Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.

  2. Sweden na daf da shiga ƙungiyar NATO

    Sweden - NATO

    Asalin hoton, EPA

    Ƙasar Sweden ta kai mataki na gaba a ƙoƙarin da ta ke yi na shiga ƙungiyar tsaro ta NATO, bayan kwamitin majalisar Turkiyya sun nuna amincewa da shigarta a fakaice.

    Tun a bara ne Sweden ta shigar da buƙatar shiga NATO, lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

    Ana buƙatar dukkan Ƙasashe mambobi kafin tabbatar da hakan, da farko Turkiyya ta buƙaci wasu abubuwa kafin ta amince.

    Ana sa ran ɗaukar makonni kafin Turkiyyar ta sanar da amincewarta a hukumance.

    A baya dai shugaba Rajib Tayyip Erdogan ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince ammna za a ɗauki lokaci saboda wasu dalilai.

    A ɓangare guda ita ma Hungary ba ta aike da amincewarta a hukumance ba.

  3. Iran ta ƙara yawan makamashin Uranium da take samarwa

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Iran ta ƙara yawan sinadarin Uranium da take samarwa.

    Wani rahoto da hukumar ta fitar, wanda kamfanin dillancin labaran reuters ya gani, ya bayyana cewa Tehran na ƙara yawan kayayyakin nukiliya da kashi 60, wanda ke kusa da matakin kera makamai..

    Ta ce masu sa ido sun lura da sauyin ne cikin wata guda da ya gabata, na farko a matatar Fordow ta Iran, sannan a cibiyar Natanz.

    Sai dai Iran ta musanta cewa tana shirin kera makaman nukiliya.

  4. An kashe Falasɗinawa kusan 21,000 tun fara yaƙi a Gaza - Hamas

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya da ke karkashin ikon Hamas a Gaza, ta ce Falasɗinawa kusan 21,000 aka kashe tun soma yaƙi tsakaninsu da Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.

    Yayin da aka kashe fararen hula 240 a ranar Litinin kaɗai, wasu dubbai kuma sun jikkata sakamakon ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi a sansanonin 'yan gudun hijira.

    Shugaban sojin Isra'ila Laftanal Ƙanar Herzi Halevi, ya ce Isra'ila za ta ci gaba da kai hare-hare ta sama babu kakkautawa a yankunan Falasɗinawa.

    Ya ce sai sun kai ga shugabannin Hamas, ko da hakan zai ɗauki makonni ko watanni, saboda zukatansu na kan hakan sannan suna amfani da kwarewa a yaƙin.

  5. Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yari a Ogun

    Gidan yari

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yarin Ijebu Ode da ke jihar Ogun a kudancin Najeriya.

    Hukumomin gidan yarin sun tabbatar da tserewar fursunonin guda uku

    Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyara hali reshen jihar Ogun Victor Oyeleke ya fitar, ta ce fursunonin sun tsere ne ranar Asabar da tsakar dare.

    Fursunonin sun tsere ne ta hanyar tsallaka katanga.

    A cewar sanarwar, tuni aka shiga farautar fursunonin - hukumomin sun ce suna da bayanansu da kuma iyalansu, suna kuma aiki da sauran hukumomi domin dawo da su cikin gaggawa.

    Har ila yau, sanarwar ta ce ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere yana zaman gidan yarin ne kan hukuncin fashi da makami da aka yanke masa, ɗayan kuma an ɗaure shi a gidan yarin ne kan aikata kisa.

    Na ukun kuma yana zaman gidan yari kan aikata cin zarafi ta hanyar lalata.

    Tserewar furusnoni ko fasa gidajen yari ba sabon abu ba ne a Najeriya.

    Masana kuma na bayyana damuwa kan haɗarin da ke tattare da matsalar fasa gidajen yari wanda ke bayyana irin rikon sakainar kashi da ake yi wa gidajen yarin musamman a halin rashin tsaro da dukkan sassan ƙasar ke fuskanta.

  6. An samu fashewar wani abu a kusa da ofishin jakadancin Isra'ila a Delhi

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta tabbatar da fashewar wani abu a kusa da ofishin jakadancinta da ke New Delhi, babban birnin Indiya.

    Hukumomin ƙasar Indiya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron Isra'ila na bincike don gano abin da ya haddasa fashewar.

    Gidan talabijin na Channel 12 mallakin Isra'ila ya ce fashewar ta faru ne mitoci 50 daga ofishin jakadancinta a Delhi.

    Sai dai babu wanda ya jikkata a fashewar.

  7. Hare-haren Filato aikin mugaye ne abin alla-wadai - Gwamnonin Arewa

    Gwamnonin Arewa

    Asalin hoton, Gwamnonin Arewa

    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa 19 karkashin jagorancin gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai kan wasu al’ummomi a jihar Filato da suka yi sanadin mutuwar mutum sama da 100.

    Maharan dai sun kona gidaje da dama a daren Lahadi, da kuma yin awon gaba da kayan amfanin gona tare da lalata dukiyoyi.

    Wata sanarwa da aka fitar a madadin Gwamnonin Arewa, gwamna Yahaya ya yaba wa Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato bisa irin ƙoƙari da ya yi na ganin an nemo waɗanda suka kai harin cikin gaggawa domin su fuskanci hukunci.

    "Abin takaici ne da ɓacin-rai jin labarin rasa rayuka sama da 100 da kuma lalata dukiyoyi a wannan hari, musamman a lokacin da mutane ke murnar bukukuwan karshen shekara.

    "Wannan abin da maharan suka aikata ya saɓa wa zaman tare da kuma haɗin-kai muke ɗabbakawa a yankinmu, ba za mu lamunci afkuwar irin haka ba," in ji Inuwa Yahaya.

    Sanarwar gwamnonin ta kuma dole ne a ba da fifiko ga zaman lafiya a cikin al'ummominmu.

    Gwamnonin sun ce yanzu lokaci ne na jaddada zaman lafiya da haɗin kai ba tare da la’akari da bambance-bambance ba.

    Sun kuma yaba wa jami’an tsaro kan namijin ƙoƙari da suke yi wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da cewa dole ne a gaggauta kamo maharan.

  8. Sojin saman Najeriya sun lalata haramtattun wuraren tace mai shida a Fatakwal

    Sojin saman Najeriya

    Asalin hoton, NAF

    Hare-haren da jiragen rundunar Operation Delta Safe na sojin saman Najeriya sun lalata wasu haramtattun wuraren tace mai a Opu Arugbana da ke karamar hukumar Degema na jihar Ribas.

    Cikin sanarwar da rundunar sojin saman ta fitar, ta ce an kai harin ne a ranar 23 ga watan Disamba, 2023.

    "Mun gano haramtattun wuraren tace man ne a wani wuri mai nisan kilomita shida kudu da Opu Arugbana," in ji sanarwar.

    Sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama'a na rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta ce bayan gano wuraren shida ne sai suka lalata su, abin da ya karya lagon ɓata gari da ke tafiyar da wuraren.

    Gabkwet ya ce duk da yake ana cikin lokacin bukukuwa, amma hakan bai hana sojoji ci gaba da kai hare-hare ta sama kan masu aikata laifuka a yankin Neja-Delta da sauran sassan ƙasar nan ba.

    Shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, wanda ya shafe ranar Kirsimeti tare da sojoji a yankin Arewa maso Gabas, kuma a halin yanzu kuma ke jihar Katsina domin ganawa da dakarun Operation Hadarin Daji, ya yaba wa ƙoƙarin kwamandojin rundunar da irin jajircewarsu wajen yaƙi da ƴan 'ta'adda.

  9. Jirgin sama ya kai yaro ɗan shekara shida inda ba can zai je ba a Amurka

    Passenger jet

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Jirgin sama ya tashi da wani yaro ɗan shekara shida, ba tare da rakiyar wani nasa ba zuwa wani birni da ba can ya nufa ba, bayan an "ɗora shi bisa kuskure" a jirgiin saman kamfanin Spirit Airlines.

    Yaron mai suna Casper na tafiya ne daga birnin Philadelphia don ganin kakarsa da ke garin Fort Myers a jihar Florida.

    Amma sai ya tsinci kansa a birnin Orlando - tafiyar awa huɗu daga garin Fort Myers - bayan an ɗora shi cikin wani jirgin sama na daban.

    Kamfanin Spirit Airlines ya nemi afuwa kuma ya yi tayin mayarwa kakarsa kuɗin da ta kashe na tuƙa motar da ta je ta ɗauko Casper.

    Casper ya yi niyyar tashi daga filin jirgin saman ƙasashen duniya na Philadelphia zuwa filin jirgin saman ƙasashen duniya na Florida da ke kudu maso yamma a garin Fort Myers ranar Alhamis don ganin kakarsa, Maria Ramos.

    Sai dai a wani abu mai kama da shirin fim, sai aka ɗora Casper a wani jirgin sama da zai je Orlando, birnin da ke da nisan tafiyar kilomita 260 daga Fort Myers.

    Bayan jirgin da ya kamata a ce ya sauka a ciki ne amma ba ta ga jikanta ba, sai Misis Ramos ta shiga fargaba.

    "Sai na garzaya na shiga cikin jirgin inda na haɗu ma'aikaciyar jirgi inda na tambaye ta, 'Ina jikana? Ba an damƙa miki shi a Philadelphia ba?'" Misis Ramos ta faɗa wa tashar talbijin ta WINK-TV a Fort Myers.

    Ta ce ma'aikaciyar jirgin sai ta ce: "A'a, Ba mu taho da yara ba."

    An yi sa'a, Casper ya yi ƙoƙarin yi wa kakarsa waya jim kaɗan bayan ya sauka a Orlando. Misis Ramos daga nan ta tuƙa mota zuwa Orlando inda ta ɗauko jikan nata.

  10. Wasu hotuna na hare-haren Jajiberen Kirsimeti kan garuruwan Filato

    Bayanai suna ci gaba da fitowa game da hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai kan garuruwan Filato a ƙananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi da kuma Mangu tun daga ranar Jajiberen Kirsimeti.

    Ƙungiyar Amnesty International ta ce an kashe sama da mutum 140 a hare-haren, yayin da aka jikkata ƙarin ɗaruruwa.

    Wasu majiyoyin ma na cewa mutanen da aka kashe na kai wa 160.

    Hukumomi dai ba su tabbatar da alƙaluman ba zuwa yanzu.

    Baya ga kashe-kashen rayuka, ana zargin maharan da wawashe dukiyar al'umma tare da ƙona gidaje da motoci da sauran kadarori.

    Ga wasu hotuna na irin ɓarnar da aka yi a lokacin hare-haren:

    Plateau attack

    Asalin hoton, Amnesty International

    Plateau Attack

    Asalin hoton, Amnesty International

    Plateau Attack

    Asalin hoton, Amnesty International

    Plateau Attack

    Asalin hoton, Amnesty International

    Plateau Attack

    Asalin hoton, Amnesty International

  11. Babu sararawa a hare-haren Isra'ila ke kai wa Gaza - Jami'ar Majalisar Duniya

    Gaza war

    Asalin hoton, NURPHOTO VIA GETTY IMAGES

    Bayanan hoto, Mata a asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza na makoki game da mutuwar makusantansu a wani abu da Hamas ta ce wani harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Al-Maghazi ranar Lahadi ne ya yi sanadi

    Babu sararawa a hare-haren da Isra'ila ke kai wa ta sama, kamar yadda jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya ta shaida wa BBC bayan ta kai ziyara wani asibiti da ke faman kula da majinyata.

    Gemma Connell ta hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta faɗa wa BBC cewa abin da ta gani a asibitin Al-Aqsa na tsakiyar Zirin Gaza ranar Litinin "kisan mummuƙe ne kawai".

    Mutanen da suka ji tsananin raunuka ba sa iya samun kulawar likitoci saboda asibitin ya "cika ba masaka tsinke", in ji ta.

    Tun farko, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi alƙawarin zafafa yaƙi da Hamas.

    Ya ce ya kai ziyara Gaza a ranar Litinin da safe kuma aikin da sojojin Isra'ila ke yi a can bai "ko kusa zuwa ƙarshe ba".

    Kalamansa na zuwa ne kwanaki bayan Sakataren Wajen Amurka Anthony Blinken ya ce kamata ya yi Isra'ila ta rage tsananin hare-haren da take kai wa.

  12. Hukumar wanzar da zaman lafiya a Filato ta yi tir da kashe-kashen baya-bayan nan

    Hukumar wanzar da zaman llafiya ta jihar Filato ta yi alla-wadai da hare-haren jajiberen Kirsimeti a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi.

    Ta ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane yayin da wasu gommai suka ji raunuka.

    Jami'in da ke kula da harkoki a hukumar Mista Elkannah Izam ya ce hukumarsu ta yi matuƙar takaici kan hare-haren da ta ce an kai wa mutanen da ba su takali kowa da faɗa ba.

    Sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce babban abin takaicin shi ne hare-haren sun faru ne daidai lokacin da ake bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Kiristi wanda ta bayyana da Yariman Zaman Lafiya.

    Shugaban hukumar ya kuma hori jami'an tsaro su bi sawun maharan don ganin sun kamo su tare da gurfanar da su a gaban kotu.

  13. Tsohuwar ministar jin ƙai ta yi martani kan alaƙanta ta da 'mai halasta kuɗin haram'

    Former minister

    Asalin hoton, Sadiya Faruq Umar/X

    Tsohuwar ministar jin ƙai da kare aukuwar bala'i ta Najeriya, ta mayar da martani kan wasu rahotannin da ke cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC, ta kama wani ɗan kwangila da aka yi zargin ya halasta kuɗin haram har naira biliyan 37, a binciken da take yi.

    A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Sadiya Umar Farouq, ta ce rahotannin ba komai ba ne, face wani yunƙurin ɓata mata suna.

    A ranar Litinin ne jaridar Punch da wasu shafukan sada zumunta suka wallafa rahoton da cewa EFCC na ci gaba da bincike kan badaƙalar naira biliyan 37 da aka sauya wa ma'ajiya daga lalitar gwamnatin tarayya zuwa wasu asusu-asusu guda 38 masu alaƙa da ɗan kwangila James Okwete a bankunan kasuwanci.

    Jaridar ta ƙara da cewa an bankaɗo zargin halasta kuɗin haram ɗin ne a ma'aikatar harkokin jin ƙai.

    Sai dai tsohuwar ministar ta ce alaƙanta ɗan kwangilar da sunanta, ƙage ne kuma kwata-kwata ba ta san mutumin da ake magana kansa ba.

    A cewarta, "James Okwete bai taɓa yi min aiki ba, kuma bai taɓa wakilta ta ba, ta kowacce irin siga".

    Sadiya Farouq ta ce tuni ta tuntuɓi lauyoyinta don su lalubo zaɓin da take da shi na neman kadi a kan abin da ta kira "zargin nufaƙa da aka yi mata".

  14. Tinubu ya yi tir da harin Filato wanda aka kashe 'fiye da mutum 140'

  15. Ana neman wani uba bayan an gano gawar mata da 'ya'yanta huɗu a Faransa

    Police line

    Asalin hoton, Getty Images

    An ƙaddamar da bincike kan aikata kisan kai bayan an gano gawawwakin mutum biyar a wani gida da ke arewa maso gabashin birnin Paris.

    Mamatan sun haɗar da wata mace da 'ya'yanta huɗu kama daga ɗan wata tara zuwa mai shekara 10, kamar yadda masu shigar da ƙara suka ce.

    An gano gawawwakin nasu ne da maryacen Litinin a garin Meaux, mai nisan kilomita 40 daga babban birnin Paris.

    'Yan sanda na neman wani uba ɗan shekara 33, wanda ya "tsere". Dangin mamatan ne suka ankarar da hukumomi bayan sun kasa jin wani bayani daga 'yan'uwansu.

    Mai shigar da ƙara Jean-Baptiste Bladier ya tabbatarwa da kafofin yaɗa labaran Faransa cewa 'yan sandan Versailles na bincike a kan lamarin.

    Gidan bai nuna wata alama ta cewa an fasa an shiga ba daga waje, sannan kuma ba a ga mahaifin yaran ba, in ji shi.

  16. Rasha ta tabbatar da lalata mata jirgin yaƙi a Tekun Bahar Aswad

    Russian ship attack

    Asalin hoton, OLEKSANDR TRETYAK

    Bayanan hoto, Shugaban rundunar sojojin saman Ukraine ya wallafa hotunan da ba a tantance su ba, na harin da aka kai kan tashar ruwan Feodosiya

    Rasha ta tabbatar cewa ɗaya daga cikin jiragen ruwan yaƙinta ya lalace a Tekun Bahar Aswad yayin wani wani hari daga dakarun Ukraine.

    Harin ya faru ne a tashar ruwa ta Feodosiya a cikin yankin Crimea da ke ƙarƙashin mamayen Rasha cikin tsakiyar daren Litinin.

    Ma'aikatar harkokin tsaron ƙasar ta ce wani harin jirgin saman yaƙin Ukraine ɗauke da makamai masu linzami ya ritsa da wani babban jirgin ruwan Rasha mai suna Novocherkassk.

    Tun farko, shugaban rundunar sojin saman Ukraine ne ya ce jiragensu sun tarwatsa wani jirgin ruwan Rasha.

    An kashe mutum ɗaya a harin, in ji shugaban yankin Crimea wanda Rasha ta ɗora kan mulki, Sergei Aksyonov.

    Ya ƙara da cewa an lalata gine-gine guda shida kuma an kai adadin wasu mutane ƙalilan zuwa cibiyoyin tsugunnarwa da wucin gadi.

    An ce harkokin sufuri na gudana tashar ruwan kamar yadda aka saba bayan an killace yankin, a lokaci guda kuma an shawo kan gobarar da ta tashi sanadin harin.

    Kwamandan rundunar sojojin saman Ukraine, Laftanal Janar Mykola Oleshchuk ya wallafa hotunan da ke aka ce wai suna nuna harin, inda aka ga wata gagarumar fashewa a tashar.

  17. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa, barka da sake kasancewa da ku.

    Da fatan an wayi gari lafiya? Yaya bukukuwan Kirsimeti? Mukhtari Adamu Bawa ke muku fatan alheri.

    Allah ya kawo mana buɗi ta inda ba mu zata ba.

    Idan kun kasance da ni, zan kawo muku labarai da rahotanni a wannan shafi na kai tsaye daga sassa daban-daban na duniya.