Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Habiba Adamu and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.

    Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. MDD ta ce har yanzu Taliban na hana mata zuwa makaranta

    Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghanistan ta ce shugabannin Taliban suna ci gaba da hana matan ƙasar aiki, da zuwa makaranta, da kuma kula da lafiya.

    A sabon rahoton da ta fitar kan Afghanistan, Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce Taliban ta umarci direbobin motar Bas a birnin Kandahar, da su daina ɗaukar mata ba tare da muharramansu maza ba.

    Haka nan kuma, an bayar da rahoton cewa an kulle wasu mata ma'aikatan lafiya uku saboda zuwa aiki ba tare da muharrami ba.

    Tuni dai kakakin Taliban ya musanta zargin, yana cewa an gina rahoton ne a bisa rashin fahimta.

  3. Amurka ta ƙaƙaba wa kamfanin jirgin saman Iraqi takunkumi kan zargin tallafawa ta'addanci

    Amurka ta ƙaƙaba wa kamfanin jirgin saman Iraqi takunkumi, bisa zargin cewa yana tallafawa ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Iran.

    Ma'aikatar kuɗin Amurka ta zargi kamfanin Fly Baghdad da safarar makamai zuwa filin jirgin-saman Damascus, inda ƙungiyoyin mayaƙa ke ayyukan su.

    Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka a Iraqi, tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Hamas.

    Fly Baghdad ya yi watsi da wannan takunkumi, yana mai cewa ba shi da wani nauyin yin bayani kan batun.

  4. Gwamnatin Taraba ta haramta hawa babura, ta takaita zirga-zirgar Keke Napep a Jalingo

    Babura

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Taraba ta haramta amfani da babura kowane iri a Jalingo, babban birnin jihar

    Haka-zalika, gwamatin ta kuma takaita zirga-zirgar Keke Napep daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 8:00 na yamma.

    Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwar ayyukan ta'addanci a kwaryar birnin Jalingo.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin kwamishina ƴan sandan jihar domin ganin haramcin ya yi aiki yadda ake so.

    Gwamnatin ta ɗau alwashin kama wa da kuma hukunta waɗanda suka bijire wa haramcin hawa baburan, inda ta ce za a kwace babura da Keke Napep ɗin da suka saɓa dokar sannan a lalata su.

  5. Super Eagles ta doke Guinea-Bissau, ta kai zagaye na biyu a gasar Afcon

    Super Eagles

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan cin Guinea-Bisau 1-0 ranar Litinin.

    Wasa na uku-uku a cikin rukunin farko da aka buga kenan, inda a lokacin Equatorial Guinea ta caskara Ivory Coast 4-0.

    Najeriya ta zura kwallo ne a minti na 36, bayan da Guinea ta ci gida ta hannun Opa Sangante.

    Super Eagles ta ci kwallo biyu ana sokewa, ita ma Guinea-Bissau ta zura kwallo a ragar Nageriya, amma ba a karɓa ba.

    Da wannan sakamakon Super Eagles ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da maki bakwai, yayin da Equatorial Guinea ce ta yi ta ɗaya da maki bakwai iri ɗaya da na Najeriya.

    Ivory Coast ta sha kashi a hannun Equatorial Guinea da ci 4-0 a ɗaya karawar rukunin farko.

    Kai tsaye Equatorial Guinea ce ta ja ragamar rukunin farko da maki bakwai sai Najeriya ta biyu ita ma mai maki bakwai.

    Tun a baya Equatorial Guinea ta ƙasa haura wasannin rukuni a gasar cin kofin Afirka biyu, amma ta ja ragamar rukunin farko a Ivory Coast.

  6. An kashe gomman mutane yayin da faɗa ke ci gaba da kazanta a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, ANADOLU

    An ruwato kashe gomman mutane sakamakon hare-hare babu kakkautawa a birni Khan Younis da ke kudancin Gaza, yayin da faɗa ke ci gaba da kazanta tsakanin sojoji da mayakan Hamas.

    Mazauna birnin sun ce tankokin yaƙi sun mamaye wani asibiti da kuma jami'a, wajen da dubban mutane ke zaman hijira.

    Motocin ɗaukar marasa lafiya sun ƙasa kai wa ga waɗanda suka jikkata.

    Sojojin Isra'ila sun mayar da hankali kan birnin Khan Younis a baya-bayan nan, inda suka ce manyan kwamandojin Hamas na zaune a wurin.

    A ranar Lahadi, sojojin Isra'ila suka ce sun gano wani gida a karkashin ƙasa a Khan Younis, inda ta yi imanin cewa ana riƙe da ƴan ƙasar kusan 20 da aka yi garkuwa da su.

  7. 'Mun cimma yarjejeniya da matatar man Dangote don ta ba mu tataccen man fetur'

    Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta ce ta cimma yarjejeniya da matatar man fetur ta Dangote da ta fara aiki a baya-bayan nan domin bai wa 'ya'yanta tataccen man fetur.

    IPMAN ta ce tana sa ran samun man zai taimaka wajen rage wahalarsa da ake samu a wasu sassan ƙasar, da kuma samun saukin farashi.

    Shugaban ƙungiyar dillan man fetur ɗin ta ƙasa, Alhaji Abubakar Maigandi Shatima, shi ya bayyana yayin tattauna da BBC.

    Ku latsa ƙasa don sauraron tattaunawar da Imam Saleh ya yi da shi.

    Bayanan sautilatsa sama don sauraron tattaunawar
  8. Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi kan kamfanonin da ke aiki da Sudan

    Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni shida da ke aiki da Sudan, ciki har da kwace kadarori saboda zarginsu da tallafawa ɓangarorin da ke faɗa da juna a ƙasar da makamai da kuma kuɗi.

    Cikin kamfanoni da aka sanya wa takunkumi sun haɗa da guda biyu waɗanda ake zargi da ƙera makamai da ababen hawa ga sojojin Sudan, da kuma guda uku da ke da hannu a samar wa dakarun RSF makamai.

    An zargi dukkan ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi, wanda ya ɓarke a watan Afrilun bara.

    Rikicin ya janyo mutuwar dubban mutane da ɗaiɗaita miliyoyi.

    A cikin wata sanarwa, EU ta ce tana cikin damuwa matuka kan batun yanayin jin-ƙai a Sudan, inda ta ƙara nanata goyon bayanta ga al'ummar Sudan.

    Duk wani yunkuri na diflomasiyya na ganin an shawo kan rikicin ya citura kawo yanzu.

  9. 'Ya kamata gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi aiki da buƙatun al'umma'

    Haɗin gwiwar ƙungiyoyin farar hula na masu kishin ƙasa a Jamhuriyar Nijar sun buƙaci gwamnatin mulkin sojin ƙasar da ta yi aiki da buƙatun al'umma yayin zaman tattaunawa da za su yi da Ecowas a ranar 25 ga watan Janairu.

    Ƙungiyoyin sun bayyana haka ne cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka kuma kira wani zaman dirshen a wasu wurare daban-daban na babban birnin Yamai.

    Ku latsa ƙasa don sauraron rahoton Tchima Illa Issoufou

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
  10. 'Mu muka karɓo yaranmu daga hannun masu garkuwa da mutane, ba ƴansanda ba'

  11. Ambaliya ta ɗaiɗaita birnin Dar es Salaam

    Ambaliya

    Asalin hoton, MILLARD AYO

    Gidaje da dama sun rufta sannan hanyoyi da gadoji kuma sun lalace bayan mamakon ruwan sama na tsawon kwanaki biyu da ya ɗaiɗaita birnin Dar es Salaam na ƙasar Tanzaniya.

    Ruwan ya tafi da wata mata, yayin da ake neman wani yaro guda, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Ambaliyar ta fi lalata gidajen da aka gina kusa da koguna da suka dangana da tekun Indiya.

    Hanyoyi da dama sun cunkushe har ta kai ba a iya wucewa, inda hakan ya tilastawa ɗalibai da masu aiki zama a gida a yau Litinin.

    Gomman iyalai ne ke ci gaba da duba ɓarnar da ambaliyar ta yi wa gidajensu, tare da ƙoƙarin neman kayayyakinsu.

    Mamakon ruwan sama ya afka wa birnin ne a ranakun Asabar da Lahadi.

    An ƙasa wucewa ta wata gada da za ta kai tsakiyar birnin Dar es Salam - ciki har da gidan shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan - saboda ambaliya, amma a yanzu ruwan ya ragu kuma ana iya wucewa.

    Hukumar lura da yanayi ta ƙasar Tanzaniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mamakon ruwan sama a tsawon wannan wata, yayin da shugaba Samia ta buƙaci mutane da su daga wuraren da ke barazanar faɗa wa cikin ambaliya.

  12. Hukumomi a Johannesburg za su sauya wa mutum 150 matsuguni bayan gobara

    ..

    Asalin hoton, Johannesburg Public Safety MMC/X

    Bayanan hoto, Gobarar da ta tashi ranar Lahadi, ta halaka mutum biyu tare da raunata karin hudu.

    Hukumomi a Afirka ta Kudu na shirin sauyawa fiye da mutum 150 da suka tsira daga gobarar da ta lakume wani gini da aka yi ba bisa ka'ida ba a Johannesburg.

    Gobarar da ta tashi ranar Lahadi, ta halaka mutum biyu tare da raunata karin hudu.

    Gobarar ta kuma daidaita iyalai da dama da ke zaune a ginin cikin muhalli mara tsafta.

    An kama wata mata saboda zargin tana da hannu a iza gobarar.

    Tashin gobara a gine-ginen da ake yi ba bisa ka'ida ba abu ne da ya zama ruwan dare a Johannesburg.

    Ire-iren gine-ginen galibi kan fada hannun miyagu da suke ba da haya ba tare da muhalli mai kyau ba.

  13. MDD ta ƙaddamar da gidauniyar neman kuɗi don magance ƙaurar mutane

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da gidauniyar neman tara dala biliyan 9 a bana, domin magance matsalar ƙaurar mutane.

    Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ƙaurar jama'a, ta ce akwai buƙatar bayar da tallafi ga gidauniyar domin samar da hanyar da ta dace ga masu yin ƙaurar.

    Shugabar hukumar, Amy Pope ta ce a bayyane take cewa idan aka kiyaye ƙa'ida, ƙaurar jama'a za ta kawo ci gaban duniya.

    Wannan ne dai karon farko da hukumar ke neman tallafi don gudanar da aikinta.

  14. Ruftawar ƙasa ta kashe mutum uku a Keffi

    ...

    Mutane uku sun rasu yayin da wasu kuma suka jikkata a wani hadarin zaftarewar kasa da ya faru a yankin Keffi na jihar Nasarawa ta Najeriya.

    Shugaban Karamar Hukumar ta Keffi, Muhammad Baba Shehu ya tabbatar da hakan a wata hira da BBC.

    Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da mutanen ke hakar yashi a wani wurin ɗibar yashi da ke unguwar Ayaba.

    Nasarrawa na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke da arziƙin albarkatun ƙasa.

    Haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da a lokuta da dama kan haifar da mutuwar mutane saboda rashin ɗaukar matakan kariya da suka kamata.

  15. Sabon shugaban Laberiya ya kusa shiɗewa a lokacin shan rantsuwa, Moses Kollie Garzeawu, daga Monrovia

    Joseph Boakai

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Joseph Boakai

    Sabon shugaban Laberiya, Joseph Boakai ya gaza kai ƙarshen jawabin shan rantsuwarsa yayin da ya kusa shiɗewa, inda aka rirriƙe shi a lokacin bikin wanda ya gudana a Monrovia, babban binrin ƙasar.

    Kafin nan ya kwashe kimanin minti 30 yana jawabi, inda daga baya magana ta fara yi masa wuya.

    Daga nan ne masu tsaron shi suka tattarbe shi tare da mayar da shi gida daga babban zauren majalisar dokokin ƙasar, inda bikin ya gudana.

    Daga nan ne aka kammala taron ba tare da an kai ƙarshe ba.

    An rantsar da sabon shugaban ƙasar na Laberiya mai shekara 79 a duniya ne a matsayin shugaba mafi tsufa a ƙasar, inda ake da tantama kan ƙoshin lafiyarsa.

  16. 'Isra'ila na yin luguden wuta mafi muni a Gaza'

    Falasdinawa da ke kudancin Gaza sun ce luguden wutar da Isra'ila take yi ta sama da kasa da ta ruwa shi ne mafi muni da suka taba gani tun bayan da yaki ya barke.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce akalla Falasdinawa 50 aka kashe sakamakon hare-haren Isra'ila a birnin Khan Younis tun daga daren Lahadi.

    Tankokin yakin Isra'ila sun isa kofofin asibitoci biyu a Khan Younis, inda suke hana mazauna daga samun kulawar likitoci.

    A Isra'ila, dubban masu zanga-zanga ne suka kutsa wani taro a majalisa inda suka nemi gwamnati ta kara kaimi domin ganin an sako mutanen da ake garkuwa da su a Gaza.

    Kididdigar baya-bayan nan daga ma'aikatar lafiyar ta Hamas ta nuna cewa hare-haren Isra'ila sun yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa fiye da 25,000 a Gaza.

  17. Yan sandan Kenya sun gano kokon kan wata daliba da aka yi wa kisan gilla

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Yan sanda a Kenya sun gano kokon kan wani da ake tunanin na wata daliba mai shekara 20 ne da aka yi wa kisan gilla a Nairobi, babban birnin kasar a farkon watan nan.

    An gano gawar Rita Waeni da aka saba wa kamanni cikin ledojin shara a wani gida ranar 14 ga watan Janairu sai dai kanta da wayarta da sauran kayan da ta mallaka sun bace.

    Yan sanda ba su kai ga tabbatar da ko kokon kan da aka gano ranar Lahadi a madatsar ruwa ta Kiambaa mai kusan nisan kilomita 15 daga wajen da aka yi kisan, na dalibar ne.

    "Gawar ta rube, an nannade ta cikin wata riga launin shanshanbale sannan kuma mun gano wani dutse. Muna tunanin an dasa dutsen domin gawar ta nutse," in ji shugaban yan sandan Kiambaa, Pius Mwanthi.

    Yan sanda sun kwaso wayar Ms Waeni da wasu kayanta da suka bace daga madatsar ruwan.

    Kisan Ms Waeni na ci gaba da jefa al'ummar Kenya cikin kaduwa musamman ganin irin mummunan kisan gillar da aka yi mata.

    "Wannan ne karon farko da na taba ganin irin haka. Ban taba ganin irin wannan kisa ba a shekarun da na shafe ina aikin binciken kwakwaf kan laifuka," in ji mai binciken gawa Johansen Oduor.

    Iyalan Ms Waeni a makon da ya gabata sun ce makisan dalibar sun nemi kudin fansar 500,000 a kudin Kenya domin su sake ta.

    Wani da ake zargi da hannu a kisan dalibar yana tsare.

  18. 'Abin da ya sa muka yi aure irin na Indiyawa'

    Bayanan bidiyo, Abin da ya sa muka yi aure irin na Indiyawa

    Auren Dakta Mayana Sanusi Abubakar da Khadija Halliru na ɗaya daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta na arewacin Najeriya a makon da ya gabata.

    Ma’auratan sun shirya wani biki wanda ba kasafai aka saba gani ba a yankin.

    Amarya da angon sun caɓa ado da kaya irin na ƴan ƙasar Indiya, wani abu daya sa aka riƙa yaɗa bidiyo da hotunan bikin a shafukan sada zumunta.

    Sai dai angon ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ya yi irin wannan auren ba, domina a aurensa na farko ma haka ya caɓa ado da kayan Indiyawa, shi da uwargidansa.

    “Aurena na farko ma matata irin waɗannan kaya ta saka.”

    Ya bayyana wa BBC Hausa cewa “Zama (a Indiya) ne ya sa al’adar Indiya ta shige ni kuma na ji ina sha’awar matata ta fito haka”.

    Dakta Mayana ya bayyana wa BBC cewa ya kwashe shekara bakwai yana karatu a Indiya, inda daga wannan lokacin ne yake sha’awar al’audun al’ummar Indiya.

    “Idan zama na sa mutum ya zama ɗan ƙasa (Indiya) to na zama, saboda shekara bakwai ba wasa ba ne,” in ji shi.

    A nata ɓangaren, Khadija Halliru ta ce ta amince ta yi shigar Indiya a lokacin bikin auren shi ne saboda angon nata yana so.

  19. Kusan mutum 90 sun mutu sanadin muku-mukun sanyi a Amurka

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Kusan mutum 90 ne suka mutu a sassan Amurka bayan da kasar ta shiga cikin yanayi na matsanancin sanyi.

    Akalla mutum 25 ne suka mutu a Tennessee sai 16 a Oregan da har yanzu ke karkashin dokar ta baci saboda matsanancin sanyi.

    Dubban mutane kuma suna cikin duhu saboda katsewar wutar lantarki.

    Bayanai na cewa yanayin na muku-mukun sanyin zai ci gaba har tsakiyar makon nan.

    Mutum 89 ne suka mutu jumulla sanadin sanyi mai tsanani a sassan Amurka cikin makon da ya gabata, kamar yadda kididdiga daga kafar CBS ta nuna.

    Akasarin mace-macen sun faru a Tennessee da Oregan. An kuma ba da bayanan mutuwar wasu a Illinois da Pennsylvania da Mississippi da Washington da Kentucky da Wisconsin da New York da New Jersey.

  20. Magoya bayan Arsenal sun yi addu'ar godiya a coci bayan lashe wasa

    ..

    Asalin hoton, Kennedy Muriithi

    Magoya bayan Arsenal a Nairobi, babban birnin Kenya sun taru a wani coci domin yin addu'a ta musamman domin nuna godiya bayan da kungiyar ta lallasa Crystal Palace da ci biyar babu ko daya a wasan Firimiya da suka buga ranar Asabar.

    Yayin taron addu'oin, magoya bayan sanye da rigunan Arsenal sun yi ta rera wakokin yabo tare da bayyana godiya ga kungiyar saboda bajintar da ta yi.

    Sun kuma yi addu'oin ganin Arsenal ta dore kan wannan tafarki a gasar.

    an jarida Kennedy Muriithi wanda daya ne daga cikin wadanda suka halarci taron addu'oin, ya wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.

    A yanzu Arsenal da Manchester sun yi canjaras a teburin gasar da maki 43 inda Liverpool ta sha gabansu da maki 5.

    Hotunan sun janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta inda wasu suke zolayar magoya bayan na Arsenal.

    ..

    Asalin hoton, Kennedy Muriithi