Hamas ta saki uwa da ƴarta da ta yi garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku wasu sababbi gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Bawa ne ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Hoto na farko na Amurkawa da aka sake

    Ga hoto na farko da muka samu na Judith da Natalie Raanan, bayan sako su da Hamas ta yi.

    Gwamnatin Isra'ila ce ta fitar da hoton.

    Government of Israel

    Asalin hoton, Government of Israel

  3. Ba za iya fayyace irin shiga tsakani da Qatar ta yi ba wajen sako Amurkawa biyu

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya yi jawabi game da shiga tsakanin Qatar wajen sako wasu Amurkawa biyu da aka yi garkuwa da su.

    "Ina so in gode wa gwamnatin Qatar saboda taimakon da ta bayar," in ji shi, amma kuma ya ce "ba zai iya magana a fili ba" ko bayar da ƙarin bayani kan sako Amurkawan.

    "Amma ana ci gaba da gudanar da aikin gaggawa na kuɓutar da kowane Ba'amurke da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, da samar da hanyar sauki wajen fita daga Gaza," in ji Blinken.

    Ya yi kira da a gaggauta sakin duk waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Sanarwar ta karshe na magana ne kan abin da Hamas ta ce idan aka daina kai hare-hare ta sama, to za a sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

  4. Gwamnatin Najeriya za ta gina rukunin gidaje 34,500 a faɗin ƙasar

    Rukunin gidaje

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan gidaje da raya birane, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rukunin gidaje kusan 34,500 a faɗin ƙasa, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin bunƙasa al'ummomi masu ayyukan haɗin gwiwa a Najeriya.

    Arc. Dangiwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranar Alhamis.

    Ya ce biranen da za a gina za su kasance cikin matakai, inda a mataki na farko, ake da niyyar ginda rukunin gidaje 34,500 a cikin jihohi talatin 30 na ƙasar.

    Ya ce gidajen za su kuma kasance cikin rahusa domin mutane su samu damar mallaka.

    Ministan ya ce don yin haka, ma’aikatar za ta yi da aiki da bankin bayar da rancen gina gidaje na Najeriya (FMBN) don bai wa masu cin gajiyar damar samun rancen gidajen a cikin rahusa, wanda za su iya biya cikin shekaru 30.

    Ya kara da cewa "Muna shirin haɗa gwiwa da masu ci gaban kamfanoni masu zaman kansu don sayar da manyan gine-ginen a farashin kasuwa domin mu yi amfani da ribar da za a samu wajen rage farashin gidajen don masu karamin ƙarfi."

    Minista ya ce don cimma hakan, ma’aikatar za ta buƙaci goyon bayan gwamnonin jihohi wajen samun fili kyauta a matsayin gudunmawarsu ga shirye-shiryen gwamnati na gina gidaje masu sauki ga kowane ɓangare na al’umma.

  5. Masu harkar canjin kuɗi na kokawa kan faɗuwar darajar Naira, Daga AbdusSalam Ibrahim Ahmed

    Masu harkar canjin kuɗaɗen waje a Najeriya, suna bayyana damuwa game da yadda darajar kuɗin ƙasar wato Naira ke ci gaba da faɗuwa, yayin da farashin dala ke ƙara hauhauwa.

    Sun ce ba su taɓa ganin irin wannan hauhauwa a cikin shekaru 40 da suka gabata ba, inda a ranar Alhamis farashin dalar ya kai 1,100.

    Bayanai daga Babban Bankin Ƙasar, wato CBN, sun nuna cewa nairar ta faɗi daga 883.56 zuwa 775.44 kowacce dala a ranar Laraba.

    Yusuf Nabahani, tsohon shugaban kungiyar masu canji a Kano, ya ce ba sa jin daɗin yanda kasuwar take a yanzu saboda, inda ya ce lamarin ya tilasta musu samun ƙarancin masu zuwa yin canji.

    Ga rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron rahoton
  6. Ministan Faransa Darmanin na musayar yawu da Karim Benzema a kan rikicin Gaza

    Karim Benzema

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Tsohon dan kwallon Faransa na yana barazanar gurfanar da Gérald Darmanin a gaban kotu, bayan ya zarge shi da alakanta shi da masu ikirarin jihadi

    Ɗan kwallon Faransa Karim Benzema ya yi barazanar garzaya wa kotu bayan ministan cikin gidan kasar, Gérald Darmanin ya zarge shi da alaƙa da ƙungiyar masu ikirarin jihadi ta 'Yan'uwa Musulmi.

    Ministan yana mayar da martani ne ga kalaman da Benzema ya yi a shafin X, inda ya yi wa al'ummar Gaza addu'a a matsayin "waɗanda suke sake fuskantar hare-haren bama-bamai na rashin adalci waɗanda ba su bar mata ko yara ba".

    Nunar da gazawarsa ta bayyana irin wannan alhini ga 'yan Isra'ila kimanin 1,400 da Hamas ta hallaka, Mista Darmanin ya ce tsohon dan kwallon gaban na Faransa "sananne ne a kan alakarsa da kungiyar Muslim Brotherhood".

    "Muna yaki da matsattsaku ne wadda ake kira Muslim Brotherhood, saboda tana haifar da wani yanayi na akidar jihadi," ya fada wa tashar talbijin ta CNews.

    Dan kwallon kafan wanda yanzu yake zaune a kasar Saudiyya inda ya buga gasar Saudi Pro League, ya bai wa lauyansa na birnin Paris izini ya fitar da sanarwar da ke musanta wannan ikirari karara - kuma ya yi barazanar daukar matakin shari'a a kan Gerald Darmanin saboda bata-suna.

    "Karim Benzema bai taba yin wata dangantaka ko yaya take ba da wannan kungiya (da minista Darmanin ya yi ikirari)," a cewar Hugues Vigier.

    "Addu'a ga fararen hula da ke rayuwa a cikin luguden ruwan bama-bamai… ba farfaganda nake yi wa Hamas ba, ba kuma hada baki nake yi da wasu don a aikata ta'addanci ba, babu wata hadaka.

    "Dabi'a ce ta dan'adam ya nuna tausayawa idan akwai abin da mutane da yawa ke cewa aikata laifukan yaki ne… wanda kuma ko kadan bai rage munin ta'addancin da [Hamas] ta aikata ranar 7 ga watan Oktoba ba," in ji shi.

  7. Biden 'ya yi matukar farin ciki' da sakin Amurkawa biyu da aka yi garkuwa da su

    Joe Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya fitar da wata sanarwa a matsayin martani ga sakin Amurkawa biyu Judith da Natalie Raanan, yana mai cewa "ya yi matukar farin ciki", inda ya ce nan ba da jimawa ba za su sake haɗuwa da iyalansu.

    Ya ce 'yan ƙasar Amurka da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su tun ranar 7 ga watan Oktoba "sun jure mummunan bala'i a cikin kwanaki 14 da suka gabata".

    Ya ƙara da cewa za su sami cikakken goyon bayan gwamnatin Amurka yayin da suke ci gaba da murmurewa.

    Biden ya gode wa gwamnatocin ƙasashen Qatar da Isra'ila bisa aiki tare da suka yi wajen ganin an sako Amurkawan, ya kuma ce gwamnatinsa tana aiki ba dare ba rana domin kuɓutar da 'yan ƙasar da Hamas ta yi garkuwa da su.

    "A matsayina na shugaban ƙasa, ba ni da fifiko da ya wuce kare lafiyar Amurkawa da aka yi garkuwa da su a faɗin duniya."

  8. Korar kararrakin zaɓe 900 da kotu ta yi ya nuna cewa mun gudanar da sahihin zaɓe - INEC, Daga Zubairu Ahmad Kasarawa

    Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, ta bayyana cewa kotu ta yi watsi da kararrakin zaɓe 900 daga cikin 1200 da aka shigar kan zaɓukan wannan shekara.

    INEC ta ce hakan ya nuna cewa ta samu nasara gudanar da sahihan zaɓukan da suka gabata da aƙalla kashi 74 cikin 100.

    Ga rahoton Zubairu Ahmad Kasarawa.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
  9. MDD ta yi kiran kai agaji da gaggawa zuwa Gaza

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Reuters

    Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ziyarci iyakar Rafah ta Masar tare da yin kira da a ba da izinin shigar da manyan motocin agaji zuwa cikin yankin Falasɗinawa cikin gaggawa.

    Antonio Guterres ya ce "dole ne rai ya ɓaci ganin dogayen layukan motocin dakon kaya a kan iyakar.

    Masar ta ce ta buɗe iyakar daga ɓangaren ta kuma ba ta hana komai wucewa ba.

    An sa ran cewa ayarin motoci na farko za su wuce zuwa Gaza ranar Juma'a bayan da Mista Biden ya yi alkawarin cewa za a bar kayan agaji su wuce yayin ziyarar da ya kai Isra'ila a wannan makon.

  10. Afcon 2023: Golan da koci Jose Peseiro ke karewa daga masu suka

  11. Labarai da dumi-dumi, Jami'an Isra'ila sun tabbatar da sakin Amurkawa biyu da aka yi garkuwa da su

    Jami'ai a Isra'ila sun tabbatarwa BBC cewa Hamas ta saki mata Amurkawa guda biyu, Judith da kuma Natalie Raanan.

    Hamas ta yi garkuwa da matar da kuma ƴarta ne a Kibbutz Nahal Oz, da ke kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

  12. Tinubu ya naɗa sabon Babban mai Binciken Kuɗi na Ƙasa

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Twitter

    Shugaba Bola Tinubu ya amince naɗin Mr. Shaakaa Chira, a matsayin sabon Babban mai Binciken Kuɗi na Ƙasa.

    Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Ajuri Ngelale ya fitar yau Juma'a a Abuja.

    Tinubu ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da Hukumar Kula da Ma'aikatan Tarayya tayi, inda ta kuma fito da sunan Mr Chira bayan samun maki da ya fi na wadanda aka tantance.

  13. Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa ƴan mata riga-kafin cutar kansar mahaifa

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara yi wa 'yan mata riga-kafin kwayar cutar HPV mai haddasa kansar mahaifa a makon gobe.

    Ministan Lafiya da ci gaban al'umma na ƙasar Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya sanar da hakan a wata hira da BBC.

    Manufar hakan dai ita ce ceto miliyoyin 'yan mata a ƙasar daga kamuwa da cutar ta kansar mahaifa.

    Ga ƙarin bayanin da ya yi wa Haruna Shehu Tangaza.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron tattaunawar
  14. Tinubu ya ba da umarni a biya malaman jami'a albashi na watannin yajin aiki

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Twitter

    Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin biyan malaman Jami'a ta ASUU albashinsu da aka riƙe lokacin da suke yajin aiki.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma'a, ta ce Tinubu ya kuma jingine batun manufar gwamnati ta ba aiki ba biya da gwamnati tayi kan malaman bayan tsunduma yajin aiki da suka yi na tsawon wata takwas daga 14 ga watan Febrairun 2022 zuwa 17 ga Oktoban 2022.

    Sanarwar ta ce shugaban ya yi haka ne domin nuna jin-kai ga malaman.

    “A yunƙurinsa na rage matsalolin da ake fuskanta a lokacin aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar nan, tare da amincewa da aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya, Tinubu ya bayar da umarnin jingine batun ba aiki ba biya, wanda zai bai wa ‘yan ƙungiyar ASUU damar karɓar albashin watanni huɗu daga cikin takwas," in ji sanarwar.

  15. Labarai da dumi-dumi, Rahotanni na cewa Hamas ta saki Amurkawa biyu da ta yi garkuwa da su

    Kafofin yada labaran Isra'ila na ba da rahoton cewa Hamas ta saki 'yan Amurka biyu da take rike da su a Gaza.

    Zuwa yanzu babu wani tabbaci da aka samu game da wannan. Muna jira mu ji daga jami'an Isra'ila da kuma na Amurka.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka na shirin gudanar da taron manema labarai da ta saba yi kullum a birnin Washington

  16. Firaministan Birtaniya ya gana da Shugaban Falasdinawa

    Mun samu labarin cewa Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas yayin ziyara da ya kai Masar a yau Juma'a.

    Ofishin Sunak ya ce Firaministan ya miƙa ta'aziyyarsa ga waɗanda suka rasa ƴan uwansu a Gaza, inda ya nanata buƙatar ganin an buɗe hanyar kai kayan agaji zuwa Gaza.

    Dukka shugabannin sun yi Alla-wadai da harin Hamas, inda suka ce Hamas ba ta wakiltar al'ummar Falasɗinawa.

    Mai magana da yawun Sunak ya ce: "shugabannin sun amince cewa dukka ɓangarorin su ɗauki matakan kare fararen hula da kuma gine-ginensu, da guje wa asarar rayuka.

  17. Hotuna: Yadda al'amura suke a Zirin Gaza bayan yakin kwana 14

    Zirin Gaza ya shaida matsalolin jin kai masu yawa game da yakin da ya shiga kwana na 14, wanda muka haska a cikin wadannan hotuna:

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An ci gaba da luguden wuta a kudancin Zirin Gaza inda hukumomin kai daukin gaggawa na Falasdinawa da mazauna yankin ke neman wadanda aka ritsa da su a gine-ginen da hare-haren Isra'ila ta sama suka ruguza.
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Al'ummar Gaza na ci gaba da yin kaura zuwa kudu, bisa umarnin tayar da mutanen arewaci da sojojin Isra'ila suka fitar kafin harin kasa da ake tsammanin Isra'ila za ta kaddamar.
    h

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani Bafalasdine yana kiran sallah a kusa da baraguzan Masallacin Al-Amin Muhammad, wanda Isra'ila ta jefa wa bam a Khan Yunis.
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Falasdinawa sun gudanar da Sallar Juma'a a wani filin makaranta ta Hukumar kula da Falasdinawa 'Yan gudun hijira da ba da agaji ta majalisar Dinkin Duniya a Deir al-Balah, cikin tsakiyar Zirin Gaza
    h

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Harkokin lafiya a Gaza na cikin mawuyacin hali sanadin matsanancin karancin kayayyakin asibiti da jami'an lafiya, yayin da gomman wadanda suka jikkata ke zuwa asibitoci a kullum sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi ta sama tsawon kwana 14 a jere.
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Falasdinawa na ajiye gawawwakin danginsu kafin yi musu jana'iza a asibitin Al-Najjar da ke Rafah a kudancin Zirin Gaza.
  18. Labarai da dumi-dumi, Hukumomin Falasɗinawa sun ce mutanen da suka mutu a Gaza sun kai 4,000

    Ma'aikatar lafiya a Falasɗinu ta ce alkaluma waɗanda suka mutu a Gaza sun kai 4,137 tun bayan ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin Hamas da Isra'ila.

    Sun ce an jikkata sama da mutum 13,000.

    Isra'ila na ci gaba da lugudan wuta kan Zirin Gaza tun bayan kaddamar da hari da Hamas tayi a ranar 7 ga watan Oktoba.

  19. Yaran Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su

    Isra'ila ta ce kananan yara fiye da 20 ne ke cikin mutanen da Hamas ta kama kuma take garkuwa da su.

    Wadannan sunaye da bayanai na kananan yara 'yan kasa da shekara 18 da Hamas ta kama - kuma BBC ta tabbatar.

    Ofri, mai shekara 10 da Yuval, mai shekara 8 da kuma Oria Brodutch, 'yar shekara 4: Yaran suna garin Kfar Aza, cikin kibbutz a kusa da kan iyaka da Gaza, lokacin da 'yan Hamas suka kai hari kuma suka kama su.

    Daphna, mai shekara 15, da Ella Elyakim, mai shekara 8: An gan su a wani bidiyo lokacin da 'yan ta-da-kayar-bayan Hamas suka kamo su a cikin gidansu da ke Nahal Oz kibbutz

    Ethan Vahalomy, mai shekara 12: 'Yan bindiga ne suka dauke shi lokacin da suka kutsa cikin gidansu.

    Noam, mai shekara 15 da Alma Or, mai shekara 13: Wani makwabcin gidansu ya ga lokacin da aka janyo su daga cikin gidansu a Kibbutz Be’eri.

    Naveh, mai shekara 8, da Yahel Shoham, mai shekara 3: Tare da mahaifansu, an sace 'yan'uwan biyu daga gidansu a Kibbutz Be’eri.

    Noam Avigdori, mai shekara 12: Hamas ta sace matashiyar tare da mahaifiyarta, da sauran danginsu da dama.

    Ariel, mai shekara 3, da Kfri Bibas, mai wata 9: An dauki hoton yaran biyu rike a hannun mahaifiyarsu, lokacin da 'yan ta-da-kayar-bayan Hamas suka dauke su.

    Israel family

    Asalin hoton, TELEGRAM

    Bayanan hoto, Hamas ta tafi da Shiri Bibas da kananan 'ya'yanta guda biyu

    Erez Kalderon, mai shekara 12: Tare da sauran danginsu da dama, an dauki Erez Kalderon ne a Kibbutz Nir Oz.

    Natalie Raanan, mai shekara 17: Matashiyar na ziyartar mahaifiyarta ne a Isra'ila daga Illinois. Suna Kibbutz Nahal Oz lokacin da aka far musu kuma makwabta sun gan su lokacin da Hamas suka dauke su.

    Raz, mai shekara 5, da Aviv Asher, mai shekara 3: An dauki kananan yaran ne tare da mahaifiyarsu Doron lokacin da suke zaune a gidan danginsu da ke kusa da iyaka da Gaza

  20. Isra'ilawa sun yi liyafar juyayi ga 'yan kasar 200 da Hamas ke garkuwa da su

    Shabbat dinner table

    Asalin hoton, Getty Images

    Kimanin mako biyu kenan bayan da Hamas ta ƙaddamar da harin ba-zata kan Israi'la tare da yin garkuwa da 'yan ƙasar kimanin 200, kamar yadda alƙaluman da Isra'ila ta fitar.

    Ciki har da ƙananan yara 20 da aƙalla mutum 10 masu shekara fiye da 60.

    A ranar Juma'a da daddare ɗaruruwan 'yan Isra'ila suka shirya liyafar ranar hutu inda aka jera kujerun da babu mutane a kansu domin tunawa da wadanda Hamas take garkuwa da su.

    A birnin Tel Aviv, an gudanar da irin wannan alhini a kan waɗanda aka yi garkuwa da su. inda aka bar kujeru 200 babu kowa domin tunawa da mutanen.

    Ga wasu daga cikin hotunan alhinin.

    Israeli

    Asalin hoton, Getty Images

    Israeli flag

    Asalin hoton, Getty Images

    Israeli artist

    Asalin hoton, Getty Images