Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Hamas da ƙungiyar Islamic Jihad sun ki amincewa da yarjejeniyar tsagaita yaki a Gaza'

    Kafafen yaɗa labaran Isra`ila da wasu ƙasashen Larabawa sun ce Hamas da ƙungiyar Islamic Jihad sun ki amincewa da wata yarjejeniyar kawo karshen yaƙi a Gaza, wanda ƙasar Masar ta yi musu tayin ta.

    Ƙungiyoyin sun ce ba su da niyyar sauraron wata tattaunawa face maganar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

    An ba da labarin cewa Masar ta gabatar da wannan kudurin yarjejeniyar dakatar da yaƙin ne a ranar Lahadi, wadda za a aiwatar da ita cikin zango uku.

    Cikin yanrjejeniyar har da maganar kafa gwamnatin da za ta mulki Gaza, wadda za ta kunshi kwararru daga ɓangaren mahukunta a Faladinu da kuma Gaza.

    Wani ɗan ɓangaren masu tsattsauran ra'ayi a Isra`ila, Bezalel Smotrich shi ma ya yi watsi da yarjejeniyar, inda ya ce majalisar da ke kula da yaƙi ta Isra'ila ba ta da hurumin amincewa da kudurin.

  3. Sakon Kirsimeti: Sarki Charles na III ya jaddada muhimmancin martaba al'adu

    Sarki Charles na III

    Sarki Charles na III ya jaddada muhimmancin martaba al`adu da ka'idojin da manyan addinai suka yi tarayya a kan su, a wannan lokacin da rikice-rikice ke kara yawa a faɗin duniya.

    Sarkin ya faɗi haka ne a jawabinsa na murnar bikin Kirsimeti.

    Jawabinsa ya kuma taɓo batun muhalli, inda ya gode wa ɗukacin masu mayar da hankali wajen kyautata duniyar da muke ciki.

    Ya ce babu addinin da ba ya martaba dukkan halittar Allah.

    Sarki Charles dai ya daɗe yana goyon bayan yaukaka dangantaka da zumunci a tsakanin al`ummomi mabiya addinai daban-daban a Ingila da kuma ƙasashen waje.

  4. Yadda aka gudanar da bikin Kirsimeti a Nijar, Daga Tchima Illa Issoufou

    Mabiya addinin Kirista a Jamhuriyar Nijar sun bi sahun takwarorinsu na sauran ƙasashen duniya wajen gudanar da shagulgulan bikin Kirsimeti.

    Kirsimeti dai lokacin ne na tunawa da haifuwar Yesu Almasihu.

    Ga rahoton da Tchima Illa Issoufou daga Yamai.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
  5. Netanyahu ya yi alkawarin ƙara tsananta yaƙi a Gaza

    Yaƙi

    Asalin hoton, OFFICE OF ISRAELI PM

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin cewa zai ƙara tsananta yaƙi kan Hamas cikin kwanaki masu zuwa.

    Ya faɗa wa mambobin jam'iyyarsa cewa ya kai ziyara Gaza a ranar Litinin da safe kuma aikin sojojin ƙasar a can bai kusa ƙarewa ba.

    Kalamansa na zuwa kwanaki bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka ya buƙaci Isra'ila ta sassauta hare-hare da take kai wa Gaza.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon Hamas ta bayyana a ranar Litinin cewa an kashe wasu Falasɗinawa 20,674 a ci gaba da lugudan wuta da Isra'ila ke yi. Ta ce yawancin waɗanda al'amarin ya rutsa da su mata ne da ƙananan yara.

    An kashe wasu 1,200, yawanci fararen hula lokacin da mayakan Hamas suka kaddamar da hari a faɗin iyakar Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba. Kusan 240 aka yi garkuwa da su zuwa Gaza.

    Isra'ila ta ce har yanzu akwai sauran mutum 132 waɗanda Hamas ke rike da su.

    Mista Netanyahu ya ci alwashin tarwasa Hamas da kuma mayar da mutanen da ke hannuta zuwa gida.

  6. Labarai da dumi-dumi, An kashe mutum sama da 70 a wani ƙauyen jihar Filato

    Caleb Muftawang

    Asalin hoton, Governor Plateau State

    An kashe mutum akalla 76 a wani hari da aka kai cikin jihar Filato, da ke tsakiyar Najeriya.

    Mai magana da yawun gwamnatin jihar Gyang Bere, shi ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.

    Ya ce gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya bayar da umarnin kama waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

    Gwamnan ya kuma shawarci jama’a da kwantar da hankali tare da sanar da hukumomin tsaro dukkan wani abu da ba su gamsu da shi ba.

    Kananan hukumomin da hare-haren suka shfa sun haɗa da Bokkos da kuma Barikin Ladi da ke jihar ta Filato.

    Sai dai rahotanni na cewa alkalumman waɗanda suka rasa rayukansu na iya karuwa kasancewar hukumomin tsaro da haɗin gwiwar ƴan sa kai da kuma mafarauta da suka bazama a cikin daji, na ci gaba da gano ƙarin wasu gawawwaki.

    Wani tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Filato Bala Fwanje wanda ya fito daga yankin da lamarin ya faru, ya shaida wa BBC cewa sabon farmakin yana da ban tsoro duba da cewa ba Barikin Ladi ko Bokkos ne kaɗai ke fuskantar barazana ba, inda ya ce har da wasu kauyuka da ke faɗin jihar.

    Hukumomi sun ce kawo yanzu ba a san waɗanda suka kai sabon harin ba da kuma musabbabin yin haka.

    A baya dai jihar Filato ta fuskanci rikice-rikice masu alaka da kabilanci, da kuma tsakanin manoma da makiyaya.

  7. An yi jana'izar mutum takwas da ƴan bindiga suka kashe a Katsina

    Katsina

    An yi jana'izar mutum takwas da ƴan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai karamar hukumar Jibia na jihar Katsina.

    Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutum huɗu sun jikkata, sannan ba a ga guda wasu biyu ba a harin da aka kai a ranar Lahadi da dare

    Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƴan bindigar sun zo da yawa inda suka far wa mutanen waɗanda ke kan hanyarsu ta komawa gida daga kauyen Kukar Babangida zuwa Ƴan Gayya.

    Mutumin ya bayyana cewa waɗanda aka kashe ba su haura shekaru 22 zuwa 47 kuma dukkansu ‘yan kauyen Yan Gayya ne.

    Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

    Jibia dai na kan iyakar Najeriya da Nijar. Karamar hukumar ta kuma yi iyaka da kananan hukumomin Batsari, Kaita, Katsina, Batagarawa da kuma Zurmi.

    Katsina
  8. Shugaban Hamas ya ce suna fafata ƙazamin yaƙin da ba su taɓa ganin irinsa ba

    Yahya Sinwar

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Hamas a Zirin Gaza, Yahya Sinwar a wani jawabinsa na farko a bainar jama`a da ya gabatar, tun lokacin da hamas ta kai wa Isra`ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, ya ce ƙungiyarsa na gwabza mummunan faɗan da ba ta taɓa yin irinsa ba.

    Cikin wata wasiƙar da ya aike wa sashen da ke kula harkokin siyasa na ƙungiyar, Yahya Sinwar ya yi bayani dalla-dalla a kan yaƙin da Hamas ke yi da Isra'ila a Gaza, inda ya ce yanzu Hamas ta yanke shawarar shiga yakin sunkuru ko sari-ka-noke.

    Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce Yahya Sinwar ya rubuta wannan wasikar ne domin ya tabbatar wa duniya cewa yana raye.

  9. An yi kira ga Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a Najeriya

    Bishop Kukah

    Asalin hoton, KUKAH CENTRE/X

    Bishop na ɗariƙar Katolika ta Sokoto Rabaran Mathew Kukah, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya lalubo hanyar da za ta kai ga ƙarshen kashe-kashen da ake yi wa 'yan Najeriya bisa kowanne irin dalilai.

    Kukah, a cikin saƙon ranar Kirsimetinsa mai taken: “Lokacin Sake Mayar da Najeriya Ƙasaitacciya,” kuma aka raba wa manema labarai ranar Litinin, ya ce dole ne shugaban Najeriya ya yi amfani da ɗumbin gogewarsa wajen kawo ƙarshen muguntar da ake aikatawa da sunan addini da ƙabilanci da kuma ɓangare.

    Ya kuma yi bayani game da zaɓukan 2023 da abubuwan da suka biyo bayansu game da ƙasar ya zuwa yanzu, inda ya yi kira ga shugabanni a kowanne ɓangare, da cikin gaggawa su samo hanyar tausar zukata.

    Fitaccen malamin addinin Kiristan ya ce wannan aiki ba mai sauƙi ba ne ga kowacce ƙasa, kuma ba a yi wa aikin gina ƙasa ratse.

    A cewarsa, 'yan shekaru ƙalilan da suka gabata, Najeriya ta fuskanci jarrabawa a matsayinta na ƙasa dunƙulalliya, kuma yanzu wajibi ne gwamnati ta ɓullo da dabaru da hanyoyin sulhuntawa, waɗanda suka kuɓuce wa Najeriya, in ji shi.

  10. Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa

    Nijar ta dakatar da dukkan ayyukan haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa da ake kira (OIF) a taƙaice, a cewar shugabannin mulkin sojin ƙasar, yayin da take ƙara janye jiki daga tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakarta.

    Ƙungiyar mai wakilai 88 "a ko da yaushe Faransa na amfani da ita a matsayin wani makami wajen kare muradan Faransa", a cewar wani mai magana da yawun shugabannin mulkin sojin kamar yadda ya bayyana a wani jawabi ta kafar talbijin ɗin ƙasar ranar Lahadi.

    Tun cikin makon jiya ne, ƙungiyar ta OIF ta dakatar da mafi yawan ayyukan haɗin gwiwa da Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, sai dai ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da harkokin da "kai tsaye za su amfani fararen hula da kuma waɗanda za su tallafa wajen mayar da Nijar kan mulkin dimokraɗiyya".

    Taken da ƙungiyar ke bayyanawa shi ne bunƙasa harshen Faransanci da tallafawa harkokin zaman lafiya da dimokraɗiyya da ƙarfafa gwiwar haɓaka ilmi da raya ƙasa a ƙasashe rainon Faransa a faɗin duniya, waɗanda da yawansu tsoffin ƙasashen Faransa ta yi wa mulkin mallaka ne.

  11. Ana bikin Kirsimeti karon farko ranar 25 ga watan Disamba a Ukraine

    Ukraine soldiers

    Asalin hoton, Reuters

    Da yawan Kiristoci 'yan gargajiya a Ukraine na gudanar da bikin Kirsimeti karon farko a ranar 25 ga watan Disamban wannan shekara.

    Tun tale-tale al'ummar Ukraine na amfani da kalandar Juliyan wadda ake aiki da ita a Rasha wajen gudanar da bikin Kirsimeti da kan faɗo ranar 7 ga watan Janairu.

    Cikin wani al'amari da ke nuna ƙara nisanta daga Rasha, a yanzu al'ummar ƙasar na bikin Kirsimeti daidai da Ƙasashen Yamma - masu amfani da kalandar Bature.

    Christmas Service

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Kiristoci da suka yi imani da tsarin addinin na gargajiya na halartar wani taron addu'o'i a ranar Jajiberen Kirsimeti a Majami'ar St Michael Mai tulluwar Zinare a birnin Kyiv

    A watan Yuli ne Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya canza dokar, inda ya ce za ta bai wa al'ummar ƙasar damar "yin biris da al'adu gadon Rasha" da ke koyar da bikin Kirsimeti a watan Janairu.

    A wani saƙon Kirsimeti da ya fitar ranar Lahadi da maryace, Mista Zelensky ya ce dukkan al'ummar Ukraine a yanzu kansu ya haɗu.

    "Duka muna bikin Kirsimeti tare. A rana ɗaya, a matsayinmu na dangi ɗaya, 'yan ƙasa ɗaya kuma al'ummar ƙasa dunƙulalliya ɗaya."

    A Kyiv babban birnin ƙasar, wasu ma'aurata Lesia Shestakova, mai bin ɗariƙar Katolika da Oleksandr Shestakov, wanda mai bin ɗariƙar 'Yan gargajiya ne, na bikin Kirsimeti tare.

    Church hall

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Nan cikin Majami'ar St Alexander ne

    Ma'auratan waɗanda kafin yanzu, suke bikin Kirsimeti sau biyu, tare da iyayen kowannensu, sun halarci taron ibadar safe a Cocin Katolika da ke birnin (ga hotonsu nan a sama).

    Al'ummar Ukraine sun yi taron addu'o'i tare da kunna kyadira a faɗin ƙasar ranar Lahadi.

    A birnin Lviv na yammacin ƙasar, wanda yaƙi ya ɗan lalata, ƙananan yara a cikin tufafin al'ada ne suka rera waƙoƙin Kirsimeti sannan sun shiga cikin jerin gwanon bukukuwan ranar a kan tituna.

    Children celebrate Christmas

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan Ukraine na caɓa wa bishiyar Kirsimeti ado a kusa da Dandalin Samun 'Yanci a Kyiv

    Christmas service

    Asalin hoton, EPA

    Sai dai tabbas, ana tsammanin har yanzu akwai 'yan Ukraine ƙalilan da za su yi bikin Kirsimeti sau biyu - ko ba komai, kogi ba ya ƙin daɗi.

    Duk hotuna suna da haƙƙin mallaka.

  12. Ƙazafi ake min, ban buɗe asusun banki 593 a ƙasashen waje ba - Godwin Emefiele

    Emefiele

    Asalin hoton, Central Bank of Nigeria

    Bayanan hoto, Godwin Emefiele

    Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya musanta zarge-zargen satar dukiyar ƙasa da ake yi masa a wani rahoton Mai Bincike na Musamman kan harkokin bankin CBN da aka fitar a baya-bayan nan.

    Ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Re: Emefiele, others stole billions, illegally kept Nigeria’s funds in foreign banks’ da ya fitar ranar Lahadi.

    Idan za ku iya tunawa a cikin makon jiya ne, Mai Bincike na Musamman kan harkokin Babban Bankin Najeriya, Jim Obaze, ya bankaɗo cewa tsohon gwamnan bankin ya jibge fam miliyan 543, 482,213 ba tare da izini ba a bankunan Birtaniya kawai.

    Wani ɓangare na rahoton Jim Obaze a cewar jaridar Daily Post ta intanet, “Tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya jibge kuɗaɗen Najeriya ba tare da izini ba a asusun ajiya 593 na bankunan ƙasashen waje a Amurka da China da Birtaniya, lokacin da yake mulki.

    Sai dai Godwin Emefiele a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce, bayan sakin sa a matakin beli daga gidan yarin Kuje, hankalinsa ya kai kan wasu labarai masu alaƙa da rahoton Jim Obaze.

    “Na karanta labaran, kuma da ƙarfin murya ina cewa abin da suka ƙunsa, ƙarairayi ne da karkatar da hankali da kuma maƙarƙashiya don a ɓata min suna, a ci mini zarafi sannan da biyan muradin mai binciken.”

    Ya kuma ce ba shi da hannu a buɗe asusun ajiya 593 a sassan duniya, kuma bai ma san an buɗe su ba.

    Sai dai ya ce akwai sashe-sashe na babban bankin da ke da iko su aiwatar da irin waɗannan harkoki kamar yadda doka ta amince musu bisa tanade-tanaden aikin CBN.

    Don haka, a cewar Emefiele "Ni ma kamar sauran 'yan Najeriya masu kyakkyawar niyya da suka yi magana kan wannan batu, ina neman a gudanar da cikakken bincike kuma a fayyace komai a faifai game da waɗannan zarge-zarge na almundahana".

    Ya kuma ce ya umarci lauyoyinsa, su hanzarta ɗaukan matakan shari'a don wanke sunansa daga kalaman ɓata-suna da ke ƙunshe a cikin rahoton da kuma labaran da suka wallafa shi.

    • Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele
    • Emefiele ya fara shugabancin CBN
  13. Rundunar 'yan ci-rani 'masu gudun talauci' ta durfafi Amurka

    Migrants

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, 'Yan ci-rani na tafiya a lokacin da suke barin Tapachula a wani babban ayari da ke ƙoƙarin kai wa iyakar Amurka

    Wata rundunar 'yan ci-rani daga ƙasashen tsakiya da na kudancin Amurka ta ɗauki hanya ta cikin Mexico inda ta nufi arewa zuwa kan iyakar Amurka.

    Sama da mutum 8,000 ne masu shekaru daban-daban, akasari daga Venezuela da Cuba da kuma Mexico ne suka shiga jerin gwanon inda suka riƙe wani ƙyalle mai ɗauke da rubutu "Kwararar Talauci".

    Lamarin na zuwa ne kwanaki ƙalilan kafin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya fara wata ziyara a birnin Mexico City.

    Mista Blinken na fatan cimma sabbin yarjeniyoyi a kan taƙaita kwarar baƙin haure.

    Yawan 'yan ci-ranin da aka kama a kan iyakar kudancin Amurka ya zarce miliyan biyu a shekara ta 2022 da kuma 2023.

    A watan Satumban 2023 kaɗai, Jami'an Sintirin kan Iyakar Amurka sun kama 'yan ci-rani sama da 200,000 da suka tsallaka iyakar Mexico da Amurka ba bisa ƙa'ida ba, a cewar ƙididdigar Hukumar Tsaron Ƙasa a Amurka.

    Rundunar 'yan ci-rani ta ranar Jajiberen Kirsimeti ta tashi ne daga binin Tapachula na kudancin Mexico, a kusa da kan iyakar ƙasar da Guatemala.

    Wani ɗan ƙasar Honduras da ya shiga cikin jerin gwanon 'yan ci-ranin ya ce ya arce daga ƙasarsa ne don kuɓuta daga rikicin gungun 'yan daba da ke barazanar kashe shi.

    Caravan

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Rundunar Jajiberen Kirsimeti na tafiya ne a bayan wani ƙyalle mai rubutun "Kwararar Talauci" da harshen Sifaniya

    José Santos ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Ina jin tsoro don haka na yanke shawarar tafiya Mexico da fatan za a bar mu, mu shiga Amurka."

    A ranar Juma'a, Shugaba Ƙasar Mexico Andrés Manuel López Obrador ya ce yana son ya sake yin aiki tare da Amurka don magance damuwar da ake da ita game da kwararar 'yan ci-rani.

    A ranar Laraba ne shugaban na Mexico zai gana da sakataren wajen Amurka.

    • 'Yadda matasan Tunisiya suka sa min wuƙa a maƙogoro'
    • Yadda matsalar ci-rani ke janyo mace-macen aure a Nijar
  14. An kashe mutum 16 a wani ƙauyen jihar Filato

    An kashe mutum 16 a wani hari da aka kai cikin jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, inda rikici tsakanin makiyaya da manoma ya zama ruwan dare.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata majiyar tsaro a ƙasar na cewa an kai harin ne a ƙauyen Mushu., wanda ke kan iyaka tsakanin ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos.

    Wasu bayanan sun ce an hallaka mutanen ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka yi wa ƙauyen zobe.

    • Shin an fara samun nasarar kakkaɓe ƴan bindiga a Najeriya?
    • Me ya sa hare-haren 'yan fashin daji ke dawowa a Najeriya?
  15. Ga wasu hotunan bikin Kirsimeti daga sassan duniya

    Christmas service

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A fadar Vatican, Fafaroma Francis ya jagoranci taron addu'o'in tsakar dare a ranar jajiberen Kirsimeti a Majami'ar St Peter
    Christmas service

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masu ibada na Cocin Legio Maria African Church Mission, su ma sun taru don addu'o'in tsakar dare, a lokacin jajiberen Kirsimeti a kusa da Ugunja, Kenya
    Chrismas day

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Masu wasan sulu a kan ruwa a Gabar Tekun Bondi cikin birnin Sydney sanye da tufafin biki irin na lokacin Kirsimeti
    Christmas day

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Dakarun sojojin Ukraine sun halarci bikin Kirsimeti, yayin da ake fuskantar hare-haren Rasha kan Ukrraine a Lviv
    • Albarkar da Yesu Almasihu ya kawo wa Duniya
    • Liverpool ta kai iyalan Diaz cikin birni don yin bikin Kirsimeti
  16. Bidiyon yadda aka garzaya da wasu asibiti bayan harin da ya halaka mutum 70 a Gaza

    Bayanan bidiyo, Isra'ila da Gaza: Aƙalla mutum 70 ake ba da rahoton cewa sun mutu a harin da Isra'ila ta kai ta sama kan wani sansanin 'yan gudun hijira a Gaza
  17. An kashe mutum 70 a wani hari ta sama a Gaza

    Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce wani harin Isra'ila ta smaa ya yi sanadin kashe aƙalla mutum 70 a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Zirin.

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar ya ce adadin waɗanda suka mutun mai yiwuwa ne zai ƙaru, bisa la'akari da ɗumbin iyalan da ke rayuwa a yankin.

    Rundunar sojojin Isra'ila ta faɗa wa BBC cewa tana nazari kan rahotannin hari ta saman da ake ambatowa.

    Lamarin na zuwa ne bayan kafofin yaɗa labaran Larabawa da na Isra'ila sun ce ƙasar Masar wadda ta yi iyaka da Zirin Gaza, ta gabatar da wani sabon ƙuduri don neman tsagaita wuta a tsakanin Isra'ila da Hamas.

    • Kalli yadda aka yi kaca-kaca da Gaza
    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
  18. Sallama

    Jama'a barkanmu da sake kasancewa da ku a yau Litinin.

    Daga nan Sashen Hausa na BBC, muna taya al'ummar Kirista barka da bikin Kirsimeti.

    Da fatan za a yi shagulgula lafiya. Kuma kamar kullum za mu kawo muku rahotanni da labarai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta da ma sauran sassan duniya.

    Ni ne naku, Mukhtari Adamu Bawa