sudan (SJS) ta bayyana matakin a matsayin "tauye 'yancin fadin albarkacin baki da kuma 'yan jarida".

  3. Kotu ta bai wa hukumar DSS damar tsare wani 'ɗan ISIS' tsawon kwana 60

    ..

    Asalin hoton, DSS

    Babbar kotun tarayya a Abuja ta bai wa hukumar tsaron farin kaya ta DSS izinin ta ci gaba da tsare wani, Emmanuel Osase, wanda ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar ISIS.

    A wani hukunci da Mai shari'a Inyang Ekwo ya yanke, ya bai wa hukumar tsaron damar su ci gaba da tsare Emmanuel Osase a wurinta tsawon kwana 60 don ta kammala bincike kan zargin alaƙarsa da ƙungiyar, wadda hukumomi suka ce ta 'yan ta'adda ce.

    Umarnin tsarewar ya zo ne bayan wata buƙatar wucin gadi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gabatar ta hannun lauyoyinta, A.A Ugee.

    Daga bisani kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

    Jaridar Vanguard ta ambato takardu kotu na cewa an kama Emmanuel Osase ne saboda tallafa wa ISIS ba kawai wajen yayata saƙonninta ba, da kushe tsarin mulkin dimokraɗiyyar Najeriya, har ma da kiran a kai hare-haren ta'addanci kan Najeriya da al'umominta da 'yancin kasancewarta ƙasa.

  4. An kama tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya Luis Rubiales

    Luis Rubiales

    An kama tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales, a wani bangare na binciken da ake gudanarwa kan zargin aikata cin hanci da rashawa.

    Ana zarginsa da karbar wasu kudaden ba bisa ka'ida ba lokacin da ake tattaunawa kan yarjejeniyar shirya gasar cin kofin Spanish Super Cup a kasar Saudiyya.

    Mista Rubiales zai gurfana a gaban kotu bayan ya sumbaci wata ‘yar wasa ba tare da izininta ba a lokacin da tawagar kasar Sifaniya ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata.

    Masu gabatar da kara na neman a daure shi na tsawon shekara biyu da rabi a gidan yari.

  5. Fiye da mutum 50,000 sun tsere daga Haiti bayan tashe tashen hankulan ƴan daba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubun dubatar mutane ne suka tsere daga babban birnin kasar Haiti, Port-au-Prince, domin gujewa barkewar tashe-tashen hankulan gungun 'yan bindiga a makonnin da suka gabata.

    Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutum 53,000 sun bar ƙasar tsakanin 8-27 ga watan Maris.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yankunan karkara da mutanen da dama suka koma ba su da kayan aiki da za su tunkari kwararowar mutanen da suka rasa matsugunansu.

    A halin da ake ciki kuma, wasu gungun 'yan bindiga na kai hare-hare kan harkokin kasuwanci a babban birnin ƙasar, suna kona shagunan sayar da magunguna tare da lalata makarantu.

    Rundunar ‘yan sandan kasar Haiti ta yi nasarar daƙile harin da aka kai a fadar shugaban kasar a ranar Litinin din da ta gabata, amma wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kutsa kai a asibitin jami’ar Jihar Haiti da ke kusa da wurin da aka fi sani da HUEH, domin yin amfani da shi a matsayin cibiyar kwamandojin su.

    Ƴan daban ba kawai babban tashar jiragen ruwa na Port-au-Prince su ke iko da shi ba, har ma da yawancin hanyoyin shiga birnin, wanda ke yin wahalar jigilar magunguna.

    Yayin da halin da ake ciki a asibitocin babban birnin kasar ke ƙara ta'azzara, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa zuwan dubun dubatar mutanen da suka rasa matsugunansu a yankunan karkara da ba su da isasshen kayan aiki don tunkarar lamarin, shi ma ya na haifar da kalubale mai tsanani.

    Galibin waɗanda ke tserewa daga Port-au-Prince sun nufi kudu, zuwa yankunan da har yanzu ke fama da sakamakon girgizar kasar da ta afku a shekarar 2021, wadda ta kashe mutane sama da 2,000.

  6. Tinubu ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu.

    Ya sa hannu kan dokar ce a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Dokar mai taken kudurin sauya wa dokar bai wa dalibai rancen karatu fasali ta 2024, an samar da ita ne domin kafa asusun tallafa wa daliban manyan makarantu.

    A watan Yunin 2023 ne dai shugaban ya fara rattabawa kudirin hannu to amma sakamakon wasu kurakurai da aka gano, ya sa ba a iya fara aiwatar da tsarin ba, inda shugaban ya sake mayarwa majalisa domin yin kwaskwarima.

    Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma in ji shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Kasar Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kudi.

  7. Naɗa sabon kocin Kamaru Marc Brys ya ba da mamaki a ƙasar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafar Kamaru ta bayyana mamakinta bayan da ma'aikatar harkokin wasannin ƙasar ta naɗa Marc Brys a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ta Indomitables.

    Sabon kocin ɗan asalin Belgium mai shekara 61 wanda a baya-bayan nan yake OH Leuven, an zaɓe shi domin maye gurbin tsohon ɗan wasan Liverpool kuma mai tsaron bayan West Ham, Rigobert Song.

    Sai dai hukumar da alama ba ta da masaniyar naɗin inda ta ce matakin an ɗauke shi ne ba tare da shawara ba.

    Hukumar ta ce ta yi niyyar ƙarin haske kan lamarin sannan ta yi bayani ba tare da ɓata lokaci ba kan matakin da za ta ɗauka.

    Tun 2021, tsohon ɗan wasan Barcelona kuma ɗan wasan gaba na Inter Milan da Chelsea Samuel Eto'o ne shugaban hukumar ƙwallon ƙafar.

    A yanzu hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka tana gudanar da bincike kan zargin aikata ba daidai ba.

  8. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon tallafin shinkafar azumi

    A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ƙaddamar da rabon shinkafar azumi ga mabuƙata.

    Buhu 120,000 ne gwamnatin ta saya daga Kamfanin sarrafa shinkafa na Tiamin Rice

    Za a ci gaba da rabon shinkafar mai nauyin kilo 25 daga yau Laraba a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

    Ga wasu hotuna daga bikin ƙaddamar da tallafin.

    ..
    ..
    ..
    ..
  9. 'Yan sandan Abuja sun shiga daji farautar masu garkuwa

    Rundunar ƴan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya sun ritsa wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a maɓoyarsu cikin dazuka da tsaunuka da ke kewayen Apo.

    Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

    Sanarwar ta bayyana cewa "jami'an rundunar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sanda CP Benneth Igweh sun kai samame cikin dazuka da ke kewayen shiyyar Zone A da B na unguwar Apo domin tabbatar da matakan tsaro a yankin saboda ana ganin wurin ya zama maɓoyar masu sace mutane.

    "Sumamen ya haɗa da ƙone gidajen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba da dazukan da ke kewayen tsaunuka da kuma tura ƴan sanda su yi rangadi a yankunan.

    A cewar sanarwar, Igweh ya umarci mutane su ci gaba da taka tsan-tsan sannan su kai rahoton duk abin da zuciyarsu ba ta yi na'am da shi ba ga ƴan sanda.

  10. Bostwana ta yi barazanar aika giwa 20,000 Jamus

  11. Kotu ta tabbatar da dokar haramta neman jinsi a Uganda

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Kotun tsarin mulki a Uganda ta tabbatar da dokar hana neman jinsi da ta janyo cece-kuce, wadda ta sanya hukuncin ɗaurin rai da rai da na kisa ga waɗanda aka samu da neman jinsi.

    "Mun ƙi mu soke dokar haramta neman jinsi ta 2023 gaba ɗayan ta, kuma ba za mu yi wani hukunci na dindindin ba game da aiwatar da dokar," in ji alƙali Richard Buteera a zaman kotun na ranar Laraba.

    Waɗanda suka shigar da ƙorafi sun ce za su ɗaukaka ƙara.

    Malamai a Uganda da masu fafutukar kare haƙƙin bil adama da lauyoyi da ƴan jarida da ƴan majalisa da malaman addini ne suka shigar da ƙarar ta neman a soke dokar.

    Sun bayyana cewa dokar ta ci zarafin ƴancin da kundin tsarin mulki ya bayar da dama.

    Sun ƙara da cewa dokar ta ci karo da alƙawuran ƙasar a ƙarƙashin dokokin kare haƙƙin bil adama.

    Duk da nuna damuwar, dokar ta samu karɓuwa sosai a ƙasar.

    Ƴan majalisa sun zargi ƴan hamayya na ƙasashen yamma da ƙoƙarin matsa wa Afirka lamba ta karɓi halayyar neman jinsi.

    • An tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk mutumin da ya ce mai neman jinsi ne a Uganda
    • Hukuncin kisa ga masu auren jinsi a Uganda
  12. Gwamnati ta ƙara kuɗin lantarki a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta amince da ƙara kuɗin wuta ga abokanan hulɗarsu da ke ajin Band A - masu samun wuta tsawon sa'a 20 a rana.

    Mataimakin shugaban hukumar, Musuliu Oseni ya bayyana cewa a yanzu kwastamomin za su biya N225 kan kowane kilowatt inda a baya suke biyan N66.

    A taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, Oseni ya ce abokan hulɗarsa da ke samun wuta tsawon sa'a 20 a rana sune kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar a Najeriya.

    Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma sauke kwastamomin da ke ajin Band A zuwa Band B masu samun wuta ƙasa da sa'a 20 a rana saboda rashin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki na basu wutar da ta kamata.

    Ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi kwastamomin da ke sauran matakan ba.

    Tun bayan samun bayanai cewa hukumomi na iya ƙara kuɗin wuta ne, al'ummar Najeriya ke ta martani a shafukan sada zumunta inda wasu ke ganin matakin ya zo a lokacin da jama'a ke fama da tsadar rayuwa da kuma rashin tsayayyiyar wutar lantarki da ake fuskanta.

  13. Yadda ƴan agaji ke neman waɗanda suka maƙale a girgizar ƙasr Taiwan

    Kamar yadda muke ta baku ƙarin bayani game da girgizar ƙasa mafi girma a Taiwan, aƙalla mutum tara aka bayar da rahoton sun mutu sannan fiye da wasu 800 suka ji rauni a ibtila'in da ya faru da yankin.

    Masu agaji a sassan Taiwan na ƙoƙarin zaƙulo mutanen da ƙasa ta rufe a gine-gine da kuma hanyoyin ƙarƙashin ƙasa.

    Ga wasu hotuna da muka samu daga wuraren da ƴan agaji ke aikin neman mutanen da ibtila'in ya rutsa da su.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ma'aikatan hukumar kashe gobara ta Kaohsiung na duba wani gini bayan da girgizar ƙasar mai ƙarfin gaske ta afku a yankin gabashin tekun Taiwan
    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka maƙale sakamakon faɗowar ɓuraguzon gine-gine
    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Da safiyar Laraba ne girgizar ƙasa mafi ƙarfi cikin shekara 25 ta afku a yankin Taiwan inda ta lalata gine-gine da dama.
  14. An kama Luis Rubiales a wani binciken cin hanci

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama Luis Rubiales, tsohon shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya a wani ɓangare na binciken rashawa da ake masa.

    An tsare shi da isar sa Madrid daga Dominican Republic.

    Ana zargin shi da karɓar toshiya lokacin tattauna wata gwaggwaɓar kwangila ta shirya gasar Spanish Super Cup a Saudiyya.

    Masu gabatar da ƙara na neman a kulle shi tsawon shekara biyu da rabi. Mista Rubiales dai ya musanta zarge-zargen da ake masa.

    Bayan ya sauka daga jirgi, an kai shi cikin wata baƙar mota tare da jami'an tsaro.

    Ƴan sanda a yanzu suna da sa'a 72 su yi wa mista Rubiales tambayoyi, wanda ya je Dominican Republic da ƴan sanda suka gudanar da bincike a gidansa a watan da ya gabata.

    Sun kuma yi bincike a hedikwatar hukumar ƙwallon ƙafar tare da kama mutane da dama.\

    Lamarin ya zo yayin da Mista Rubiales ke shirin fuskantar shari'a kan zargin cin zarafi mai nasaba da lalata bayan da ya sumbaci wata ƴar wasa Jenni Hermoso a baki bayan wasan ƙarshe na kofin duniya.

    Ms Hermoso da ƴan tawagar ƙungiyar sun ce sumbatarta da ya yi ƙasƙantarwa ne.

    An tilasta wa Rubiales ajiye aiki amma ya musanta aikata ba daidai ba.

    • Wani alƙali ya nemi Luis Rebiales ya bayyana gaban kotu
    • Shugabannin ƙwallon kafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus
  15. Ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi wa gine-gine a Taiwan cikin hotuna

    Girgizar ƙasar ta yi mummunar ɓarna inda ta lalata gine-gine a sassan Hualien da ke gabashin gaɓar tekun Taiwan.

    Ga wasu hotuna na irin ɓarnar da girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.4 ta yi.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Zaftarewar ƙasa ta tunkari wata gada kusa da Xiulin a Taiwan sakamakon girgizar ƙasa
    ..

    Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

    Bayanan hoto, Wata mota kan wani titi da ya rufta a birnin New Taipei
    ..

    Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

    Bayanan hoto, Girgizar ƙasar ta lalata manyan gine-gine kamar tashar jirgin ƙasa ta Taipei
    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ɓuraguzai na zubowa ƙasan wani gini a birnin New Taipei
  16. An sa dokar ta ɓaci a Zimbabwe saboda matsanancin fari

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Zimbabwe sun saka dokar ta ɓaci a ƙasar sakamakon matsalar fari da ta jefa mutum miliyan uku cikin yunwa.

    Shugaba Emmerson Mnangagwa ya ce ƙasar na buƙatar tallafin dala biliyan 2 domin magance tasirin farin na matsalar abinci.

    Rashin saukar damina ya shafi yankuna da dama a kudancin Afirka inda hukumar samar da abinci ta duniya ta ce mutum miliyan 20 ne ke fama da rashin abinci.

    Zimbabwe ce yanzu ƙasa ta uku a kudancin Afirka da ta ayyana dokar ta ɓaci cikin wata ɗaya.

    A Zambiya da Malawi, waɗanda suma suka ayyana dokar ta ɓaci, an samu lalacewar amfanin gona da dama musamman masara sakamakon rashin ruwan sama.

    A yanzu dai Zimbabwe ta shiga neman masara a kasuwar duniya kuma hukumomi sun ce adadin mutanen da za su buƙaci agajin abinci zai ƙaru fiye da mutum miliyan 2.7 da aka yi hasashe.

  17. Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku

  18. Mozambique ta haramta shigar da na'uin karnukan da ke da haɗari ga ƙasarta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin noma a Mozambique ta haramta shigar da na'uin karnukan da ake gani na da haɗari.

    Matakin yunƙuri ne na magance yawan cizon kare da aka bayar da rahoton faruwar su a faɗin ƙasar da ke kudancin Afirka.

    Cizon kare abu ne da aka saba gani a Mozambique. A farkon shekarar da ta gabata, kusan mutum 9,000 aka ruwaito kare ya ciza, ragin kashi 21 cikin 100 daga shekarar 2022.

    Wasu daga cikin mutanen sun samu munanan raunuka da ta kai ga yanke sassan jiki ko ma mutuwa.

    Haramcin ya shafi nau'ikan kare 26 kuma matakin bai shafi karnukan da hukumomi ke amfani da su don tsaro ba da waɗanda kamfanonin samar da tsaro masu zaman kansu ke amfani da su da karnukan da ake amfani da su lokacin wani bala'i da waɗanda suke taimakawa wajen bayar da agaji.

    Suma karnukan da suka samu horon kula da mutanen da ba sa gani ba sa cikin nau'in karnukan da aka haramta.

    Ma'aikatar kuma ta ce nau'in karnukan da aka haramta kuma tuni suna cikin ƙasar, dole ne a yi masu rajista da hukumomi cikin wata biyu.

  19. Fiye da mutum 120 sun maƙale cikin ɓuraguzai bayan girgizar ƙasar Taiwan

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Taiwan sun tabbatar da maƙalewar mutum 127 cikin ɓuraguzan gini sakamakon girgizar ƙasar da ta faru.

    Cikin adadin, 77 a cikinsu sun maƙale a cikin wata hanya da ke ƙarƙashin tsauni a Jinwen da Daqinqshui a Hualien, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

    Sannan mutane biyu Jamusawa ne da suka maƙale a hanyar ƙarƙashin ƙasa a Chongde da ke gandun daji na yankin.

    Sauran mutum mutum 50 kuma sun maƙale a ƙananan motocin bas huɗu da suke hanyar zuwa gandun dajin Taroko daha birnin Hualien.

    Dukkansu ma'aikata ne da za a kai otal ɗin SilksPlace Taroko gabanin hutun yini huɗu daga Alhamis zuwa Lahadi.

  20. Kotu ta ba da umarni a saki dangin Bazoum nan take

    Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta yanke hukunci a kan ƙarar lauyoyin dangin hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, waɗanda aka kama, kuma ake tsare da su.

    Ana zarginsu ne da hannu a yunƙurin Bazoum na tserewa daga inda shugaban mulkin sojin ƙasar, Abdourahamane Tchiani ke tsare da shi.

    Kotun ta ce kama mutanen da tsare su, ba sa kan ƙa'ida, don haka ta umurci hukumomin mulkin sojin Nijar, su saki mutanen nan take.

    Ta kuma ce gwamnatin Nijar za ta biya tarar CFA miliyan ɗaya ga duk wuni ɗaya da za su sake yi a hannun hukuma.

    Sojojin fadar shugaban ƙasa ne suka kama mutanen a wani samame da suka kai wani gida cikin birnin Yamai ranar da aka zargi Bazoum da yunƙurin tserewa zuwa Najeriya.