Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen shafinmu na kai tsaye, wanda muka kawo muku wainar da aka toya a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    A madadin sauran abokan aiki, Badriyya Tijjani Kalarawi da Mukhtari Adamu Bawa ke muku sallama daga nan Sashen Hausa na BBC.

    Allah ya tashe mu lafiya.

  2. Gwamnatin Najeriya za ta karbe lasisin masu hakar ma'adinai

    Ministan albarkatun kasa na Najeriya, Dr Dele Alake, ya ce a wannan shekarar ta 2024 gwamnatin kasar za ta karbe karin lasisin wasu masu hakar ma'adinai a kasar.

    Alake ya bayyana hakan ne a sakon sa na sabuwar shekarar 2024 ga 'yan kasar daga gidansa a jihar Lagos.

    Kamfanin dillacin Najeriya NAN, ya rawaito gwamnatin Najeriyar ta sanar da yi wa lasin hakar ma'adinai 1,633 daga hannun wadanda ba su biya kudaden da ya kamata su biya gwamnati da suka hada da haraji ba a shekarar da 2023 da ta wuce.

    Ministan ya kara da cewa gwamnatin Najeriyar ta na gayyatar masu zuba jari daga kasashen ketare a fannin hakar ma'adinan, dan haka zamanin kin biyan gwamnati hakkinta ya wuce.

    Ana fama da matsalar masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Najeriyar, da masu lasin da ba sa biyan kudaden haraji a fannin hakar ma'adinan.

  3. Dubban mutane za su kwana a waje bayan wata gagarumar girgizar ƙasa a Japan

    Dubban mutane ne za su kwana a sansanonin da aka kafa a sararin Allah, bayan mummunar girgizar kasa ta afkawa kasar Japan.

    Akalla mutane 2 ne aka tabbatar da mutuwarsu, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Kydo ya sanar, amma ana fargabar adadin ka iya fin haka a kwanaki masu zuwa.

    Gwamman gine-gine sun ruguje a garuruwa da dama, inda ake fargabar mutane da dama sun makale a baraguzan gini.

    Da safiyar Litinin ne girgizar kasar ta afku da ta kai maki 7.6, kuma tun da fari an yi gargadin za afuskanci Tsunami amma daga bisani aka yi watsi da hakan..

  4. An naɗa tsohon ɗan adawa a matsayin firaministan Chadi

    Shugaban gwamnatin riko ta Tchadi, Janaral Mahamat Idriss Deby, ya nada tsohon madugun ‘yan adawa Succes Masra a matsayin firaiminista.

    Mr Masra, shi ne shugaban jam’iyyar adawa ta Reformers, ana kallon nadinsa a matsayin wani muhimmin mataki a kokarin da ake yi na sasantawa da ‘yan adawa da dawo da zaman lafiya a Chadi.

    Ya yi fice wajen sukar manufofin gwamnati, kuma bai jima da komawa kasar daga gudun hijirar da ya yi, bayan hukumomin kasar sun amince ya koma gida.

    Ana sa ran Success Masra zai taka muhimmiyar rawa domin tabbatar an gudanar da zabe a shekarar nan, kamar yadda gwamnatin mulkin soja ta yi alkawari.

    A watan Disambar 2023 ne, aka gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a, da amfani da sabon kundin tsarin Mulki, wanda masu suka ke ganin zai karawa shugaban kasa karfin iko.

    An kuma yi amanna wani kokari ne da Janaral Mahamat Deby ke yi na ci gaba da zama kan Mulki kamar mahafinsa.

    A shekarar 2021 ne ya zama shugaban gwamnatin riko ta Chadi, bayan rasuwar mahaifinsa da ya shafe shekaru sama da 30 akan Mulki.

  5. Jaririn da aka fara haifa a asibitin ƙasa na Najeriya a 2024

    Nigeria's First Lady

    Asalin hoton, Presidency Nigeria

    Bayanan hoto, Matar shugaban Najeriya Senata Remi da matar mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima

    Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga mata masu juna biyu su dauki zuwa asibiti domin duba lafiyarsu da muhimmanci, da yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

    Sanata Remi ta ce wannna zai bai wa jami'an lafiya damar bin hanyoyin kare jaririn da ke cikin uwa daga kamuwa da cutar, da tabbatar da ingancin lafiyar uwa da jaririnta.

    Misis Remi ta bayyana hakan ne a wata ziyara da ta kai Babban asibitin gwamnatin Tarayya da ke Abuja, inda ta tarbi jaririn farko da aka haifa a wannan sabuwar shekarar ta 2024.

    Ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni su shiga a dama da su wajen taimakawa gwamnati na cika burin samar da ingantaccen fannin lafiya ga 'yan Najeriya baki daya.

  6. Hotuna: Yadda mutane ke zaune a waje bayan girgizar ƙasa ta ɗaiɗaita gidajensu

    Bari mu duba wasu daga cikin hotunan da muka samu daga kasar Japan, inda aka umarci dubban mutane ficewa daga muhallansu, wasu ma a mastugunan wucin gadi da aka kafa a wurin za su kwana.

    Matsugunin wucin gadi a Kanazawa

    Asalin hoton, Kyodo/Reuters

    Bayanan hoto, Mazauna yankin da giurgizar kasar ta shafa, sun samu matsugunin wucin gadi a wata makaranta da aka kafa a Kanazawa
    Kanazawa

    Asalin hoton, Kyodo/Reuters

    Bayanan hoto, An maida yawancin gine-ginen gwamnati an maida su mazaunin wucin gadi, kamar dai wannan ginin ainahi ofishin gwamnati ne a Kanazawa
    Joetsu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Su kuma wadannan mutanen sun samu mafaka a wani katon wurin wasanni da ke Joetsu, a Japan
    Wajima

    Asalin hoton, Kyodo/Reuters

    Bayanan hoto, Tun da fari, mazauna yankin sun fiuce tare da nausawa kan tudu da ke Wajima domin tsira daga girgizar kasar da ta afkawa mazauninsu.
  7. Kotun koli a Isra'ila ta yi watsi da sauyi a fannin shari'a

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, AP

    Bayanan hoto, A shekarar da ta gabata an yi ta zanga-zangar kin amincewa da dokar a daukacin Isra'ila

    Kotun koli a Isra'ila ta yi watsi da dokar yin sauye-sauye a fannin shari'ar kasar mai cuike da cece-kuce da ya janyo zazzafar zanga-zanga a shekarar da ta gabata kan kan gwamnatin Benjamin Netanyahu.

    Sauyin dai zai ragewa kotun koli karfin fada aji, da bai wa gwamnati karin iko wajen nada sabbin alkalai.

    Masu sukar lamiri sun ce, idan aka amince da matakin zai kassara dimukradiyya tya hanyar raunana fannin shari'ar.

    Ana ganin wannan mataki dai mai girma ne musamman fannin abokan adawar Netanyahu. Matakin kotun kolin na yin watsi da kudurin dokar da gwamnati ta gabatar a shekarar 2023, ya biyo bayan watannin da aka dauka ana gudanar da zanga-zanga a daukacin kasar ta Isra'ila.

    A watan Yuli ne gwamnati ta gabatar da kudurin dokar, da zai ragewa alkalan kotun kolin karfi baki daya.

  8. 'Yan Najeriya da burinsu a 2024

  9. Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan kasafin kuɗin 2024

    Nigeria budget signing

    Asalin hoton, Presidency Nigeria

    Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu kan ƙudurin kasafin kuɗin bana na sama da naira tirliyan 28 zuwa doka, jim kaɗan bayan komawarsa Abuja daga Lagos.

    Ya dai bai wa al'ummar Najeriya tabbacin cewa zai bi diddigi wajen ganin yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin, ya kuma ce ya umarci dukkan ma'aikatu da hukumomi su riƙa bayar da rahoton yadda suke aiwatar da kasafin kuɗin wata-wata ga ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar ta ce manyan ɓangarorin da kasafin kuɗin ya mayar da hankali a kansu akwai tsaron ƙasa da samar da tsaro a cikin gida, samar da aikin yi da daidaita harkokin tattalin arziƙi da bunƙasa yanayin zuba jari da rage talauci.

    Shugaba Tinubu ya nanata cewa ƙudurinsa na kyautata harkokin zuba jari da ƙoƙarin samar da al'umma mai bin doka wadda ba za ta fifita kowanne mutum ba, zai fara da muhimman sauye-sauye a ɓangaren shari'a, wanda kuma an samar da kuɗaɗen yin su a cikin kasafin kuɗin.

    "Samar da kuɗi ga ɓangaren shari'a wani muhimmin ƙuduri ga ƙoƙarinmu wajen tabbatar da wata al'umma mai bin doka da tsayawa a kan daidai. An ƙara kuɗaɗen da ake warewa ɓangaren shari'a daga tushe daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342," cewar shugaban ƙasar.

    Sanarwar ta ce muhimman alƙaluma a cikin kasafin kuɗin su ne manyan ayyuka naira tirliyan goma da ayyukan yau da kullum naira tirliyan 8.8 sai biyan basuka tirliyan naira 8.2 sai kason tallafi na doka daga asusun tarayya naira tirliyan 1.7.

  10. Kotu ta ɗaure Muhammad Yunus da ya taɓa lashe kyautar Nobel a gidan yari

    Muhammad Yunus

    Asalin hoton, EPA

    Wata kotu a Bangladesh ta yanke wa mutumin da ya taɓa lashe kyautar Nobel a fannin zaman lafiya Muhammad Yunus hukuncin ɗaurin wata shida a gidan yari saboda keta dokokin ƙwadago na ƙasar.

    Farfesa Muhammad Yunus ya kasance mai sukar lamirin Firaminista Sheikh Hasina.

    Magoya bayansa sun ce shari'ar tana da alaƙa da siyasa.

    An samu masanin tattalin da ake kwarzantawa da wasu abokan aikinsa uku daga Grameen Telecom - ɗaya daga cikin kamfanonin da ya kafa - da laifin gazawa wajen kafa wani asusun kyautata jin daɗin ma'aikatansu.

    Dukkansu su huɗun sun musanta aikata wani ba daidai ba kuma an ba da belinsu ya zuwa lokacin da za a kammala sauraron ɗaukaka ƙara.

    Farfesa Muhammad Yunus ɗan shekara 83 wanda a faɗin duniya aka fi saninsa da "mai bankin talakawa", ana yaba masa saboda ɓullo da wani tsari na ba da rance mai sauƙi don taimaka wajen fitar da miliyoyin mutane daga talauci.

    A 2006 ne aka bai wa Farfesa Yunus da Bankinsa na Grameen kyautar zaman lafiya ta Nobel saboda kasancewa a kan gaba fagen aikinsu.

  11. Isra'ila ta ce akwai yiwuwar yaƙin Gaza zai ci gaba tsawon shekara ta 2024

    Gaza destruction

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana tsammanin rikici a Gaza zai ci gaba da gudana a tsawon shekara ta 2024.

    A wani saƙon sabuwar shekara, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari ya ce an daidaita harkar tura dakarun soji don shirin tunkarar "faɗa na tsawon lokaci".

    Ya ce za a janye wasu dakaru - musamman ma sojojin wucin gadi - don ba su damar sake tattaruwa.

    "Waɗannan gyare-gyare ana yin su ne don tabbatar da ganin an yi tsare-tsare da shirye-shirye da nufin ci gaba da yaƙi a shekara ta 2024," in ji shi.

    Ya ce wasu sojoji masu wucin gadi za bar Gaza "tun a wannan mako" don ba su damar "sake kintsawa gabanin wasu ayyuka da ke tafe".

    Mutum 21,978 - akasari mata da ƙananan yara ne - aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon Hamas. Ta kuma an jikkata mutum 56,697 a Gaza a tsawon wannan lokaci.

    Adadin ya haɗar da na mutum 156 da aka kashe da 246 da aka ji wa raunuka a tsawon sa'a 24 da ta wuce, ma'aikatar ta ƙra da cewa.

  12. Hotuna: Girgizar ƙasa ta janyo rugujewar gidaje da tsagewar tituna

    Ga ƙarin hotuna yanzu da ke irin ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi a wasu sassa na Lardin Ishikawa.

    A building in Kaga city

    Asalin hoton, Kyodo via Reuters

    Bayanan hoto, Girgizar ƙasa ta janyo rugujewar wani ɓangare na wannan gini a birnin Kaga
    A scene of earthquake destruction in Wajima

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Tsananin ɓarnar da girgizar ƙasa ta haddasa wa gidaje a Wajima
    Road cracks from earthquake

    Asalin hoton, Kyodo via Reuters

    Bayanan hoto, Tsananin girgizar ƙasa ya sa har tituna sun riƙa tsattsagewa
    Wajima

    Asalin hoton, Mutane sun tsere zuwa wani filin ajiye motoci na wata makaranta a birnin Wajimi bayan an yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliyar teku ta Tsunami

    Bayanan hoto, Kyodo via Reuters
  13. An yi gargaɗin fuskantar Tsunami bayan girgizar ƙasa a Japan

    An yi gargaɗi kan yiwuwar fuskantar wata gagarumar ambaliyar teku a Japan bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin 7.6 a kan mizani ta auka wa yankin tsakiyar ƙasar.

    An buƙaci mutanen da ke zaune a yankunan gaɓar teku - musamman a lardin Noto - sun tsere zuwa yankunan da ke kan tudu.

    Hukumomi sun yi gargaɗin cewa igiyoyin ruwa za su iya kai wa har tsawon mil biyar a lardin Noto.

    Sun kuma bayar da gargaɗin samun ambaliyar teku ta tsunami a maƙwabtan yankuna kamar Niigata da Toyama, inda suka ja kunnen cewa igiyoiyin ruwa za su iya kai wa tsayin mil uku.

    Jami'ai a Birnin Suzu da ke Lardin Ishikawa sun ce gidaje da dama da kuma turakun wutar lantarki sun karye a can bayan girgizar ƙasa, a cewar tashar yaɗa labaran ƙasar ta NHK.

    Bayanan bidiyo, Lokacin da girgizar ƙasa ta auka wa garin gaɓar teku na Japan
  14. Wasan tartsatsin wuta da shagulgulan maraba da sabuwar shekara ta 2024 a sassan duniya

    Bayanan bidiyo, (Gargaɗi: Akwai walwalin fitilu masu haske idanu) Bukukuwan da tartsatsin wuta yayin da duniya ke yin maraba da shekara ta 2024
  15. Matatar man fetur ta Fatakwal ta fara aikin gwaji

    Jaridar Punch a Najeriya ta ce kamfanin samar da man fetur na ƙasar NNPCL ya fara kai ɗanyen man fetur don ayyukan tace mai na gwaji a matatar man fetur ta Fatakwal.

    Ta dai ambato wasu jami'ai na NNPCL na tabbatar mata da hakan, kuma ta ƙara da cewa dillalan man fetur su ma sun shaida mata wannan al'amari, da kuma cewa matatar za ta riƙa tace man fetur da dizal da kuma sauran nau'o'in mai don jihohin Najeriya 12 ciki har da Abia da Rivers da Akwa Ibom da Delta.

    Ta ce NNPPCL ya shaida mata cewa nan gaba kaɗan za a kammala ayyukan tace mai na gwaji da ake yi a matatar Fatakwal, don fara tace ɗanyen man fetur da za a iya sayarwa a kasuwa.

    A ranar 21 ga watan Disamba ne, gwamnatin Najeriya ta ba da sanarwar cewa an kammala wasu gyare-gyare a wani sashe da ake kira Area-5 na matatar Fatakwal da ke cikin jihar Rivers.

    Ta ce ɓangaren farko na matatar ya kammala kuma za ta fara tace ɗanyen man fetur ganga 60,000 a kullum bayan hutun Kirsimeti.

    Rahoton na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC a ranar Lahadi ta soki lamirin gwamnati saboda abin da ta kira gazawarta wajen cika alƙawurra da yawa da ta yi wa 'yan Najeriya ciki har da alƙawarin cewa matatar man fetur ta Fatakwal za ta fara aiki a wannan wata na Disamba.

  16. Abubuwan da muke sa ran za su faru a 2024

    Crescent

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani kusufin wata da aka ɗauki hotonsa a wani gidan adana kayan tarihi cikin birnin Ciudad Juarez, na ƙsar Mexico a watan Oktoba

    Mafi yawan sassan duniya sun shiga sabuwar shekara ta 2024, don haka bari mu ɗan yi duba kan abubuwan da shekarar mai yiwuwa ta tanadar wa rayuwarmu. Mun zayyana 'yan batutuwa ƙalilan don ku yi tunani a kai.

    Janairu- Gasar cin Kofin Afirka wadda Ivory Coast za ta karɓi baƙunci, za ta kankama.

    Fabrairu- Kamar kullum za mu iya sa ran ganin Sabuwar Shekarar Gargajiya a wasu ƙasashe na faɗin duniya (kamar wadda aka fi sani da sabuwar shekarar al'ummar China)

    Maris- Vladimir Putin, mutumin da ya jagoranci Rasha a matsayin firaminista da kuma shugaban ƙasa tun 1999, zai sake tsayawa takara a wa'adi na biyar.

    Afrilu- Mutane a Amurka za iya ganin kusufin wata na ƙarshe a ƙasar cikin sama da shekara 20, wanda akan yi shagulgula a Arkansas.

    A Afrilu zuwa Mayu muna kuma sa ran ganin babban zaɓen Indiya.

    Mayu- Kumbon zuwa duniyar wata na China mai suna Chang’e-6 zai yi ƙoƙarin tattaro sama da kilogram biyu na samfura daga sashen duhu na Wata.

    Yuni- Mata biyu za su shiga takarar shugaban ƙasa a Mexico yayin da kuma za a buɗe Gasar cin Kofin Turai na UEFA Euro 2024 a Jamus. Sai Gasar cin Kofin Duniya na wasan Kurket mai taken T20 wanda Amurka za ta karɓi baƙunci.

    Yuli- Za a fara wasannin Olympic na birnin Paris.

    Agusta- Za a fara gasar tseren mata ta Tours de France a Netherlands kuma a kawo ƙarshe a Faransa.

    Oktoba- Rasha za ta karɓi baƙuncin babban taron BRICs a kudu maso yammacin birnin Kazan.

    Nuwamba- Ma'aikatan farko na kumbon zuwa duniyar wata a cikin shekara 52, 'yan sama jannati huɗu za su tafi zuwa sararin wata tsawon kwana goma.

    Za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Amurka, kuma ga dukkan alamu za a sake fafata takara ne tsakanin Joe Biden da kuma Donald Trump ne.

    • Ƙayatattun hotuna daga faɗin duniya na 2023
    • Mace-macen da suka fi ɗimauta 'yan Najeriya a 2023
  17. Shagulgulan sabuwar shekara daga faɗin duniya

    Akasarin al'ummar duniya a yanzu sun shiga sabuwar shekara, kuma a nan ƙasa ga wasu hotuna masu ƙayatarwa daga faɗin duniya yayin da mutane ke murna.

    Revellers

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An ga 'yan biki suna tsalle a gefen teku yayin da tartsatsin wuta ke fashewa a sararin samaniyar bakin tekun Copacabana a Rio de Janeiro
    2024 Celebrations

    Asalin hoton, USA Sport Today

    Bayanan hoto, Yanzu ga wani wuri daga sashen birnin Dallas yayin da tartsatsin wuta ya dallare samaniyar birnin saboda murnar sabuwar shekara
    Reveller

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata kwance a ƙasa tana birgima a cikin ƙyallaye masu launukan ban sha'awa na confetti bayan dare ya raba a Dandalin Times Square na birnin New York
    Ahmedabad, India

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Masu taron addu'o'i suna maraba da sabuwar shekara a Wurin Ibada na Sun Temple da ke ƙauyen Modhera a kusa da Ahmedabad cikin ƙasar Indiya.
  18. Ina sane da duk guna-guninku game da matsin rayuwa - Bola Tinubu

    President Tiubu

    Asalin hoton, BAYO ONANUGA/X

    Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin gina ƙasa da za ta tabbatar da daidaito da adalci da kuma rage giɓin da ke tsakanin al'umma.

    Ya ce ko da yake ya yi imani masu kuɗi su ci moriyar dukiyar da suka mallaka da guminsu, amma jazaman ne duk wani ɗan Najeriya mai aiki tuƙuru ya samu damar da zai ci gaba a rayuwa.

    Shugaba Tinubu na wannan bayani ne a cikin jawabin da ya gabatar na shiga sabuwar shekara ta 2024.

    Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki ba kama hannun yaro don tabbatar da ganin duk 'yan Najeriya sun ɗanɗani daɗin gwamnatinsu.

    Tinubu ya ce abin murna sosai yi wa al'ummar ƙasar maraba da shiga sabuwar shekara ta 2024, kuma dole ne su ɗaga hannu don yi wa Allah godiya da wannan karimci da baiwa da ya yi wa Najeriya da kuma rayukan al'ummarta.

    Ya ce a tsawon wata bakwai da ya shafe a kan mulki, ya ɗauki wasu matakai da suka wajaba kuma masu wahala don ceto ƙasar daga shiga bala'in tattalin arziƙi, daga ciki akwai batun cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canza kuɗaɗen ƙasashen waje, da ke amfanar masu kuɗi kawai

    Shugaba Tinubu ya ce yana sane da cewa a lokuta da dama hirarraki da muhawarorin jama'ar Najeriya na mayar da hankali ne a kan batutuwan tsadar rayuwa da matsanancin hauhawar farashi wanda a yanzu ya kai kashi 28% da kuma yawan marasa aikin da ba za a amince da shi ba.

    • Yawan matalauta ya ƙaru zuwa miliyan 104 a Najeriya
    • 'Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara'
  19. Bidiyon kaɗawar agogon London don shiga sabuwar shekara

    Bayanan bidiyo, Bugun ƙararrawar agogon bangon London da ake kira Big Ben don shiga sabuwar shekara

    Yayin da duniya ke ci gaba da yi wa juna fatan alheri game da murnar shiga sabuwar shekara ta 2024 lafiya, bari mu koma baya kaɗan don ganin gagarumin wasan tartsatsin wuta da aka yi birnin London.

    A bana ne aka cika shekara 100 cif tun lokacin da BBC radio ta fara gabatar da bugun ƙararrawar babban agogon London da ake kira Big Ben, don yi maraba da sabuwar shekara.

    • Fatan ma'aikatan BBC game da sabuwar shekara ta 2024
  20. Ƙarin hotunan bikin sabuwar shekara daga Las Vegas

    Ga ƙarin hotuna daga birnin Las Vegas yayin da suka yi maraba da shiga sabuwar shekara ta 2024 ɗazu-ɗazun nan.

    Rahotanni sun ce mafi yawan jihohin Amurka a yanzu sun shiga sabuwar shekarar, amma dai har yanzu akwai ƙarin al'ummomin yammacin ƙasar kamar Alaska da Hawaii da ke yankin Tekun Fesifik.

    Fireworks
    Fireworks
    2024

    Asalin hoton, Reuters