Rushe ƙasaitaccen shataletalen Kano ya janyo zazzafar muhawara
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa, Haruna Kakangi and A'isha Babangida
Ƴan sanda sun kama baƙin haure 12 a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Rudunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta damke wasu bakin haure 12 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi zamba.
A wata sanarwa da rundunar da fitar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun hada da ‘yan asalin kasar Mali guda 7 da kuma ‘yan jamhuriyar Niger guda 5.
Sanarwan ta cigaba da cewa bakin hauren korarru ne daga kasar Saudiyya kuma an kama su ne bayan 'yan sanda sun kai samame a inda suke zaune a ungwar hotoro ‘yandodo quarters da ke birnin Kano.
A lokacin da aka kama su, an samu wadanda ake zargin da wasu sabbin raunuka da suka yi wa kansu a manyan yatsunsu ta hanyar amfani da reza.
‘Yan sanda sun ce manufar ita ce domin yin basaja a hoton ɗan yatsa ta yadda hukumomin Saudiyya ba za su iya gano su ba idan sun koma ƙasar.
Sanarwan ta ce bayan rundunar ta kammala bincike, za ta mika dukkan wadanda ake zargin zuwa hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Kano domin cigaba da nasu binciken.
Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC AbdulRasheed Bawa
Matar da ta kashe mahaifiyarta ta miƙa kanta ga ƴan sanda

Asalin hoton, Getty Images
Wata mata mai shekara 39 wadda ake zargin ta kashe mahaifiyarta ta hanyar ɗirka mata maganin hawan jini fiye da ƙa'ida ta miƙa kanta ga ƴansanda.
Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Yuni, inda matar ta kai kanta ga ofishin ƴansanda a garin Bengaluru na ƙasar Indiya.
A lokacin da ta isa ofishin, matar mai suna Sonali Sen, ta shaida wa ƴansanda cewa ita ce ta kashe mahaifiyarta da kanta.
Ta kuma ce mahaifiyar tata ce ta umurce ta da yin hakan.
A lokacin da ta yi ƙarin bayani kan lamarin, Sonali ta ce bayan ta kashe mahaifiyar tata, ta sanya gawar a cikin akwati kafin daga bisani ta ɗauko ta ta tunkaro ofishin ƴan sanda.
A lokacin da suka duba, ƴan sanda sun gano hoton mahaifin Sonali a cikin akwatin gawar, wanda ya daɗe da rasuwa.
Ƴansanda sun ce Sonali ta banka wa tsohuwar tata ƙwayoyin magani hawan jini har guda 30, inda bayan wani ɗan lokaci ta samu bugun zuciya, daga ƙarshe sai Sonali ta yi amfani da wani tsumma ta shaƙe mata wuya, daga nan rai ya yi halinsa.
Binciken da ƴan sanda suka gudanar ya nuna cewa marigayiyar ta koma zama a gidan ɗiyarta Sonali da mijinta, waɗanda suke zama tare da uwar mijin.
Sai dai bayanai sun ce tun bayan da ta koma gidan da zama take samu rashin jituwa da uwar mijin ɗiyar tata.
Lamarin ya yi ƙamari, inda a ranar Lahadi, toshuwa Biva cikin fushi ta buƙaci ɗiyar tata da ta kashe ta.
Yanzu dai ƴansanda suna tsare da Sonali bisa tuhumar ta da laifin kisan kai, bayan da ta ce ta kashe mahaifiyar tata ce domin cika umarnin da ta ba ta.
Mutane 59 sun mutu sakamakon nitsewar jirgin ruwa ɗauke da ƴan gudun Hijira

Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, An kai wadanda suka tsira asibiti a garin Kalamata A cewar hukumomin ƙasar Girka, ya zuwa yanzu an tabbatar da cewa mutane 59 ne suka nutse a ruwa, sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da ke dauke da 'yan gudun hijira.
An bayyana cewa, jirgin ya taso ne daga birnin Tabruk na ƙasar Libya zuwa kasar Italiya a lokacin da ya yi hatsari a kusa da gaɓar tekun Peloponnese na kasar Girka.
Wani jirgin sintiri na hukumar Turai Frontex ya hango jirgin a ranar Talata inda ya kai rahoton inda yake ga jami'an tsaron gaɓar tekun Girka.
Bayan nutsewar wannan jirgin, kwale-kwalen ceto sun yi nasarar kwashe mutane sama da 100 daga cikin ruwan, amma iska mai karfi ta kawo cikas wurin cigaba da aikin.
Fasinjojin da aka ceto sun ce wadanda suka dauko su a jirgin ba su ba su rigunan ruwa ba.
Najeriya ta sake komawa ta ɗaya wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ta sake komawa matsayinta ta ɗaya a cikin jerin ƙasashe masu fitar da ɗanyen mai bayan da ta samu ƙari a yawan ɗanyen man da take fitarwa a kowace rana.
A watan Mayu, alƙaluma sun sun nuna cewa Najeriya ta rinƙa fitar da ɗanyen mai ganga miliyan 1.184.
Alƙaluman wata-wata da Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur da Duniya (OPEC) ta fitar sun nuna cewa Najeriya ta ɗara Libya, mai fitar da ganga miliyan 1,158, da Angola mai fitar da ganga miliyan 1,111, da kuma Algeria mai fitar da ganga 962,000.
A cikin shekarar nan ta 2023 ne dai yawan ɗanyen man da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare ya ragu matuƙa, inda ya koma ganga 999,000 a kowace rana, lamarin da ya mayar da ita bayan ƙasashen Libya da Angola da Algeria.
Najeriya dai na fama da matsalar masu satar ɗanyen mai, da rashin tsaro a yankin Neja-Delta mai arziƙin man fetur, da fasa bututan mai, waɗanda gwamnati ta ce su ne manyan dalilan da suka sanya fitar da ɗanyen man ya yi ƙasa sosai.
An zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya kashe budurwar da ta ƙi auren shi

Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mohamed Adel ya amsa laifin kisan a shari’ar da aka yi masa a shekarar da ta gabata Hukumomi a Masar sun zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin kashe wata ɗalibar jami’a a bara bayan ta ƙi amincewa da buƙatar aurensa.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda Mohammad Adel ya caka wa Nayra Ashraf wuƙa tare da yanka mata maƙogwaro a watan Yunin bara a wajen jami'ar Mansoura, inda su biyun suka yi karatu.
Hakan ya haifar da firgici a faɗin ƙasar yayin da shari'ar ta sake buɗe muhawara kan cin zarafin mata.
Adel ya fuskanci shari'a cikin gaggawa kuma an same shi da laifin kisan kai da gangan.

Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Iyayen Nayra Ashraf mai shekaru 21 sun halarci shari'ar a bara A Masar akan zartar da hukuncin kisa kan masu laifi ne cikin shekaru hudu bayan yanke hukunci, amma a shari'ar Adel, masu gabatar da ƙara sun buƙaci a gaggauta yanke masa hukuncin.
Mahaifin Ms Ashraf ya ce duk da cewa kisan da aka yanke wa wanda ya kashe diyarsa ba zai dawo da ita ba, an tabbatar da adalci.
Wasu mata masu zaman kansu sun kai abokin huldarsu kotu

Asalin hoton, Getty Images
An gurfanar da wani matashi a gaban kotun majistare da ke jihar Ondo, bisa zargin kwanciya da wasu mata masu zaman kansu huɗu amma ya ƙi biya.
Sun ce kamata ya yi abokin hulɗar nasu ya biya su naira 45,000 kuɗin aikin da aka yi masa, amma bai biya ba.
'Yan sanda sun gurfanar da matashin mai shekara 25 a kotu, bisa zargin yaudarar matan huɗu, ta hanyar aika musu da sakon kuɗin banki na bogi da niyyar zamba.
Mai shigar da ƙarar Akao Moremi, ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin, ya aikata hakan ne a cikin watan Oktoban 2022 a birnin Ondo.
Alƙaliyar kotun Mai shari'a Charity Adeyanju, ta amince da buƙatar lauyan wanda ake zargin, sannan ta bayar da umarnin cewa a biya masu ƙarar kuɗinsu kafin zaman kotun na gaba.
Alƙaliyar ta ce kotun ta kuma bayar da umarnin cewa dole ne a gabatar da shaidar biyan kuɗin a gaban kotu yayin zama na gaba.
Daga ƙarshe Mai shari'a Adeyanju ta ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Yunin da muke ciki.
An tuhumi magoya bayan Leeds da aikata rashin da'a
Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru a Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙididiga ta ƙasar Ghana ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 42.2 a watan Mayun da ya gabata, a maimakon kashi 41.2 da yake a watan Afrilu.
Hukumar ta ce farashin kayayyakin ya ƙaru ne sakamakon ƙaruwar farashin kayan abinci zuwa kashi 52.4 cikin 100 adadi mafi yawa da ya taɓa kai wa cikin watanni masu yawa.
Sauran abubuwan da suka haddasa ƙaruwar hauhawar farashin, sun haɗar da tashin farashin gidaje da ruwa da wutar lantarki, da man fetur.
Ƙasar Ghana dai na yunƙurin farfaɗowa daga hauhawar farashin bayan da a watan Disamban bara ya kai kashi 54 cikin 100.
Iyalai da dama na fama matsin tattalin arziki.
Gwamnatin ƙasar dai na alaƙanta matsalar da annobar korona da ta shafi duniya da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, to sai dai 'yan adawa na ganin laifin gwamnatin ƙasar ne.
A yanzu ƙasar na karɓar bashin dala biliyan uku a ƙarƙashin wani shirnin na shekaru uku da asusun bayar da lamuni na duniya.
Hakan na nufin gwamnatin ƙasar za ta gabatar da wasu tsare-tsare masu tsauri domin bunƙasa kuɗin shigar ƙasar.
Shugaban ƙasar Nana Akufo Addo ya yi kira ga 'yan ƙasar da yi haƙuri kasancewar taimakon IMF ba zai iya warware matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba.
Rushe ƙasaitaccen shataletale ya janyo ka-ce-na-ce a Kano

Asalin hoton, Family
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gina sabon shataletale a gaban gidan gwamnatin jihar.
Bayan da ta rushe tsohon shataletalen sakamakon dalilai na tsaro kamar yadda gwamnatin ta bayyana.
A cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta tuntuɓi injiniyoyi a fannin gine-gine domin yin nazari game da ginin shataletalen kafin ta rusa shi.
A cewar sanarwar injiniyoyin sun ce ginin ba shi da inganci kuma zai iya faɗuwa tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.
Saboda a cewarsu an gina shi da kayyaki marasa inganci, a maimakon amfani da tsantsar siminti da kyakkyawan kankare.
Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa masanan sun bai wa gwamnati shawarar cewa ginin ya yi tsawo a gina shi a gaban gidan gwamnatin jihar, saboda ya tokare babbar kofar gidan.
Sanarawar ta ƙara da cewa ginin na haifar wa direbobi matsaloli saboda yadda yake rufe musu ganin sauran hanyoyin da ke da mahaɗa a shataletalen.
Kan hakan ne gwamnatin jihar ta ce ya zama wajibi ta rushe ginin, domin sake fasalin ginin ta yadda za ta rage tsayinsa ta yadda za a riƙa hango babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin tare da kare masu ababen hawa.
Rahotonni sun ce an wayi gari da ganin motocin rusau a kan ginin shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar.
Gbajabiamila ya sauka daga kujerar ɗan majalisa

Asalin hoton, Femi Gbajabiamila/Twitter
Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya sauka daga kujerarsa ta ɗan majalisar wakilan Najeriya, domin fara aiki a sabon muƙaminsa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.
Sabon kakakin majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanto wasiƙar murabus ɗin nasa a zauren majalisar ranar Laraba.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa mista Gbajabiamila a matsayin sabon shugaban ma'aikata na fadarsa.
Mista Femi dai ya samu nasara a zaɓen kujerar ɗan majalisar wakilan ƙasar mai wakiltar mazaɓar Surulere ta ɗaya a jihar Legas
An dai yi ta nuna damuwa kan yadda ɗan majalisar zai tafiyar da muƙaman biyu, bayan da ya ƙarbi rantsuwa tare da sauran 'yan majalisar sabuwar majalisa ta 10 ranar Talata, har ma ya jefa ƙuri'arsa a zaɓen shugabannin majalisar.
A yanzu hukumar zaɓen ƙasar za ta shirya zaɓen cike-giɓi na ɗan majalisar wakilan mazaɓar.
'Yar Najeriya ta kammala girkin sa'a 120 don kafa tarihi a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Wata 'yar Najeriya mai suna Adedamilola Adeparusi, ta cika burinta wajen kammala girkin sa'o'i 120, a wani yunƙuri na karya tarihin da wata 'yan ƙasar ta kafa na shafe sa'o'i masu yawa tana girki ba tare da hutawa ba.
A ranar Talata ne Kundin Adana Tarihi na Duniya (Guinness World Records) ya tabbatar da Hilda Baci a matsayin wadda ta fi kowa daɗewa tana girki ba tare da hutawa ba.
Hilda ta shafe sa'o'i 100 tana girki inda take hutun minti biyar cikin kowacce sa'a ɗaya.
To sai dai Kundin Adana Tarihin na Duniya ya ce sa'o'i 93 da miti 11 ne Hilda Baci ta kwashe tana girkin ba 100 kamar yadda ta yi iƙirari tun da farko.
Mutanen da suka taro domin shaida girkin Misis Adeparusi da aka fi sani da Dammy 'yar asalin jihar Ekiti, sun barke ta sowa a daidai lokacin da ta kammala girkin nata.
A ranar Laraba ne ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ''Na kammala girkin sa'o'i 120. Ina miƙa saƙon godiya a gare ku bisa taimakon da kuka nuna min ta fuskar ƙarfafa gwiwwa da kuɗi da shaida yadda na gudanar da aikin da addu'o'inku. in ba don taimakon da kuka ba ni ba, da hakan bai kasance ba''.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kawo yanzu dai Kundin Adana Tarihin na Duniya bai yanke hukunci kan duba yunƙurin kafa tarihin da misis Dammy ta yi ba.
To amma kasancewar Hilda Baci ba ta daɗe da kafa wannan tarihi ba, mutane a shafukan sada zumunta na ta sukar yunkurin Dammy, inda wasu ke kallon yunƙurin nata a matsayin ƙoƙarin ƙwace fice ko tarihin da Hilda ta yi a fannin.
M23 na da hannu a kisan kiyashin DR Congo - HRW

Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ... Kungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce ta ƙara samun wasu shaidun da ke nuna cewa 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda sun kashe mutane da dama a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo waɗanda daga bisani aka binne su a kaburbura.
Kungiyar ta ce an kashe fararen hula da 'yan bindiga a lokacin da da ƙungiyar 'yan tawayen M23 ta mamaye ƙauyen Kishishe tsakanin watan Nuwamba zuwa Afrilun da ya gabata.
Ƙasar Rwanda dai ta musanta goyon bayan 'yan tawayen M23 waɗanda a baya suka ce ba su da hannu a kisan kiyashin.
HRW ta shawarci gwamnatin Kongo ta nemi taimako daga Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka don gudanar yanda za su haƙo gawarwakin da aka binne, tare da hukunta waɗanda ke da hannu a cikin lamarin.
'Yan bindiga sun halaka mutum 23 a ƙauyukan jihar Plateau

Asalin hoton, Getty Images
'Yan bindiga sun kashe a kalla mutum 23 a wasu tagwayen hare-hare da suka kai wasu ƙauyukan jihar Plateau, a wani rikici mai alaƙa da manoma da makiyaya.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Alfred Alabo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe wasu makiyaya biyu tare da manoma 21 a wasu tagwayen hare-hare na ramuwar gayya da aka ƙaddamar a wasu ƙauyukan jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya ce ya kaɗu da kashe-kashen, yana mai cewa ya damu matuƙa yadda harkokin tsaron jihar ke ƙara zama abin tayar da hankali.
“Matsalar tsaron jiharmu ya zama tamkar tsohon injin da ke buƙatar kwaskwarima da ingantaccen gyara'', in ji sanarwar.
Jihar Plateau wadda ke tsakiyar Najeriya a lokuta da dama na fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci.
Matan Najeriya fiye da 25,000 sun maƙale a Mali – NAPTIP

Asalin hoton, NAPTIP
Bayanan hoto, ... Hukumar da ke Yaƙi da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce aƙalla mata da ‘yan mata 'yan Najeriya sama da 25,000 da aka yi safarar su ne suka makale a Mali.
Kwamandan hukumar mai lura da shiyyar Benin, Mista Nduka Nwanwenne ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron bita da aka shirya wa ƙwararru kan harkokin yada labarai a birnin Legas.
Kamfanin dillancin Labaran Ƙasar NAN ya ce an shirya taron bitar ne domin bunƙasa ƙwarewar mahalarta taron wajen wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da safarar mutane.
Ita ma babbar daraktar hukumar ta NAPTIP, Fatima Waziri-Azi, ta ce babban maƙasudin taron bitar shi ne jawo hankalin ƙwararrun kafafen yada labarai kan mummunar ɗabi’ar safarar mutane domin ƙara wayar da kan jama’a kan illolin.
Mista Nduka ya ce “Binciken da hukumar NAPTIP ta gudanar ya gano cewa ana yaudarar mafi yawa daga cikin matan ne da kuɗi wajen yin safararsu, domin kuwa a cewarsa binciken nasu ya gano cewa mazan Mali sun fi kashe wa mata kudi idan aka kwatanta da na Najeriya.
Kwamandan ya ce hukumar ta kama mutum 9,102 da ake zargi da safarar mutane, tare da kuɓutar da mutum 20,660 tsakanin 2004 zuwa Mayu 2023.
Masu cin ganima sun dirar wa shataletalen gidan gwamnatin Kano da aka rusa

Asalin hoton, Twitter/Jaafa Jaafar
Jim kaɗan bayan gwamnatin Kano ta rusa shataletalen gidan gwamnatin jihar, masu ɗibar 'ganima' sun dira a wurin domin kwasar ƙarafan rodi da sauran abubuwan amfani.
Rahotonnin sun ce an wayi gari ne kawai da ganin motocin rusau a kan ginin shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar.

Mutane musamman a shafukan sada zumunta na ta bayyana mabambantan ra'ayoyi game da rusa ginin, wanda aka gina domin bikin cikar jihar shekara 50 da kafuwa.

Kawo dai yanzu babu wani bayani daga gwamantin jihar Kano game da dalilin rusa ƙasaitaccen ginin.

A baya-bayan nan dai ana sukar sabuwar gwamnatin saboda rusa wasu wuraren da gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta gina, inda ta yi zargin cewa an yi gine-ginen ne a filayen da aka mallakesu ba bisa ƙa'ida ba.
Putin ya tabbatar da ɓatan tankokin Rasha 54

Asalin hoton, SPUTNIK/KREMLIN POOL/EPA-EFE/REX/Shutterstock
Bayanan hoto, ... Shugaban ƙasar Rasha ya gana da masu shafukan yaɗa labaran yaƙi, inda ya yi iƙirarin cewa hare-haren Ukraine ba su yi wata ɓarna a ƙasarsa ba.
Mista Putin ya shaida wa ƙungiyar a birnin Moscow cewa rundunar sojin ƙasar na iya samun naƙasu, to sai dai babau abin da hakan zai sauya a cewarsa.
Ya kuma yi zargin cewa Ukraine na da hannu wajen kai hari madatsar ruwan Kakhovkabayan da hare-haren da ta kai da harsasan Amurka suka yi wa madatsar ruwan mummunar ɓarna.
Ya ci gaba da cewa a yayin farmakin na Ukraine, Rasha ta yi asarar tankokin yaƙi 54, inda ita kuma Ukraine ta rasa tankokin yaki 160.
Jonathan ya yi wa Tinubu bayani kan zaɓen raba gardama a Mali

Asalin hoton, Dada Olusegun
Jakadan ƙungiyar ƙasashen ECOWAS na musamman da ke shiga tsakani kan rikice-rikicen da ake yi a Mali, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wa sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu bayani game da abubuwan da ke faruwa Mali da sauran ƙasashen yammacin Afirka.
Mista Jonathan ,ya ce ya je fadar shugaban ƙasa ne domin miƙa wa Tinubu sakamakon tattaunawa da sauran mambobin ƙungiyar Afrika ta yamma da yake jagoranta.
A matsayin sa na wakili na musamman, ga ƙungiyar ECOWAS, tsohon shugaban na Najeriya na jagorantar tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar Mali ciki har da shugaban mulkin sojin ƙasar Col Assimi Goïta, da ƙungiyoyin farar hula da na addinai domin warware rikicin zamantakewa da siyasa a ƙasar.
Jonathan ya ce a matsayinsa na mai shiga tsakani na ƙungiyar ECOWAS akwai wasu batutuwan da suka shafi nahiyar da kuma yankin da yake tattaunawa da shugabanni daban-daban.
Hajjin bana: zuwa yanzu an yi jigilar maniyyata 46,000 - NAHCON

Asalin hoton, NAHCON
Bayanan hoto, Maniyyatan Najeriya Hukumar Alhazan Najeriya ta ce kawo yanzu ta yi jigilar maniyyata 46,258 zuwa kasa mai tsarki tun bayan fara jigilar maniyyatan ranar 25 ga watan Mayu.
Yayin da yake magana da manema labarai ranar Talata a Abuja, shugaban hukumar Alhazan ƙasar Zikrullah Hassan,ya ce hukumar Alhazan ƙasar ta samu biza 73,310 daga cikin kujerun aikin haji 75,000 da hukumar ta ware wa jihohin ƙasar.
Zikrullah Hassan wanda ya samu wakilcin kwamishin tsare-tsare da tattara alƙaluma na hukumar Sheikh Suleiman Momoh, ya ce duk da matsalolin da hukumar ta fuskanta yayin jigilar maniyatan, hukumar za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin kowanne maniyyaci ya samu tafiya.
“Akwai matsalolin da suka taso, amma muna ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalolin''.
Ya ƙara da cewa hukumar ta kammala shirya wuraren zama da abincin maniyyata a biranen Makka da Madina, haka kuma hukumar ta ce za ta tabbatar da sauke nauyin maniyyatan musamman a ƙasa mai tsarki.
Sheikh Suleiman Momoh ya ce yayin da ya rage mako biyu aikin hajjin ya kankaman, hukumar za ta tabbatar da an ɗauki kowanne maniyaci da ya biya kuɗinsa zuwa ƙasa mai tsarki, kafin lokacin.
