Diezani Madueke ta gurfana a kotun Birtaniya kan tuhumar rashawa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Haruna Kakangi

  1. Ban kwana

    A madadin Haruna Ibrahim Kakangi, Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Kungiyoyin kwadago sun janye shirin yajin aiki a Najeriya

    g

    Asalin hoton, Tinubu X

    Gamayyar ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye shirinsu na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.

    Bayan wata doguwar tattaunawa tsakanin wakilan ƙungiyoyin da wakilan gwamnati, yanzu dai ɓangarorin biyun sun cimma matsaya wadda ta kai da dakatar da tsunduma yajin aikin nan da kwana 30 masu zuwa.

    Dama ƙungiyoyin sun yi shirin shiga yajin aikin ne saboda matsin rayuwa da mafi yawan 'yan Najeriya suke ciki, waɗanda suka samo asali daga cire tallafin man fetur da wasu sabbin manufofi da gwamnatin Shugaba Tinubu ta gabatar.

    Wasu daga cikin abubuwan da aka cimma akwai kudi dubu 35,000 da Gwamnatin Tarayya ta amine za ta bayar ga duka ma'aikatanta wanda za a fara daga watan Satumbar da ya gabata, kafin a samu matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi, wanda ake tsammanin za a mayar da shi doka.

    Dakatar da karɓar harajin kan man dizel nan da wata shida masu zuwa. Akwai maganar motocin sufuri masu amfani da man CNG da ake za ran gwamnatin za ta ɗabbaƙa nan ba da dadewa ba.

    Batun biyan albashin malaman gaba da sakandire na gwamnatin tarayya da ke bin bashi, wanda shi ma an miƙa shi gaban ma'aikatar kwadago da ayyukan yi domin ci gaba da duba shi.

    Akwai biyan kuɗi da suka kai 25,000 da Gwamnatin Tarayya za ta yi a duk wata har na tsawon watanni uku ga magidanta miliyan 15 wanda za a fara daga wannan wata na Oktoba, kuma shirin zai hada da 'yan fansho.

    Kazalika gwamnati za ta sanya hannunta kan lamarin takin zamani domin saukaka samun shi ga manoma a faɗin ƙasar.

    Waɗannan na cikin wasu abubuwan da aka cimma, wanda hakan ya kai ga fasa tafiya yajin aikin nan da kwana 30.

  3. 'Yan Real Madrid da aka je da su Napoli

  4. Tuhumar da ake min a kotu wasan kwaikwayo ne - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Donald Trump

    Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gurfana a gaban wata kotu da ke New York, a wata shari'a da aka fara kan lamarin da ka iya shafar kasuwancinsa.

    A lokacin da yake barin kotun, Trump ya bayyana shari'ar a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa tare da neman a dakatar da alƙalin kotun.

    Tun farko, Trump ya bayyana babbar lauyar jihar New York, Letitia James a matsayin ƴar nuna wariyar launin fata.

    Ta shigar da shi ƙara ne a kotu bisa tuhumarsa da laifin zamba na kuɗi da suka kai dala miliyan 250, tare da neman a haramta wa tsohon shugaban ƙasar da ƴaƴansa biyu - Donald Junior da Eric gudanar da kasuwancinsu a jihar ta New York.

    A ɓangare ɗaya Mista Trump na fuskantar shari'o'i da suka jiɓanci manyan laifuka, kamar na ƙoƙarin murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na baya-bayan nan.

  5. Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga fursunoni 1,000 albarkacin ranar Maulidi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga sama da fursunoni 1,000 daga gidajen yarin ƙasar domin murnar bikin Maulidin annabi Muhammad (SAW).

    Wata kafar yaɗa labarun gwamnati ta ce an kuma sassauta hukuncin kisa da aka yanke wa mutane 54.

    Dama dai jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenie kan yi afuwa ga fursunoni a lokutan murna na addinin musulunci.

  6. Nijar ta amince Aljeriya ta shiga tsakani a rikicin siyasar ƙasar

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jamhuriyar Nijar ta amince da tayin da Aljeriya ta yi, ta zama mai shiga tsakani kan rikicin siyasar ƙasar.

    Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta fitar, ta ce shugaban ƙasar, Abdelmadjid Tebboune ne zai jagoranci tattaunawar.

    Dama dai Aljeriya ta daɗe tana gargaɗi kan ɗaukar duk wani matakin soji a lamarin na Nijar, inda sojoji suka ƙwace iko a watan Yuli.

    Tun farko ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Nijar, amma duk da haka ta ci gaba da amfani da hanyoyi na diflomasiyya.

  7. Ana alhinin rasuwar shaharren malamin jami'a Farfesa Umaru Shehu

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    Wata sanarwa da ƙungiyar dattijan Borno ta fitar ta bayyana rasuwar farfesa Umaru Shehu, mai shekaru 97 a duniya.

    Sanarwar wadda ta samu sa hannun sakataren ƙungiyar, Dr. Bulama Gubio, ta ce sanannen farfesan ya rasu ne da safiyar yau Litinin.

    Marigayin, wanda farfesa ne a ɓangaren likitanci, ya riƙe shugabancin Jami'ar Najeriya da ke Nsukka daga 1978 zuwa 1980.

    Ya kuma yi karantarwa a makarantu da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da ƙasar Amurka.

    Shehu ya zama Farfesa Emeritus ne a shekarar 2000, kuma shi ne na farko da ya kai irin wannan matsayi na karatu a Najeriya.

  8. Liverpool za ta ɗaukaka ƙara kan jan katin Jones

  9. Kotu ta soke zaɓen Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

    ...

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a jihar Nasarawa ta umarci hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta janye takardar shaidar cin zaɓen da ta bai wa Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC.

    A wani hukunci da kotun mai alkalai guda uku ta gabatar karkashin jagorancin Mai shari'a Ezekiel Ajayi, mafi rinjayen alƙalan sun ayyana ɗan takarar jam'iyyar PDP, David Umbugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na 18 ga watan Maris a jihar Nasarawa.

    Alƙalan sun gabatar da hukuncin ne ta hanyar manhajar Zoom.

    David Umbugadu ne ya shigar da ƙarar a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar nasarar Abdullahi Sule a zaɓen watan Maris.

  10. Yadda alayyahu zai gyara muku fatar jiki

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Kun san jerin amfanin da alayyahu ke da su ga lafiyar jiki? Ku kalli bidiyon da ke sama.

  11. Watakila Antony ya buga wa Man United wasa da Galatasaray

  12. Tsohuwar matar shugaban kasa a Ghana Theresa Kufuor ta rasu

    Ghana ex-first lady

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Theresa Kufuor ta kasance ungozoma kuma 'yar fafutuka a fannin lafiya

    Tsohuwar matar shugaban kasar Ghana, Theresa Kufuor, ta rasu tana da shekara 87.

    "Karimci da alheri da kuma girman da take da shi, ba su da na-biyu," a cewar shugaban kasar mai ci a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

    Theresa Kufuor ta kasance Uwargidan shugaban kasa daga watan Janairu 2001 zuwa Janairun 2009 kuma za a fi tunawa da ita wajen jajircewa a kan aikin bunkasa kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara a Ghana.

    Kokarin gangaminta ya zama kashin bayan kawo manufar kula da lafiyar mata kyauta a lokacin haihuwa, abin da ya yi matukar rage mace-macen mata masu juna da biyu da jarirai a kasar.

    A 1962 ne ta auri tsohon shugaban kasar John Agyekum a 1962 bayan sun gamu a wajen raye-rayen Ranar Jamhuriya na London, shekara daya kafin su yi aure.

    Ta rasu ta bar mijinta da 'ya'yanta biyar.

  13. Diezani Madueke ta bayyana a kotun Birtaniya kan rashawa

    Tohuwar ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke

    Asalin hoton, AFP

    Tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke ta gurfana a gaban wata kotu da ke birnin Landan bisa zargin ta da ayyukan rashawa.

    Madueke wadda ta gurfana a kotun yau Litinin, ana tuhumar ta ne da karɓar cin hanci na kuɗi da kayan ƙawa da amfani da jiragen sama na alfarma da kuma yin rayuwa irin ta hamshaƙan masu kuɗi a Birtaniya.

    Ana zargin cewa ta karɓi waɗannan abubuwa ne a matsayin cin hanci domin ta bayar da kwangilolin da suka shafi man fetur.

    Diezani Alison Madueke ta riƙe muƙamin minista ne ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.

    A lokacin da ta gurfana a gaban kotun a yau Litinin, ta yi magana ne kawai domin tabbatar da sunanta da kuma adireshinta.

    Ba a yi mata tambaya a kan ko ta amsa laifin ko kuma a'a ba, ko da yake dai lauyanta ya shaida wa kotun cewa ba za ta amsa laifin ba.

    Diezani ce ta biyu a cikin mutanen da suka taɓa riƙe wani babban muƙami a Najeriya, da suka gurfana gaban kotu a Birtaniya cikin shekarun nan bisa zargin ayyukan rashawa.

    A shekara ta 2012, wata kotu a Birtaniya ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori hukuncin ɗaurin shekara 13 bayan samun sa da laifin rashawa da halasta kuɗin haram.

    A shekara ta 2015 ne aka kama Diezani Madueke a birnin Landan, jim kaɗan bayan sauka daga muƙamin minista, inda aka gurfanar da ita a kotu kan laifuka shida waɗanda suka jiɓanci rashawa.

    Ta kwashe shekara takwas ɗin da suka gabata a ƙarƙashin beli a wata unguwa da ke birnin Landan.

    • Kotu ta ki yarda a taso keyar Diezani
    • Kadarorin Diezani da na wasu ƴan siyasa da gwamnatin Najeriya za ta yi gwanjonsu
  14. Ra'ayoyin ƴan Najeriya kan cikar ƙasar shekara 63 da samun ƴancin kai

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  15. Abin da ya sa sabuwar wayar iPhone 15 take daukar zafi

    Iphone

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Apple ya dora alhakin zafin da sabuwar wayarsa ta iPhone 15 ke yi a kan wata kwaya mai cutarwa da ke cikin injin sarrafa wayar da kuma ayyukan sabunta manhajoji kamar Instagram.

    Tun lokacin da kamfanin ya fara sayar da sabuwar wayar da ya fitar a watan Satumba, wasu masu amfani da iPhone 15 suka fara korafin cewa wayoyin nasu na daukar matukar zafi.

    Apple ya ce akwai wata kwaya mai cutarwa a duk lokacin da aka sabunta injin sarrafa wayar wato iOS 17.

    Ya kuma yi ikirarin cewa sauye-sauyen da ake samu a kan manhajojin wasu kamfanonin ne ke "janyo su cika injin sarrafa wayar".

    Masu amfani da iPhone sun kwan da sanin cewa wayoyinsu kan dauki dan zafi a farkon lokacin da suka fara amfani da su, ko kuma idan wayoyin na aika wasu bayanai zuwa babban rumbu adana bayanai saboda yawan lantarkin da suke ja da kuma aikin da wayar take yi fiye da kima - sai dai lamarin ya fi muni ga wayoyin iPhone 15.

    Masu amfani da wayar sun hau shafukan sada zumunta don yin korafi a kan yadda sabbin wayoyin suke daukar zafi.

    Apple ya ce mai yiwuwa ne wayar takan dauki zafi cikin kwanaki kalilan na farko "bayan kunna wayar ko kuma sake adana bayanan da take tattarawa saboda karuwar aikace-aikace a bayan fage."

    Kamfanin ya ce: "Mun fahimci wadansu yanayi kalilan da ke iya sanyawa wayoyin iPhone su dauki zafi fiye da yadda ake tsammani."

  16. Jirage sun yi luguden bam kan mutanen da ake zargi 'yan Boko Haram ne a Najeriya

    Tucano

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta yi luguden wuta a kan mayakan da ta ce suna samun mafaka a Tumbun, yankunan da ke kusa da Tafkin Chadi a cikin jihar Borno.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, rundunar sojojin saman kasar ta ce jiragenta sun harba bama-bamai inda suka lalata maboyar wadanda ta kira ''yan ta'adda' kuma ta tarwatsa sansaninsu.

    Ta ce jiragenta sun kai hare-haren ne daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Satumba, lokacin da aka tabbatar da ayyukan 'yan ta'adda, masu barazana ga cibiyoyin sojoji da fararen hula da ke zaune a Tumbun Fulani da Tumbun Shitu, in ji sojin sama.

    Sanarwar da daraktan hulda da jama'a na rundunar sojojin sama Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar na cewa an ga mayaka suna dora jarkoki a cikin motocin a-kori-kura da ake girkawa bindigogi har guda biyu da aka boye a cikin tsirrai.

    Bayan kai hare-haren ne, sojojin saman sun ce an kashe dumbin 'yan ta'adda, sannan an lalata motocin.

    Haka zalika, hare-haren da jiragen yaki suka kai a Tumbun Shitu bayan an gano maboyar bata-gari rufe a karkashin surkuki, inda kuma aka hangi motocin a-kori-kura uku da ake girka wa bindigogi suna shiga. Ta ce bayan an yi luguden wutar, rundunar ta yi bibiya inda ta tabbatar da hallaka ''yan ta'adda da dama da kuma lalata motocin a-kori-kura'.

  17. Ana sa rai Trump zai bayyana a shari'ar da za a fara yi masa kan almundahana

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Ana sa rai tsohon shugaban Amurka zai bayyana a kotun New York yau Litinin don fara wata shari'a kan almundahana da ake yi masa, wadda ta jefa harkokin kasuwancinsa cikin matsala.

    Ana zargin Mista Trump da manyan 'ya'yansa maza biyu da kuma kamfaninsa na Trump Organization, da kambama darajar kadarorinsu da fiye da dala biliyan biyu.

    A makon jiya ne, wani alkali a birnin New York ya yanke hukuncin cewa tsohon shugaban yana da alhaki kan damfarar da aka yi a harkokin kasuwanci.

    Lauyoyin Trump sun yi kokari amma ba tare da sun yi nasara wajen kawo jinkiri a shari'ar.

    A ranar Talatar da ta wuce, Mai shari'a Arthur Engoron ya yanke hukuncin cewa Mista Trump ya yi aringizon dukiyar da ya mallaka da daruruwan miliyoyin daloli.

    Atoni Janar ta New York Letitia James a yanzu tana neman a ci tarar Trump dala miliyan 250 kuma a hana shi gudanar da kasuwanci a jihar da aka haife shi.

    Sakamakon wannan al'amari.ana iya tilasta wa kamfaninsa na Trump Organization ya rabu da wasu kadarori da ya mallaka ta hanyar sayarwa ko kuma ya mika ikon tafiyar da su ga wani kamfani da kotu za ta nada.

    Trump ya ce ya shirya halartar zaman shari'ar da za a fara da safiyar Litinin din nan.

    "Zan halarci zaman kotun washe gari da safe don na kare sunana da mutuncina," ya rubuta a shafinsa na sada zumunta mai suna Truth. "Wannan shari'ar gaba daya wani wasa da hankali ne!!!"

    • Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari
  18. Mafi kyawun alherai suna nan zuwa gare ku - Uwargidan shugaban Najeriya

    Uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu, ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali a kan gyara matsalolin Najeriya, inda ta amsa cewa mijinta ba matsafi ba ne.

    Ta bayyana haka ne lokacin da ta halarci addu'o'in coci a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekara 63 da samun 'yancin kai.

    Remi Tinubu ta ce gwamnatin mijinta ta gaji dumbin matsaloli. Amma ta nanata cewa gwamnatin Tinubu ta zo da niyyar gyara matsalolin da ke damun Najeriya.

    “Ba mu zo nan, don mu yi ta dora laifi a kan wata gwamnati ba, sai don gyara barnar da aka yi,” ta fada a babbar cocin kasar da ke Abuja ranar Lahadi.

    “Mijina ba mai siddabaru ba ne. Zai tsaya tsayin daka ya yi aiki – kuma na yi imani sannan ina fatan cewa za ku yi amanna da wannan gwamnati.

    Mafi kyawun alherai suna nan tafe gare ku,” uwargidan shugaban kasar ta ce.

    • Shawarata ga matar Tinubu - Turai 'Yar'adua
  19. 'Yan kwadago za su yi taro don fitar da matsaya a kan niyyarsu ta shiga yajin aiki

    Labour unions

    Asalin hoton, Nigeria Labour Congress/X

    Shugabannin kwadago na Najeriya za su gudanar da taro da takwarorinsu na rassan kungiyoyin ma'aikata don tattauna batun karin albashin wucin gadi na N35,000 a tsawon wata shida da gwamnati ta yi ga ma'aikata a ranar Lahadi.

    Shugaban babbar kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Joe Ajaero ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan wani taro na tsawon sa'a hudu da jami'an gwamnati a karkashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar, Mista Femi Gbajabiamila.

    Kwamared Ajaero ya ce kungiyoyin kwadago su kadai, ba za su iya dakatar da shiga yajin sai-baba-ta-gani da suka tsara farawa daga gobe Talata ba, sai fa idan sun tuntubi rassan kungiyoyinsu.

    Ya ce sun gudanar da taro kuma sun duba kusan dukkan batutuwan da ake dambarwa a kansu da kuma alkawurran da gwamnati ta yi, da hanyoyin da za a bi don tabbatar da ganin an cika su.

    Don haka za mu je, mu kai wa ma'aikatan da muke wakilta, wadannan alkawurra kafin zartar da wata sabuwar matsaya, in ji Kwamared Ajaero.

  20. Ruftawar coci a Mexico ya yi sanadin mutuwar masu ibada

    Wani coci da ya rufta a arewacin Mexico, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum tara tare da jikkata karin kusan hamsin.

    Hukumomi a jihar Tamaulipas sun ce rufin cocin na Santa Cruz da ke Cidad Madero ne ya rufta, yayin da masu ibada suka taru a lokacin, cikinsu kuma har da yara.

    Wakilin BBC ya ce akalla mutum 100 ne ake kyautata zaton suna cikin ginin lokacin da rufin ya fado, kuma har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.

    Wani limamin coci da ke gundumar ya yi kira ga jama'a su kai dauki don ceto wadanda baraguzai suka danne.

    Hotunan da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jama'a suka yi cirko-cirko a kusa da ginin, yayin da ake dakon masu aikin ceto.