Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye a wannan rana ta Litinin.
Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye a wannan rana ta Litinin.
Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
A yau cikin shirin Girke-girken Ramadan 2024, Hajara Muhammad da aka fi sani da Chef Hajjo ta koya mana yadda ake yin shinkafar ƴan China da miyar 'sweet and sour'.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters
Wani harin da Isra'ila ta kai ya lalata ginin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin ƙasar Syria, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma raunata mutane da dama, a cewar hukumomin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an kashe jami'an diflomasiyya da dama a harin da aka kai a yammacin birnin.
Wani babban kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran Mohammad Reza Zahedi na cikin waɗanda suka mutu a cewar kafar yaɗa labaran ƙasar.
Bayan harin, rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta ce uffan ba kan rahotannin kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje.

Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciyo rancen kuɗi naira biliyan 14.26 ba, sai dai kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo na naira biliyan 20.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce gwamnati ba ta ci wani bashi a gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.
"Muna so mu fayyace rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.
"Gwamnatin jihar Zamfara ba ta taɓa neman buƙatar karɓar rance ba ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce ya kamata jama'a su gane cewa gwamnatin baya ce a jihar ta ciyo bashin kuɗin na naira biliyan 20, amma ta ƙasa karɓar kuɗaɗen duka.
“Gwamnatin da ta gabata ta karbi naira biliyan 4 daga cikin rancen biliyan 20 da aka nema domin aikin filin jirgin sama na Zamfara, duk da cewa ba a yi amfani da kuɗaɗen ba.
“Bayan da muka shigo ofis, mun gano cewa sharuɗan biyan kuɗin ya sa kawo karshen yarjejeniyar ba zai yiwu ba ba tare da ya jawo babbar asara ga jiha ba," in ji sanarwar.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴan sanda jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Isyaku Babale, bisa zargin kashe daɓa wa yayansa wuka har lahira.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ta ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuka wajen daɓa wa babban wansa mai suna Abubakar Balewa ranar Lahai, 31 ga watan Maris bayan cacar-baki da ta ɓarke tsakaninsu.
Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da ya faru ne, sai suka tura jami’ansu zuwa wurin, abin da ya kuma ya kai ga kama matashin mai shekara 30 wanda ke zaune a Anguwan Dawaki.
Ya ce bayan garzayawa da mutumin asibiti ne likita ya tabbatar da cewa ya mutu.
Binciken da aka gudanar ya ƙara nuna cewa ƴan uwan junan sun saba yin faɗa da juna ta hanyar amfani da muggan makamai, sai dai, a wannan karo, har ta kai ga rasa ran ɗaya daga cikinsu.
"Cacar-baki tsakanin ƴan uwan ta ɓarke ne bayan da wanda ake zargin ya faɗa wa ɗan uwansa da ya kashe da ya daina shan ‘Sholi’ a ɗakinsu saboda warinsa, wannan abin ne ya janyo faɗa tsakaninsu.
"Jim kaɗan bayan an shiga tsakaninsu ne, wanda ake zargin ya ruga ya ɗauko wani abu da ake kyautata zaton wuƙa sannan ya daɓa wa yayan nasa a ciki,” in ji Wakili.
Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, suka shiga farautar wanda ake zargin inda har ta kai ga kama shi a Kasuwan Shanu na jihar ta Bauchi.
Wakili ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin yin cikakken bincike kan lamarin.

Asalin hoton, EPA
Masu aikin ceto masu hakar ma’adinai 13 da suka maƙale bayan zaftarewar ƙasa a gabashin Rasha sun kawo karshen aikinsu, tare kuma da ɗaukar cewa mutanen sun mutu, a cewar kafofin yaɗa labaran Rasha.
An ƙasa ci gaba da aikin ceto a yankin Amur saboda fargabar ci gab da zaftrewar ƙasa.
Lamarin ya faru ne makonni biyu da suka wuce, inda masu hakar ma’adinai suka makale mitoci sama da 100 cikin ƙasa. An kuma fuskanci ambaliyar ruwa a yankuna da dama.
Wurin ya kasance ɗaya daga cikin wuraren hakar ma’adinai mafi girma a duniya da kuma ƙasar Rasha.
Jami’ai sun ce na’urorin ɗaukar hoto da aka saka karkashin ƙasa a wurin hakar ma’adinan sun nuna duka wuraren da ya kamata mutanen su samu mafaka cike da ruwa da laka da kuma kankara.
“Rayuwar masu aikin ceto da kuma ta masu hakar ma’adinan na cikin haɗari,” a cewar wata sanarwa da aka fitar.
Ana yawan samun zaftarewar ƙasa a wuraren hakar ma’adinai a Rasha, kuma so da yawa ana ɗora laifi kan rashin ɗaukar matakai a wuraren da kuma cin hanci.
A 2019, masu hakar ma’adinai sama da 15 ne suka mutu sannan da dama suka jikkata lokacin da wata madatsar ruwa kusa da wurin haƙa ta ɓalle a yankin Krasnoyarsk na ƙasar ta Rasha.

Asalin hoton, Kebbi State Government/X
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi Alla-wadai da halin wasu ɓata-gari masu wawar abinci a Birnin Kebbi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamnan kan fannin yaɗa labarai, Ibrahim Adamu Argugun ya fitar, bayan wani taro da mataimakin gwamnan jihar Sanat Umar Abubakar Tafida ya yi da wasu kwamishinoni da masu ba da shawara da kuma shugabannin hukumomin tsaro ranar Lahadi.
Shugabannin hukumomin tsaron sun yi wa mataimakin gwamnan bayani kan abin da ya janyo wawason kayan abincin, musamman ma wasu yankuna a birnin Kebbi.
Sanarwra ta ce jami’an tsaro na ɗaukar matakai domin shawo kan lamarin.
Gwamnatin jihar ta ce tana kira ga dukkan ƴan jihar masu bin doka da oda da kada su bari ɓata-garin su yi amfani da wannan damar wajen biyan buƙatu na kashin kansu.
Ƴan bidiga sun sanya wa wasu garuruwa bakwai da ke yankin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara biyan tarar kusan naira miliyan 30 ko su halaka mutanen yankin da suka yi garkuwa da su ciki har da mata.
Wani mazaunin yankin ya ce lamarin ya jefa fargaba a zukatan da dama daga cikin mazauna yankin wanda hakan ya sa suka fara tsallakawa zuwa yankunan jihar Kebbi.
Sai dai rudunar ƴan sandan jihar ta Zamfara ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.
Ga Khaliofa Shehu Dokaji da ƙarin bayani.
Ƴan sandan Isra'ila sun kama ƴar uwar jagoran siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh.
Wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar, ta ce an kama matar mai shekara 57 ne da zargin cewa tana da alaƙa da wata ƙungiyar mayaka.
Tana zaune ne a birnin Tel Sheva da ke kudancin Isra'ila.
An sa ran matar za ta gurfana gaban kotu ranar Litinin.
Jagoran siyasar na Hamas Mr Haniyeh, na zaune ne a wane waje a ƙasar Qatar.

Asalin hoton, EFCC/Facebook
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ya tabbatar da cewa ba za su bar manyan ɓarayi ba a yaƙin da suke yi da masu alaƙa da cin hanci da rashawa a ƙasar.
Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan ɓarayi, za kuma su ci gaba da bin sawun ƙananan ɓarayi.
Ya ce aikin da EFCC take yi zai ci gaba da karaɗe ko'ina, da kuma kan kowa da kowa ba tare da wani da ke alaƙa da duk wani nau'in laifin kuɗi ko na tattalin arziƙi ya kuɓuta ba.
Shugaban na EFCC ya ba da wannan tabbaci ne ranar Lahadi lokacin da hukumarsa ta shirya wani taron wayar da kai da kuma yunƙurin shigar da jama'a cikin harkokin yaƙi da cin hanci da rashawa.
A cewarsa, a cikin wata biyun da ya wuce, hukumarsa ta EFCC ta gurfanar da tsoffin gwamnoni guda biyu gaban shari'a.
Ana dai sukar hukumar ta EFCC da cewa ta zama kyanwar lami, ba ta iya bin manyan 'yan siyasa da sauran manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati waɗanda ake zargi da tafka gagarumar sata da kuma almundahana da dukiyar al'umma.
Sai dai, Mista Ola Olukoyede ya ce ba gaskiya ba ne a ce EFCC ta fi kauri wajen kama masu damfarar intanet.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kai ziyara ƙasar Senegal don halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaba Bassirou Diomaye Faye.
Tinubu zai bar Abuja ne a ranar da za a yi bikin rantsuwar wato Talata, bayan ya samu gayyata a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya, ta ce Tinubu zai koma gida ne a dai wannan rana da zarar an kammala bikin na birnin Dakar.

Asalin hoton, Getty Images
Wani hamshaƙin ɗan gargajiya mai shekara 63 ya fusata jama'a a Ghana bayan ya auri wata yarinya 'yar shekara 12.
Bokan Nuumo Borketey Laweh Tsuru XXXIII, ya yi auren ne a wani bikin al'ada da aka yi ranar Asabar.
Sakamakon caccaka ne kuma, shugabannin al'umma suka fito suna cewa mutane ba su fahimci al'adun gargajiyarsu ba.
Mafi ƙarancin shekarun aure bisa doron doka a Ghana shi ne 18 kuma an samu raguwar yawan auren wuri a ƙasar, amma lamarin na ci gaba da faruwa nan da can.
A cewar wata ƙungiya Girls Not Brides, mai rajin kawar da auren wuri, kashi 19% na 'yan matan ƙasar ne aka yi musu aure kafin su kai shekara 18.
Bidiyo da hotunan gagarumin shagalin bikin na ranar Asabar wanda gomman jama'ar yankin suka halarta, sun karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya harzuƙa da yawan al'ummar Ghana.
A lokacin bikin, matan da suka yi jawabi a harshen Ga sun faɗa wa yarinyar ta riƙa yin shiga don hilatar mijinta.
Ana kuma iya jin su lokacin da suke ba ta shawarar ta shirya wa shiga rayuwa irinta matar aure kuma ta yi amfani da turarurrukan da suka ba ta kyauta wajen tayar wa mijinta sha'awa.
Irin waɗannan kalamai ne suka harzuƙa mutane, don kuwa ana ganin hakan na nuna cewa aure ne na haƙiƙa ba kawai na bidiri ba.
Masu sukar lamarin sun yi ta kira ga hukumomi su rusa auren sannan su gudanar da bincike a kan Mista Tsuru.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun da ta tura don aikin murƙushe ‘yan ta-da-ƙayar-baya a jihohin Katsina da Zamfara sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 11 a cikin kwana biyu.
Sun dai kai samame ne maɓoyar waɗanda suka kira ‘yan ta’adda, inda suka kashe wani adadi na ‘yan bindigar a ranar 29 ga watan Maris.
Ta ce dakarun soji sun yi nasarar kai wa mafakar wani riƙaƙƙen ɗan fashin daji mai suna Hassan ‘Yan tagwaye hari, a cikin ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka kashe uku a cikinsu tare da ƙwato makamai.
Rundunar sojin ta kuma ce dakarunta sun ragargaza sansanonin ɗan fashin, wanda ta ce yana da hannu wajen satar mutane da ayyukan ta’addanci a wasu yankuna na arewa maso yamma.
A jihar Katsina kuma, cewar rundunar sojin ƙasan Najeriya, dakarunta sun gwabza faɗa a ranar 30 ga watan Maris da waɗanda suka kira ‘yan ta’adda a Shawu Kuka da Shinda da Tafki da Gidan Surajo da Citakushi da Kabai I da Kabai II duka a cikin ƙaramar hukumar Faskari.
Ta ce dakarun sun yi nasarar kashe ‘’yan ta’adda’ takwas tare da gano bindigogi ƙirar gida guda uku da kakin sojoji da kuma ɗumbin hatsin sata.

Asalin hoton, Other/Facebook
Babban limamin Cocin Katolika ta Sakkwato Matthew Hassan Kukah ya soki lamirin tsarin da ake bi wajen raba tallafin rage raɗaɗi ga 'yan Najeriya, ana tsakiyar fama da mawuyacin tsananin rayuwa a ƙasar.
Gwamnatoci a dukkan matakai sun ɓullo da hanyoyin bayar da tallafin rage raɗaɗi, bayan cire tallafin man fetur.
Sai dai, da yake jawabi game da batun tsarin raba tallafin rage raɗaɗi, Bishop Kukah ya ce akasarin mutane ba sa samu. Ya nunar cewa a lokuta masu yawa kaso mai yawa na irin wannan kuɗi, sace su ake yi.
Malamin addinin Kiristan na wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels.
Ya ce: “Muna buƙatar mu ga wani ƙwaƙƙwaran shiri da gwamnati za ta ɓullo da shi, wanda zai taimaka wajen raba mu da irin wannan bin layi muna karɓar tallafi duk da ba a yaƙi muke yi ba.
“Ina jin tsagwaron zubar da mutunci ne a ga 'yan Najeriya suna bin layi kullum a cikin rana, suna jiran su karɓi buhun shinkafa, wadda mai yiwuwa ba za ta samu ba, ba kuma don ba a bayar da kuɗin ba, amma sai don sanin cewa duk wanda ya ba da kuɗi a Najeriya daga gwamnatin tarayya yana da masaniyar cewa, wani ƙwaƙƙwaran kaso na kuɗin, a ko da yaushe sacewa ake yi.”

Asalin hoton, Reuters
Kwanaki ƙalilan bayan kamfanin Xiaomi mai ƙera wayoyin zamani a ƙasar China ya ƙaddamar da motar lantarkinsa ta farko, an faɗa wa masu sha'awar sayen motar cewa sai sun ƙara jira tsawon wata shida kafin a iya kai musu motar.
Bidiyo da hotunan tallace-tallacen motar a shafukan sada zumunta na China sun nuna kamfanin yana shaida wa masu sayen motar cewa za a iya ɗaukar tsawon mako 27 kafin motar ƙirar SU7 Max ta isa gare su.
Kamfanin a baya ya ce mutanen da suka yi oda a cikin kwana ɗaya kacal sun kai 88,898. Sai dai cikin hanzari Xiaomi bai amsa roƙon BBC na neman ji daga gare shi ba.
Katafaren kamfanin ƙere-ƙere, wanda shi ne na uku mafi girma wajen sayar da wayoyin salula na zamani a duniya, yana goga kafaɗa da takarorinsa masu ƙera motocin lantarki kamar Tesla da BYD.
Farashin matsakaiciyar motar SU7 ya kai dala 29,872 kwatankwacin naira miliyan 40.

Asalin hoton, Other/Facebook
Wasu mazaunan jihar Kebbi sun auka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnati a unguwar Bayan Kara cikin Birnin Kebbi, inda suka wawashe buhunhunan kayan abincin da ke ciki.
Mutanen waɗanda suka bijire wa jami'an tsaron da aka jibge a gidan ajiyar, sun kuma fasa wasu gidajen ajiyar kaya na 'yan kasuwa da shagunan da ke yankin inda suka saci kayan abinci.
Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa zauna-gari-banzan sun kuma far wa wata babbar mota da aka laftawa kayan abinci dangin hatsi waɗanda aka yi niyyar rabawa a Birnin Kebbi.
Ta ce wawar kayan abinci a gidajen ajiyar kaya irin na Birnin Kebbi, ta faru a Abuja da garin Suleja a cikin jihar Neja.
Hakan na faruwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa wanda galibi aka yi imani ya faru ne sanadin cire tallafin man fetur da barin naira ta ƙwaci kanta a kasuwar canji.
Ta dai ambato Muhammadu Gwadangwaji, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar hatsi da ke Bayan Kara a Birnin Kebbi, wasu matasa sun ma cinna wuta kan shaguna da gidajen ajiyar kayan 'yan kasuwa a lokacin wawason.
“(Jami'an tsaro) sun harba harsasai da hayaƙi mai sa hawaye sama, amma su (matasan) ba su razana ba. Sun kutsa kai suka shiga ciki, sannan suka washe gidan ajiyar kayan gwamnati da wasu shagunanmu na 'yan kasuwa”.
Da yake mayar da martani, Ahmed Idris, wanda shi ne babban sakataren yaɗa labarai ga Gwamna Nasir Idris, cewa ya yi lamarin “abin takaici ne”.

Asalin hoton, Getty Images
Zuzzurfan rarrabuwar kan siyasar Isra'ila ta sake dawowa sabuwa fil a kan idon jama'a.
Tsawon wani ɗan lokaci, an jingine su wuri ɗaya, yayin da kaɗuwa da rajin haɗin kan ƙasa suka biyo bayan hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba na mayakan Hamas - sai dai wata shida bayan nan, dubun dubatar masu zanga-zanga sun sake fantsama a kan titunan Isra'ila.
Yaƙin da ƙasar ke yi, ya sake yi musu ƙaimi a ƙudurinsu na kawo ƙarshen mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu, mafi dogon zamani.
A Ƙudus, 'yan sanda sun yi amfani da ruwan ɗoyi wajen fesa wa masu zanaga-zangar da rufe babban titin arewa zuwa kudu.
Wasu a cikinsu na ta rera taken Netanyahu ya sauka daga mulki sannan a gudanar da zaɓen wuri, yayin da wasu ke nanata kiran a gaggauta sako 'yan Isra'ila kimanin 130 da ake garkuwa da su a Gaza. Ana dai jin cewa akwai wani adadi daga cikinsu da ya rasu.
Babbar fargabar masu zanga-zangar ko danginsu da abokan arziƙi, ita ce ƙarin waɗanda ake garkuwar da su, za su yi ta mutu idan aka ci gaba da gwabza yaƙin ba tare da an bi matakin sulhuntawa ba.
Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta janye daga asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza bayan wani samame na tsawon mako biyu, wanda ya yi raga-raga da galibin gine-ginen asibitin.
A cewar rundunar tsaron sojin Isra'ila, dakarun ƙasar sun "hallaka 'yan ta'adda" kuma sun gano "ɗumbin makamai da bayanan ayyukan sirri" a yankin.
Samamen ya faru ne bayan Isra'ila ta ce ta samu bayanan sirrin da ke nuna cewa Hamas na amfani da asibitin a matsayin wani sansanin ƙaddamar da hare-hare.
Hamas dai ta musanta amfani da cibiyoyin lafiya don gudanar da ayyukan sojoji.
A cikin 'yan makonnin nan, an ba da rahoton ɓarkewar ƙazamin faɗa a zagayen asibitin, wanda shi ne mafi girma a Gaza.

Asalin hoton, REUTERS/Umit Bektas
Babbar jam'iyyar adawa ta Turkiyya ta yi iƙirarin samun manyan nasarori a zaɓen da aka yi cikin manyan biranen ƙasar na Istanbul da Ankara.
Sakamakon wata babbar mahangurɓa ce ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda ya yi fatan sake karɓe iko da biranen ƙasa da shekara ɗaya bayan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a wa'adi na uku.
Ya dai jagoranci yaƙin neman zaɓe a birnin Istanbul, inda ya girma har ya zama magajin gari.
Sai dai Ekrem Imamoglu, wanda ya yi nasarar cin zaɓen magajin birnin karon farko a 2019, ya samu nasara a karo na biyu da jam'iyyarsa ta adawa wadda babu ruwanta da wani tsarin addini ta CHP.
Shugaba Erdogan dai ya yi alƙawarin buɗe sabon shafi a ƙasaitaccen birnin mai yawan jama'a kusan miliyan 16, sai dai magajin birnin Istanbul mai ci yana gab da samun fiye da kashi 50% na ƙuri'un da aka kaɗa, inda zai kayar da ɗan takarar jam'iyyar AP ta shugaba Erdogan da maki fiye da 11 da kuma ƙuri'u kusan miliyan ɗaya.