'Yan sanda sun daƙile yunƙurin 'yan bindiga na tare hanyar Gusau zuwa Sokoto

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yansan jihar Zamfara ta ce ta daƙile yunƙurin 'yan bindiga na tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto a daidai ƙauyen Kwaren Ƙirya da ke yankin ƙaramar hukumar Maru.
Cikin wata sanarwar da kakakin 'yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya fitar ya ce hankula sun kwanta bayan yunƙuri 'yan bindigar na ranar Talata.
Sanarwar ta yi watsi da jita-jitar da ake ta yaɗawa cewa a ranar Talata mahara sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto, tare da sace mutum 26.
Rundunar 'yan sandan ta ce a ranar talata da safe ne jami'anta sun samu rahoton cewa mahara sun tare babbar hanyar, inda nan take rundunar ta tattara jami'anta da ke yaƙi da ayyukan masu garkuwa da mutane tare da haɗin gwiwar 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa wajen inda suka yi bata-kashi da maharan, inda maharan suka ranta a na kare tare da raunukan harbin bindiga..
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa labarin da ake yaɗawa cewa maharan sun sace matafiya 26 daga wasu motoci biyu a wurin, ba gaskiya ba ne.
Rundunar ta ce tana ɗaukar matakan da suka dace don hana aukuwar makamancin wannan ala'amari.
Jihar zamfara dai na daga cikin jihohin arewain Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da ke tare hanyoyin mota tare da sace fasinjoji domin neman kuɗin fansa.



















