Mu kwana lafiya
Masu bibiyarmu ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu don samun sababbi fil daga sassan duniya.
Mu zama lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Masu bibiyarmu ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu don samun sababbi fil daga sassan duniya.
Mu zama lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar 'yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya da kuma masu dakon man sun musanta yunƙurin ƙara farashin man zuwa N700 kan lita ɗaya.
Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) ta masu kasuwancin mai da kuma Distributors and Transporters of Petroleum Products (ADITOP) sun musanta shirin ne cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar.
Suka ce farashin mai a yanzu yana tafiya ne kan farashin kasuwa, kuma an yi hasashen ƙara kuɗin man ne saboda darajar naira da ke sama tana ƙasa a kasuwar canji.
A cewar rahoton NAN, wasu 'yan kasuwa sun yi hasashen tashin farashin man ne zuwa naira 700 kan kowace lita, saɓanin yanzu da yake 540, da zarar 'yan kasuwa masu zaman kansu sun fara shiga da man cikin ƙasar a watan Yuli.
Sun yi hasashen ne bisa farashin da kasuwa ta yi wa naira a yanzu da kuma kuɗin sauke man a Najeriya.
Darajar naira ta ragu a ranar Juma'a zuwa N769.25 kan dala ɗaya a buɗaɗɗiyar kasuwar canji, bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye tsarin ƙayyade farashin naira da Babban Bankin Najeriya ke yi a baya.
Hakan na nufin darajar nairar ta ragu da kashi 0.82 cikin 100 idan aka kwatanta da N763 da aka canzar da ita kafin fara bikin Babbar Sallah a ranar Laraba.

Asalin hoton, Getty Images
Dandalin sadarwa na Twitter ya ƙayyade adadin saƙonnin da masu amfani da shi za su iya karantawa a rana, a cewar mamallakin kamfanin Elon Musk.
Cikin wani saƙo a Twitter, Mista Musk ya ce shafukan da aka tantantace (masu maki) za su iya karanta saƙo 6,000 a rana ɗaya.
A gefe guda kuma, shafukan da ba su da maki za su iya karanta 600 ne kawai.
Cikin wata sanarwa, Musk ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne da zimmar shawo kan "yawan" zirarewar bayanai da kuma daƙile masu bi ta bayan fage.
A ranar Juma'a aka faɗa wa duk waɗanda suka yi yunƙurin karanta saƙo a dandalin cewa dole ne sai sun shiga shafinsu kafin su iya ganin sa.
Matakin "na ɗan loƙaci ne", in ji Mista Musk.

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Netherlands ya nemi afuwa a hukumance game da rawar da ƙasarsa ta taka a cinikin bayi, yana mai cewa "abin ya taɓa shi sosai shi kansa".
A yau Asabar Sarki Willem-Alexander ya bayyana lamarin da "rashin imani".
Ƙasar ta zama babbar 'yar mulkin mallaka bayan ƙarni na 17, inda ta mamaye wurare da yawa a faɗin duniya kuma 'yan ƙasar suka yi safarar mutum fiye da 600,000.
Ya ƙara da cewa 'yan masarautar ba su yi wani yunƙurin dakatar da cinikin bayin ba.
Yana magana ne yayin wani taron cika shekara 160 da kawo ƙarshen cinikin bayi. Sai dai ba a sani ba ko sarkin ya shirya neman afuwar a madadin gidan sarautar kafin taron.
A watan Yuni, wani bincike ya gano cewa sarakunan Netherlands sun samu kudin da ya kai darajar yuro miliyan 545 a yanzu a tsakanin 1675 zuwa 1770 daga wuraren da suke mulkin mallaka kuma ake yin bauta.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai da kuma ma'aikatan ofishin difilomasiyyar Rasha 40 ne ke shirin barin birnin Bucharest na Romaniya a yau Asabar bayan ƙasar ta nemi su fice.
Hukumomi a Romaniya sun ce an ɗauki matakin ne don nuna adawa da yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine.
Jami'ai 11 da ma'aikata 29 tare da iyalansu ne za su fice a wani jirgin sama na fasinja, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Romaniya ta bayyana.
Tun a ranar 8 ga watan Yuni aka buƙaci su bar ƙasar, inda aka ba su wa'adin wata ɗaya.
Kamar sauran wasu ƙasashen Turai, Romaniya ta kori jami'an ne saboda zargin leƙen asiri.

Asalin hoton, KNSG

Asalin hoton, KNSG

Asalin hoton, KNSG

Asalin hoton, KNSG

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, State House

Asalin hoton, State House

Toshon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya yaba da matakan cire tallafin man fetur da na daidaita farashin dala da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗauka.
A wata tattaunawa da BBC Yariman Bakura ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakan da wasu shugabanni ƙasar suka kasa ɗauka.
Ya ƙara da cewa matakan biyu an daɗe ana shan alwashin ɗaukarsu, amma ba a cika ba sai a yanzu.
''Waɗannan matakan ko Buhari da ya gabata ya sha cin alwashin ɗaukarsu, amma ƙarshenta sai ya ɗaga zuwa watan shida, bayan kuwa ya san a watan biyar zai ƙare mulki'', in ji tsohon ɗan majalisar dattawan.
Yariman Bakura ya ce, duk da cewa za a samu tsanani a farkon waɗannan matakai, amma akwai fatan samun sauki nan gaba.
''Kamar yadda kowanne musulmi ya san cewa Allah (S.W.T) ya ce a cikin kowanne tsanani a kwai sauƙi, dama sai an ɗauki matakai da mutane daga farko suke ganin kamar an tsananta musu'', in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan hukumar kula da ala'muran ɗaurarru na ƙasar Qadri Abu Bakr ya mutu a wani mummunan hatsarin mota a gaɓar yamma da Kogin Jordan.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce hatsarin ya auku ne a kusa da garin Jama'in da ke kudu da birnin Nablus.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ambato mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar na cewa ministan tare da wasu mutum biyu sun rasu a yayin hatsarin.
Hatsarin ya auku ne sakamakon taho-mu-gama da motar ministan ta yi da ta sauran mutanen.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar ECOWAS ta yi Allah wadai kan wasu hare-hare da masu ikirarin jihadi suka kai wa jami'an tsaro a Burkina Faso, lamarin da ya haddasa mutuwar aƙalla sojoji 30.
Hukumar gudanarwar ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta gaggauta gudanar da bincike domin gurfanar da waɗanda suke da hannu a lamarin, tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan.
Hare-haren sun auku ranar Litinin da Talata a yammaci da arewacin ƙasar.
Burkina Faso na fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi waɗanda ke fitowa daga makwabciyar ƙasar Mali tun shekarar 2015.
Fiye da mutum 10,000 ne suka mutu, yayin da kusan mutum miliyan biyu suka rasa muhallansu sakamakon rikice-rikicen.
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke kawo ƙarshen aikin dakarunta da ke wanzar da zaman lafiya a Mali, masana na gargaɗi kan ƙaruwar ayyukan masu ikirarin jihadi a yammacin Afirka.

Jihar Gujurat da ke yammacin Indiya ta fuskanci mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon sa'a 24, lamarin da ya haifar da mummunar ambalirar ruwa a wasu sassan jihar.
Ƙafofiin yaɗa labaran ƙasar sun ce hukumomin kare aukuwar bala'o'i na tarayya da na jihar sun tura jami'ansu wasu sassan jihar domin taimaka wa waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Jihar na daga cikin yankunan da ke fuskantar ambaliyar Ruwa a Indiya.
Jami'ai sun ce ambaliyar ta haddasa rushewar gine-gine da nutsewar wasu a kudancin jihar.

Ambaliyar ta raba mutane da dama da muhallansu

Ruwan ya mamaye tasha jirgin ƙasa ta Kutch Gandhidham.
Haka kuma, an samu mummunar ambaliyar a yankuna Junagadh da Jamnagar da Valsad da Navsari da Mehsana da kuma Surat.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar ta ce gundumar Junagadh da ke jihar ya fuskanci ruwan sama mai ƙarfin gaske tun daga safiyar ranar Juma'a har zuwa ranar Asabar da safe.

Haka lamarin yake a gundumomin Jamnagar da Kaprada da Anjar of Kutch da kuma Khergam.


Asalin hoton, HILLSBOROUGH COUNTY SHERIFF’S OFFICE
Hukumomin a Amurka sun kama mutumin da ake zargi da da aikata kisan kai bayan shekara 40 yana wasan ɓuya da jami'an tsaro.
'Yan sanda sun ce ana zargin Donald Santini mai shekara 65 da amfani da sunayen ƙarya 13 domin kauce wa kamun jami'an tsaro bayan kashe wata mata mai shekara 33 a jihar Florida ta Amurka a shekarar 1984.
An kama shi ne a yayin da yake aiki a matsayin shugaban hukumar ruwa a wata unguwa a jihar California.
An dai tisa-ƙeyarsa zuwa jihar Florida domin fuskantar tuhuma kan zarge-zargen da ake yi masa.
Ana zarginsa da kashe wata mata mai shekara 33 a lokacin. Hukumomin sun ce Mista Santini shi ne mutum na ƙarshe da aka gani da matar kafin a tsinci gawarta a ɗaure cikin wata hanyar ruwa.
Hukumomin sun ce ya gudu daga yankin bayan da aka zarge shi da kashe matar.
An yi ta nuna hotunansa a gidajen talbijin na ƙasar a matsayin mutumin da ake nema ruwa-a-jallo a shekarun 1990, da 2005, da kuma 2013.

Tsohon gwamman Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce zama teburin sulhu da yan bindiga ne hanyar da ta fi dacewa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.
A cewarsa, irin zama teburin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi da yan Neja Delta a kudancin Najeriya, idan aka bi irin tsarin, za a iya shawo kan matsalar tsaron a yankin arewa maso yammaci.
Ya ce yana kira ga sabbin manyan hafsashin tsaro da su zauna da 'yan bindigar kamar yadda a baya aka zauna da 'yan bindigar da suka addabi yankin Naija Delta a fara maganar sulhu da su.
''Ai 'Yan Najeriya ne yawancinsu, an ce akwai mutanen waje, amma su 'yan Najeriya ɗin a zauna da su a jawo hankalinsu a nuna musu yadda aka yi wa 'yan Naija Delta, yadda aka sakar musu kudi bayan yin sulhun da su aka sakar musu kudi, suka fara sana'o'i da abin yi, su ma waɗanan nan a zauna da su a samar musu hanyar cin abinci''.
Yariman Bakuran ya ce idan hakan ta gagara to sai a bi su duk inda suke a ɗauki matakin da ya dace.
Dangane da sulhu da 'yan bindigar, da wasu jihohin ƙasar suka yi yunƙurin yi a baya, wanda kuma bai yi nasara ba, Yariman Bakura ya ce ba a yi sulhun na gaskiya ba.
Sanata Yarima ya ce ''ba wai zama da su a yi musu alƙawari, sannan a watse ne sulhu ba, ni na bibiyi duk sulhun da aka yi da su a bayan, duka alƙawuran da aka yi musu an saɓa, domin ba za ka kira mutumin da talauci da jahilci suka sanya shi shiga daji sannan ka yi tunanin yin sulhu da shi ba tare da cika masa alƙawuran da ka ɗauka masa ba''.
A filinmu na Gane mini Hanya na wannan makon Awwal Ahmad Janyau ya tattauna da tsohon gwamnan na Zamfara kan batutuwa da dama inda ya soma tsokaci kan yadda yake kallon kamun ludayin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asalin hoton, AFP/GETTY
'Yan sandan ƙasar kenya sun ce mutum 49 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku yankin kudu maso yammacin kasar.
Babbar jami'ar 'yan sandan yankin Agnes Kunga ta shaida wa BBC cewa mutum 20 sun samu munanan raunuka.
Hatsarin wanda ya rutsa da wata babbar mota ya yi sanadiyyar jikkatar gomman mutane.
Lamarin ya faru ne a lokacin da babbar motar ta kwace wa direban sanna ta yi taho-mu-gama da wasu motocin da babura tare da take masu sana'o'in da ke gefen titin.
'Yan sanda sun ce babbar motar ta buge akalla ababen hawa tara da ke tseye a gefen titin.
Mamakon ruwan sama da aka yi ya haifar da jinkirin aikin ceto mutanen da hatsarin ya shafa, lamarin da ya sa mutane da dama suka mutu.

Asalin hoton, Nigerian Police/Twitter
Muƙaddashin babban Sifeton 'yan sandan Najeriya Olukayode Adeolu Egbetokun ya yi Allah wadai da wasu jami'an rundunar 'yan sanda da suka tuƙa mota suka bi ta kan wani mutum a wani lamari da ya faru ranar Alhamis a jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce mukaddashin Babban Sifeton 'yan sandan ya bayar da umarni ga jami'an 'yan sandan - waɗanda yanzu haka ke tsare a Edo - da su hallara a shalkwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin domin ɗaukar mataki a kansu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga yadda jami'an 'yan sandan suka tuka wata mota tare da bin ta kan wani mutum da ake tunani direban motar ne, da ya kwanta a gaban motar, lamarin da ya jefa mutanen da ke wajen cikin firgici.
Sanarwar 'yan sandan ta yi kira ga al'umma musamman mutanen garin Ekpoma da su kwantar da hankulansu, tare da alƙawarta cewa rundunar 'yan sandan ba za ta lamunci irin wannan mummunan aika-aika da wasu ɓata-garin jami'anta ke yi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wani tsohon minista a Burtaniya ya shaida wa BBC dewa yarjejeniyar da gwamnati ta kulla ta tisa-ƙeyar masu neman mafaka zuwa Rwanda na da hadari ga martabar Birtaniya a idon duniya.
Kalaman Justine Greening na zuwa ne bayan wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a makon da ya gabata ya bayyana cewa kasar Rwanda na goyon bayan yan tawayen M23 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Ana zargin ƙungiyar da kisan gilla, da fyade da kuma raba mutane miliyan guda da matsugunansu
Amurka da EU sun buƙaci Rwanda ta daina goya wa 'yan tawayen baya.
Wani jakadan Birtaniya a yankin ya yi tir da abin da ya kira 'goyon bayan 'yan tawayen ƙetare', ba tare da kama sunan Rwandan ba.
Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya, Suella Braverman, ta ce har yanzu shirin na nan daran dam, duk da hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar Alhamis na cewa shirin ya saɓa doka
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.