Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba, Ahmad Tijjani Bawage, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa, Kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya, musamman yadda hukuncin kotun ƙoli kan zaɓukan gwamnoni ya gudanar.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Al'ummar Bauchi su zo mu haɗa kai don gina jiharmu - Gwamna Bala
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya yi kiran haɗin kan ɓangaren adawar jihar domin ginawa da ciyar da jihar gaba.
Yayin da yake zantawa da manema labarai jim-kaɗan bayan kotun kolin ƙasar ta tabbatar da nasarar zaɓensa, Gwamna Bala Muhammad ya ce nasarar da ya yi a kotun ta al'ummar jihar ce baki ɗaya.
A yau ne kotun olin ƙasar ta tabbatar da nasarar gwamnan a zaɓen ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Sanwo-Olu ya yaba wa Tinubu kan hukuncin kotun ƙoli
Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/Facebook
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da shugaban Najeriya Bola Tinubu
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yaba da hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta yanke da ya tabbatar da nasararsa a zaɓen ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar Sanwo-Olu ya yaba wa shugaban ƙasar kan abin da ya kira ''ƙarfafa dimokraɗiyyar ƙasar'
Gwamnan ya ce samun nasararsa a kotun ƙolin zai bai wa gwamnatinsa damar ci gaba da kawo ayyukan ci gaba da ta faro a jihar tun 2019.
“Ina son yaba wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu musamman kan yadda ya yi ƙoƙarin ƙarfafa dimokraɗiyyar ƙasarmu''.
Ya kuma yi kira ga 'yan jam'iyyar adawa da su haɗa kai domin ciyar da jihar gaba.
A yau ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar da nasarar gwamna Sanwo-Olu na jam'iyyar APC.
Matatar mai ta Dangote ta fara aiki
Asalin hoton, X/@ALIKODANGOTE
Rahotonni daga Najeriya na cewa matatar mai ta Dangote ta fara aiki a yau Juma'a.
Babbar matatar da ke birnin Legas ta fara aikin ne bayan kammala ta tare da ƙaddamar da ita a watannin da suka gabata.
Matatar ta fara aikin ne bayan tara kimanin ganga miliyan shida na ɗanyen man fetur a wannan makon
A watan Disamban da ya gabata ne matatar ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.
Sabuwar matatar ta zama mafi girma a nahiyar Afirka.
A watan Nuwamba ne kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen man fetur ga matatar.
Wannan dai wani lokaci ne da aka daɗe ana jira a ƙasar ta Najeriya, ganin cewa ana sa ran matatar za ta sauya harkokin man fetur a ƙasar.
Duk da cewa Najeriya ce kan gaba wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka, amma ba ta iya tace shi domin samar da man fetur domin amfani a ƙasar, wadda ita ce kan gaba wajen yawan jama'a da ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka.
Amurka ta ce ta kai hari kan 'yan tawayen Houthi don karya ƙungiyar
Fadar White House ta ce hare-haren da jiragen yaƙin Amurka da na Birtaniya suka kai kan wuraren Houthi a ƙasar Yamen an yi su ne don karya ƙarfin da ƙungiyar, musamman wurin da take taskancewa da harbawa da kuma makamanta masu linzami da jiragen sama marasa matuka.
An kai harin ne bayan da 'yan Houthi suka sha kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya; suna da'awar cewa suna yin aiki tare da Falasdinawa a Gaza.
Kungiyar ta sha alwashin mayar da martani.
Gwamnonin jihohin da suka yi nasara a kotun ƙoli
Gwamnonin jihohin da suka samu nasara a shari'o'in zaɓukansu da kotun ƙoli ta yanke hukunci a yau Juma'a:
Dauda Lawan Dare na Zamfara - PDP
Caleb Mutfwang na Filato - PDP
Bala Mohammed na Bauchi - PDP
Abba Kabiru Yusuf na Kano - NNPP
Alex Otti na Abia - LP
Francis Nwifuru na Ebonyi - APC
Sanwo-Olu na Legas - APC
Bassey Otu na Cross River - APC
Tinubu ya dakatar da shirye-shiryen tallafin dogaro da kai na hukumar NSIPA
Asalin hoton, NSIPA
Bayanan hoto, Dakatarwar ta ƙunshi shirin N-Power
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar da duka shirye-shiryen yaƙi da talauci na hukumar NSIPA da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gamnatin ƙasar ta ce an ɗauki matakin ne domin gudanar da bincike kan zargin badaƙa tsakanin jagorancin hukumar da kuma yadda take gudanar da shirye-shiryenta.
Sanarwar ta ce an dakatar da duka shirye-shirye huɗu da hukumar ke jagoranta, kama daga shirin N- Power, da biyan kuɗaɗen tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi da tallafa wa masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i da shirin ciyar da ɗaliban makarantun firamare.
Sanarwar ta ƙara da cewa a matakin farko dakatarwar ta mako shida ne, kafin a kammala bincike kan batun.
Shugaba Tinubu ya kuma nuna damuwa kan samun kura-kurai a yadda ake tafiyar da shirye-shiryen musamman biyan kuɗi ga mutane da ke amfana dashirye-shiryen hukumar.
Shugaban ƙasar ya kuma kafa kwamitin dai zai gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar da nufin samar da sauyin da ake buƙata a ayyukan hukumar.
''Don haka an dakatar da duka ayyukan hukumar da suka haɗar da gudanarwa da biyan kuɗaɗe da yin rajista'', in ji sanarwar
Sanarwar ta ci gaba da cewa shugaba Tinubu na son tabbatar wa 'yan ƙasar da masu ruwa da tsaki , cewa a shirye gwamnatinsa take wajen tabbatar da gaskiya da adalci kan shirye-shiryen hukumar musamman kan niyar da aka kafata, na amfanar da masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.
Ina taya Abba Kabir murna kan nasarar da ya samu - Atiku
Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook
Bayanan hoto, Jagoran adawa na Najeriya, Atiku Abubakar
Jagoran adawa a Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya taya gwamnonin jihohin da suka samu nasara a kotun ƙolin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku Abubakar ya ce hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da nasarar al'ummar jihohin Bauchi da Filato da Akwa Ibom da Zamfara, tare da ɗaga martabar dimokraɗiyya a ƙasar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma miƙa sakon taya murna ga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP kan nasarar da ya samu a kotun ƙolin.
''Wannan hukunci ya ba ni damar tabbatar da ƙudurina na cewa haɗin kan jam'iyyun adawa zai taimaka wajen ƙarfafa dimokraɗiyyar Najeriya'', in ji Atiku.
''Don haka a shirye nake na jagoranci wannan ɓangare, ta hanyar yin aiki tare da shugabanni da gwamnoni don tabbatar da ci gaban ƙasarmu''.
Jagoran adawar ya ci gaba da cewa hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da ƙarfin da jam'iyyarsa ta PDP ke da shi a jihohin da take mulki.
''Ina kira da gwamna Bala Muhammadu na Bauchi da Dauda Lawal na Zamfara da Barista Caleb Muftwang na Filato da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom da su ɗauki nasarar da suka samu a kotun ƙolin a matsayin wata dama da za su sake inganta jagorancin da suka riga suka fara kafawa a jihohinsu'', in tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Ya kuma ce ''ina da yaƙinin cewa jam'iyyarmu ta PDP za ta ci gaba da kasancewa babbar jam'iyyar adawa a ƙasar, da taimakon gwamnoni da kuma ni kaina, a yayin da za mu tunkari kakar zaɓe mai zuwa''.
Za mu shirya don tunkarar zaɓen 2027 - Jam'iyyar APC a Kano
Asalin hoton, FACEBOOK/FAIZU ALFINDIKI
Jam'iyyar APC a Kano sun ce sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotunƙolin Najeriya da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.
Sakataren jam'iyyar na jiha Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa BBC cewa sun karɓi ƙaddara, suna kuma fatan hakan ya zame musu alkairi.
''Allah ya sa hakan ne ya fi alkari, kuma muna bai wa 'yan jam'iyar mu na APC tda sauran al'ummar jihar kano hakuri, tare da kiran a zauna lafiya'', in ji shi.
Ya ce kuma suna kyautata wa Allah zato cewa tabbas hakan zai zama alkairi a gare su.
''A yanzu muna cikin alhini, kuma bai kamata mu ɗauki mataki a lokacin alhini ba, amma idan ƙura ta lafa, za mu zo mu zauna, mu shirya domin tunkarar zaɓen 2027''.
Tun da farko dai jam'iyyar ce ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, kafin yau kotun ƙoli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan farkon.
Ku zo mu haɗa hannu don ceto jihar Zamfara - Dauda Lawan Dare
Asalin hoton, Zamfara State Govt.
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya yi kira ga jam'iyyar adawa da ta zo a haɗa kai wajen ceto jihar daga halin da take ciki.
Gwamna Dauda ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi bayan da Kotun Koli ta tabbatar da nasararsa a matsayin gwamnan jihar Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamna Lawal ya ce hukuncin kotun ya nuna abin da al'ummar Zamfara suka zaɓa, inda ya ce aiki tare na da muhimmanci musamman wajen samun ci gaba.
Gwamnan ya ce nasarar ta al'ummar jihar Zamfara ne baki-ɗaya.
"Ya kamata mu haɗa kai da aiki tare don samar da kyakkyawar makoma ga Zamfara. Ina cike da murna kan tabbatar min da nasara da Kotun Koli ta yi a yau," in ji Dauda Lawal.
Ya ce wannan nasara za ta ƙara masa kwarin gwiwar cika alkawuran da ya yi wa al'umma lokacin yaƙin neman zaɓe.
"Hukuncin kotun ya tabbatar da abin da al'ummar jihar Zamfara suka zaɓa a zaɓen gwamna da aka yi a watan Maris ɗin bara. Ina kira ga al'ummar Zamfara, ciki har da jam'iyyun adawa da su zo mu haɗa hannu da kuma aiki tare don sake ginawa da ceto jihar," in ji gwamnan.
Ya kuma ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin gaggawa don kuɓutar da Zamfara daga rashin kyakkyawan shugabanci.
Isra'ila ta ce Afirka ta Kudu ta jirkita gaskiya a zargin kisan ƙare-dangi
Isra'ila ta ce Afirka ta Kudu ta jirkita gaskiya a shari'ar da suke yi a Kotun Duniya ta ICJ, inda Afirka ta Kudu ta shigar da ƙararta kan zargin aikata kisan ƙare-dangi kan Falasɗinawa
Lauyan Isra'ila, Tal Becker ya faɗa wa kotun cewa Afirka ta Kudu ya gabatar da abin da ya kira ''jirkita gaskiyar abin da ya faru'' a rikici tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.
Afirka ta Kudu dai na zargin Isra'ila da aikata kisan ƙare-dangi kan Falasɗinawa a yaƙin da take yi a Gaza.
Sannan ta yi kira ga kotun da ta dakatar da Isra'ila da kai hare-haren soji zuwa cikin Gaza.
Isra'ila na bayar da bahasi ne kwana guda bayan Afirka ta Kudu ta gabatar wa kotuntuhume-tuhumen kisan ƙare-dangi da take zargin Isra'ila da aikatawa.
Kotun ta ICJ ita ce babbar kotun MDD, kuma dole ne ƙasashen da suka rattaɓa hannu a kafuwarta - ciki har da Isra'ila da Afirka ta Kudu -su yi biyayya ga hukuncinta, sai dai kuma ba za a tilasta wa kowace ƙasa yin biyayya ga hukuncin ba.
Kotun ƙoli ta tabbatar da Francis Nwifuru a matsayin gwamnan Ebonyi
Asalin hoton, FRANCIS NWIFURU/FACEBOOK
Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da zaɓen Francis Nwifuru na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.
Kotun ta tabbatar da matakin kotun ɗaukaka ƙara a Legas inda ta kori ƙarar da Chukwuma Odii na jam'iyyar PDP ya shigar saboda rashin cancanta.
A baya, alƙalan kotun ɗaukaka ƙara sun yanke hukunci a watan Nuwamban bara cewa PDP da ɗan takararta ba su da hujja bisa doka ta yin katsalandan cikin harkar jam'iyyar APC wajen fitar da gwanin da zai yi mata takara.
Kotun Duniya za ta saurari bahasin Isra'ila kan zarginta da kisan kare dangi
A yau ne babbar kotun MDD za ta saurari bahasin Isra'ila kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar kan zarginta da aikata kisan kare dangi a yaƙin da ta ke yi a Gaza.
Ita ce rana ta biyu kuma ta karshe na zaman kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague, inda za ta mayar da hankali kan buƙatar Afirka ta Kudu na ɗaukar matakin bai wa Falasɗinawa kariya.
Tun da farko, Firaiminista Benyamin Netanyahu ya kare ƙasarsa da cewa; "Muna yaƙar 'yan ta'adda ne da yakar karya, a yau muna ƙara ganin duniya mai fuska biyu.
Ana zargin Isra'ila da aikata kisan kare dangi a daidai lokacin da take ci gaba da gwabza faɗa da mayakan Hamas a Gaza.
Murnar magoya bayan jam'iyyar NNPP a Kano
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidyon
Ina godiya ga al'ummar Kano bisa addu'o'in da suka yi min - Abba Kabir
Asalin hoton, Abba Kabir Family
Bayanan hoto, A ranar 20 ga watan Maris ne hukumar INEC ta sanar da Abba Gida-gida a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya yi farin ciki maras misaltuwa da hukuncin kotun ƙolin da ya tabbatar da nasararsa a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
Yayin da yake magana da manema labarai a harabar kotun jim-kaɗan bayan yanke hukuncin, gwamna Abba Kabir ya ce ya gode wa al'ummar jihar Kano da ma na Najeriya baki ɗaya bisa addu'o'in da suka shafe watanni suna yi masa.
A yau ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar da nasarar Abba, inda ta soke hukuncin kotun ɗaukakka ƙara da ta ce Abba ba halastaccen ɗan jam'iyyar NNPP ba ne.
Tun da farko a cikin watan Satumba kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, inda ta ce Nasiru Gawuna na APC ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ƙoli ta ce Caleb Mutfwang ne halastaccen gwamnan Filato
Asalin hoton, @CalebMutfwang/X
Kotun ƙoli ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato.
Mutfwang na Jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 525,299 inda ya doke abokin takararsa na jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda da ya samu ƙuri'u 481,370 a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Jos, babban birnin jihar ya tabbatar da zaɓen gwamna Mutfwang.
Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a Abuja a nata hukuncin ranar 19 ga watan Nuwamban bara ta soke nasarar Mr Mutfwang lamarin da ya sa gwamnan ya garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara da nufin ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun.
An rage lokutan ibada a Zambiya don daƙile yaɗuwar kwalara
Asalin hoton, Zambian presidency/Facebook
An bai wa coci-coci a Zambia umarnin rage lokutan yin ibada zuwa sa'o'i biyu a cikin matakai da ake ɗauka don daƙile yaɗuwar cutar kwalara.
An kuma hana sayar da nau'in abincin da zai iya lalacewa ko kuma wanda aka riga aka dafa a dukkan majami'u, a cewar wani babban jami'in kula da harkokin addini, Ndiwa Mutelo.
Har ila yau, an buƙaci masu ibada da su guji gaisawa da hannu da kuma runguma don rage barazanar kamuwa da cutar.
Cikin wata sanarwa da Mista Mutelo ya fitar, ya ce an kuma umarci wuraren ibada da su samar da tsaftataccen ruwan sha, da wuraren wanke hannu da kuma man goge hannu ga dukkan mambobi.
Sama da mutum 7,800 aka ruwaito cewa sun kamu da kwalara a faɗin ƙasar tun daga watan Oktoban bara.
A cikin sa''o'i 24 da suka wuce, an samu mutum sama da 400 da suka kamu da cutar da mutuwar 18, a cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar.
Kotun ƙoli ta tabbatar da sahihancin zaɓen Dauda Lawal na Zamfara
Asalin hoton, facebook/Dauda Lawal
Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Lawal Dare na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Zamfara.
Kotun ƙolin ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba inda ta ba da umarnin a sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi uku.
Hukumar zaɓe dai ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.
Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi Inec da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.
Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Abba a matsayin gwamnan Kano
Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed na Bauchi
Asalin hoton, X/Bala Mohammed
Bayanan hoto, Bala Mohammed
Kotun ƙolin Najeriya da ke zaman ta a Abuja ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad na PDP ya samu a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
A hukuncin da ta zartar a yau Juma'a, kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Siddique Abubakar wanda ya ƙalubalanci hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da na sauraron ƙorafin zaɓen jihar, waɗanda suka tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed.
Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe a shari'ar da ake yi ta tantance ingancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen na watan Maris.
Bala Mohammed ya lashe zaɓen ne a ƙoƙarin sa na neman karo na biyu na mulkin da ya fara a a watan Mayun 2019.
Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.
Saddique Abubakar dai yana tunƙahon cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.
Sai dai, kotun ɗaukaka ƙara ta ce ɗan takarar na APC ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tallafi zarge-zargensa.
Duk da haka, bai yi ƙasa a gwiwa ba, a Juma'ar nan Saddique Abubakar yana fatan kotun ƙoli za ta yi hujjojin da ya gabatar duban basira, kuma ta ba shi gaskiya, yayin da abokin takararsa na PDP ke fatan alƙalan kotun kamar takwarorinsu na kotunan baya, su kori wannan ƙara.