Gwamnonin jihohi sun goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa and Haruna Kakangi
Rikicin Sudan na haifar da ruɗani ga ƙasashe makwafta
Rikicin da ake ci gaba da yi a Sudan ya haifar da wani rikici a yankin da ke da nasaba da tsaro da tattalin arziki, wani babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a Geneva ya yi gargadin haka.
"Wannan rikicin na iya janyo abubuwa da dama a Sudan ta Kudu - akwai tattalin arziki wanda ke da matukar muni saboda wasu sassan arewacin Sudan ta Kudu sun dogara ne sosai kan tattalin arzikin Sudan," in ji mataimakin babban kwamishinan ayyuka na hukumar kula da 'yan gudun hijiran. Raouf Mazou.
Mista Mazou ya ci gaba da cewa, "Saboda haka, rikici ne na yanki da ya shafi tsaro, amma kuma yana da matukar muhimmanci da yadda ya shafi tattalin arziki," ya kara da cewa Chadi ta nuna irin wannan damuwar.
Tun bayan barkewar rikici a Sudan a watan Afrilu, 'yan gudun hijira sun tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu, yawancinsu 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu ne da ke komawa kasar da a baya aka tilasta musu yin hijira.
Suna zuwa tare da 'yan gudun hijira daga Sudan da wasu kasashe daban-daban.
Adadin sabbin wadanda suka ketara zuwa Sudan ta Kudu a wannan makon ya zarce 100,000, in ji hukumar.
Mista Mazou ya shaida wa manema labarai a Juba babban birnin kasar ranar Talata cewa, kimanin 'yan gudun hijira 7,000 da suka yi rajista ne suka shiga Sudan ta kudu tun bayan barkewar rikicin na Sudan.
A cikin su akwai 'yan gudun hijirar Sudan 3,500, da habashawa 2,600, da 'yan Eritriya da sauran 'yan kasashe su 1,800.
Mista Mazou ya ce 'yan gudun hijira 400,000 suka tsere daga Sudan zuwa kasashe makwafta.
N'Golo Kante ya koma Al-Ittihad ta Saudi Arabia
Ambaliyar ruwa ta mamaye garuruwa 29 bayan ɓallewar dam a Ukraine
Asalin hoton, Reuters
Kasashen Ukraine da Rasha na zargin juna da tarwatsa dam din da gangan, sai dai kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa ɓallewar madatsar ruwan ba.
Shugaba Zelensky ya ce dubban daruruwan mutane sun rasa hanyar samun ruwan sha.
An tattauna da wasu kwararru kan abin da ka iya faruwa.
A cewar wasu masana, fadan da aka yi a watannin Augusta da Nuwamba na da hannu cikin fashewar madatsar ruwan.
"Ina tsammanin gazawar tsarin ginin sakamakon illar da aka yi a baya ta dalilin yakin zai iya zama sanadi," in ji Mark Mulligan, farfesa a fannin yanayi a jami'ar Landan.
Tunani na biyu kuma shi ne, Rasha, wacce ke kula da dam din, ta bar yawan ruwan da ke tafkin da ke bayan dam din ya yi yawa da gangan inda haka ya haddasa ɓallewar madatsar.
A wani nazarin hotunan tauraron dan adam, wanda hukumar kula da aikin gona ta Amurka ta gudanar, yawan ruwan ya karu matuka a cikin 'yan watannin da suka gabata.
Kotu ta yi watsi da ƙarar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Asalin hoton, Reuters
Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yi watsi wata karar da tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma ya shigar kan wani babban mai shigar da kara da kuma wani dan jarida.
Mista Zuma ya yi ikirarin cewa Billy Downer da Karyn Maughan sun fallasa wadansu bayanansa na sirri.
Lauyan Ms Maughan ya bayar da hujjar cewa Mista Zuma ya shigar da karar ce saboda bai ji dadin yadda ta bayar da rahoton wata karar da aka shigar ana tuhumar tsohon shugaban kasar da rashawa ba.
Kotun da ke zama a Pietermaritzburg ta yanke hukuncin cewa karar da mista zuma ya shigar ta keta 'yancin 'yan jarida da kuma kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu.
Kotun ta kuma ce an haramta wa Mista Zuma yin wadannan tuhume-tuhumen a cikin sirri.
Mista Downer shi ne jagoran masu gabatar da kara a shari'ar rashawa da ake yi wa Mista Zuma, wanda har yanzu ake ta jinkiri.
Muhimman dokoki biyar da majalisa ta tara ta samar a Najeriya
Gwamnonin jihohi sun goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya
Asalin hoton, PRESIDENCY
Gwamnonin jihohin
Najeriya sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu
ya ɗauka na cire tallafin man fetur.
Gwamnonin sun
bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar a ranar Laraba.
Wata sanarwa da
ta fito ta hannun daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban Najeriya, Abiodun
Oladunjoye, ta ce gwamnonin sun rinƙa yin jawabi ɗaya bayan ɗaya a lokacin
ganawar, inda suka rinƙa yaba wa shugaban ƙasar kan matakin da ya ɗauka.
Gwamnonin waɗanda
suka je fadar bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar
Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq sun ce za su yi aiki tare da shugaban ƙasar wajen
ganin an magance matsalolin da cire tallafin zai haifar.
Asalin hoton, PRESIDENCY
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu tare da gwamnonin jihohin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ne ya sanar da ƙarshen tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Maris, lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki.
Asalin hoton, PRESIDENCY
Ya ce gwamnati za ta karkatar da kuɗaɗen tallafin zuwa ga wasu ɓangarori na ci gaban ƙasa.
Sai dai ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar sun nuna adawa da lamarin, inda suka yi yunƙurin shiga yajin aiki, amma daga baya an cimma matsaya bayan jerin tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin na ƙwadago.
Asalin hoton, PRESIDENCY
An fara sauraron ƙarar da APC ta shigar kan nasarar Abba Gida-gida, Daga Zahradden Lawan
Asalin hoton, FACEBOOK/NASIRU GAWUNA
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a jihar
Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara zaman share fagen shari'a, inda ta amince da bukatar INEC na aiwatar da
wasu gyare-gyare a cikin ƙunshi martanin da ta shigar a gaban kotun.
Jam'iyyar
APC reshen jihar Kano ce ta shigar da ƙara gaban kotun korafe-korafen zaɓen
inda take ƙalubalantar nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan
Kano a zaɓen ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Sauran mutanen da jam'iyyar APCn ta kai ƙara gaban kotun, har da hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar NNPP.
A zaman kotun na yau an mayar da hankali ne, kan tsattsefe bayanai da takardun dukkan ɓangarorin da ke cikin shari'ar suka shigar gaban kotun.
An ɗauki lokaci ana
muhawara kan kuskuren da INEC ta yi wajen rubuta sunan APC a cikin martaninsu.
Barista Yahaya Isa Abdulrashid daya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar INEC ya kuma shaida wa BBC cewa Kotu ta riga ta amince da su gyara All Progressive Party da aka yi kuskuren rubutawa zuwa All Progressive Congress.
''Mun riga mun shigar da martaninmu, yanzu abin da ya rage shi ne a fara wannna shari'ar gadan-gadan\'', in ji shi.
Baya ga hukumar INEC da APC ta maka a gaban kotun akwai kuma
Inginiya Abba Kabir Yusuf, inda ta ke kalubalantar nasarar da ya samu.
Barista
Bashir Yusuf Tudun Wuzirci na cikin lauyoyin gwamna Abba Gida-Gida, ya kuma shaida wa BBC cewa sun gabatar da takardun hujjojinsu da ke nuna cewa sun yi nasara a zaɓen.
''Yanzu abin da muke jira shi ne kotun ta fara sauraron ƙorafe-ƙorafen'', in ji lauyan.
Barista Abdullahi Adamu Fagge auyan APC wadda ta shigar da ƙarar, ya ce zaman kotun na yau ,ya kawo ƙarshen gutsiri-tsoman da wasu ke yi
cewa ba a shigar da ƙarar ba ma.
''Maganar gaskiya yadda aka fara zaman nan yau kamar yadda kowa ya gani kuma ya ji, zama ne da ya yi mana kyau, kuma zama ne da aka fara shi bisa nasara game da yadda al'amuran suke faruwa'', in ji shi.
Ya kuma ce ''mun tanadi duka takardun hujjojinmu da za mu gabatarwa kotun domin tabbatar da ƙorafinmu''.
Barista Ibrahim Isa Wangida na cikin tawagar lauyoyin
jam’iyyar NNPP ya ce sun shirya tunkarar duk wani abu da APC za ta bijiro da shi
a gaban kotun.
Ya kara da cewa ''tun farkon da kaka kawo ƙararar mun dube ta, mun kuma tunkare ta, mun kuma shigar da ƙorarrafin cewar tun farko ma bai kamata a ɓata lokaci wajen wannan shari'ar ba, saboda ita kanta kotun da aka shigar da ƙarar ma ba ta da hurumin sauraron ƙarar da wanda ya yi takara ma babu sunansa a kai''.
''Kuma akwai ƙa'idoji da dama da aka saɓa a shigar da ƙarar waɗanda idan aka yi la'akari da su ma bai kamata a ɓata lokaci a kan shari'ar ba'', in ji shi.
Jam'iyyar APC dai ta na neman kotu ta ayyanata a matsayin
wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar Kano, da halastattun ƙuri'u mafi rinjaye ko
kuma, idan hakan ba ta samu ba, to a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala
ba, tare da ba da umarnin sake zaɓe a tashoshin zaɓen da aka soke.
Kotun dai ta ɗage zamanta zuwa gobe domin a saurari ɓangaren
masu ƙara da waɗanda ake ƙara, a matakin share fagen shiga shari’ar.
Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ce dai ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano cikin watan Maris din da ya gabata.
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru yusuf Gawuna na APC ya samu ƙuri'u 890,705.
Angel Di Maria ya bar Juventus
Za a yi wa Fafaroma Fransis tiyata
Fadar Vatican ta sanar da cewa za a yi wa fafaroma Francis tiyata sakamakon wata jinya da yake fama da ita a cikinsa.
A wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce Fafaroman zai kasance a asibitin birnin Roma na 'yan ''kwanaki'' bayan yi masa tiyatar.
Shugaban cocin Katalikan mai shekarar 86 na fama da rashin lafiya a 'yan shekarun nan, inda yake amfani da sanda da keken marasa lafiya sakamakon ciwon ƙafa da yake fama da shi.
Sanarwar da fadar Vatican ɗin ta fitar ta ce tawagar likitocin Fafaroman ne suka yanke shawarar yi masa tiyata, sakamakon lura da suka yi cewa jinyar tasa na buƙatar tiyatar.
Da safiyar ranar Laraba ne Fafaroman ya gabatar ya jagorancin taron addu'o'i da aka saba gudanarwar mako-mako a cocinsa.
Messi zai koma Inter Miami ta Amurka
Tinubu na ganawa da gwamnonin jihohi
Asalin hoton, Buhari Sallau/Instagram
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na ganawa da gwamnonin jihohin kasar 36 a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Wannan ce ganawar shugaban ta farko da ƙungiyar gwamnonin ƙasar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq tun bayan hawansa karagar mulki a makon da ya gabata.
To amma a ranar Juma'ar da ta gabata shugaban ƙasar ya gana da wasu gwamnoni a ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki
Daga cikin masu halartar ganawar akwai mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da sauran jami'ai.
Ghana ta yi wa 'yan gudun hijirar Burkina Faso 3000 rajista
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta ƙasar Ghana ta ce ta yi wa 'yan gudun hijirar Burkina Faso fiye da 3000 a ƙasar.
'Yan gudun hijira sun fice daga Burkina Faso ne bayan hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa ƙauyukansu.
Hukumomin Ghana na cewa har yanzu akwai fiye da 'yan gudun hijirar Burkina Faso 1000 da ba a yi wa rajista ba a ƙasar.
Rahotonni na cewa wasu daga cikinsu na zaune ne a wajen 'yan uwa da abokanan arzika.
Ana fargabar cewa ƙungiyoyin jihadi ka iya shiga cikin ƙasar Ghana ta hanyar tuɗaɗar 'yan gudun hijirar Burkina Fason.
To sai dai jami'an tsaron ƙasar na cewa suna tantance duka 'yan gudun hijirar da suka shigar ƙasar.
Mutanen da aka tantancen na daga cikin mutum kusan 8,000 da ke neman mafaka a Ghana.
Hare-haren jami'an tsaron Burkina Faso sun tilasta wa ƙungiyoyin jihadi janye sansanoninsu zuwa kusa da kan iyakar ƙasar da makwabtanta kamar Ghana da Ivory Coast da kuma Benin.
Rwanda ta kori fiye da sojoji 200 daga aiki
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame ya kori fiye da sojojin ƙasar 200, ciki har da manyan jami'an sojin ƙasar daga aiki a rundunar sojin ƙasar.
Manjo Janar Aloys Muganga wanda ya jagoranci rundunar kar-ta-kwana na rundunar sojin ƙasar daga shekarar 2018 zuwa 2019, da kuma Birgediya Janar Francis Mutiganda wanda ya jagoranci wata runduna a ƙarƙashin rundunar tattara bayanan sirri ta ƙasar na daga cikin manyan jami'an soji 14 da korar ta shafa.
Haka kuma Mista Kagame ya amince ta korar ƙananan sojoji 116, tare da dakatar da wasu sojojin 112 daga aiki.
Sanarwar korar sojojin da aka fitar ranar Laraba da safe ba ta fayyace dalilin korar sojojin 244 ba.
Matakin na zuwa ne kwana gudan bayan da shugaban ƙasar ya yi wasu sauye-sauye a rundunar sojin ƙasar, inda ya kori ministan tsaron ƙasar da babban hafsat sojin ƙasar, tare da maye gurbinsu.
Sauye-sauyen da kuma korar jami'an sojojin na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun tsamin dangantaka tsakanin ƙasar da makwabciyarta DR Kongo, inda ƙasashen ke zargin juna da mara wa 'yan tawaye baya.
Tinubu ya rantsar da sabon sakataren gwamnatinsa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayyar ƙasar.
An yi bikin rantsarwar ne a gaban jami'an gwamnatin ƙasar a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Laraba da safe.
Daga cikin waɗanda suka halarci rantsar da sabon sakataren gwamnatin sun haɗar da mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan da gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya Dakta FolasadeYemi-Esan.
A makon da ya gabata ne sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin George Akume da Femi Gbajabiamila a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati
Lai Mohammed ya samu sabon muƙami
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Lai Mohammed shi ne tsohon ministan yaɗa labarai da al'adu na Najeriya
Tsohon ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya samu sabon aiki da wani kamfanin ayyukan kamun ƙafa na ƙasa-da ƙasa, na Ballard Partners.
A wani sakon Tuwita da kamfanin ya wallafa ya ce ya naɗa Lai Mohammed a matsayin jami'in gudanarwa.
Sanarwar ta ce kamfanin na Ballard Partners wanda ke ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke kyautata alaƙa tsakanin ɓangarorin gwamnati a Amurka, ya buɗe reshensa na farko a nahiyar Afirka a Abuja babban birnin Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaban kamfanin Brian Ballard ya ce kamfanin ya bai wa Lai Mohammed aikin ne kasancewar yana ɗaya daga cikin mutanen da ake ganin kimarsu a Najeriya.
Jaridar Punch a Najeriyar ta ambato Lai Mohammed na bayyana jin daɗinsa na kasancewa ɗaya daga cikin ma'aikatan kamfanin Ballard Partners mai kyakkyawan tarihi a ayyukasa a faɗin duniya.
“Na ji dadin fara aiki da kamfanin Ballard Partners tare da buɗe ofishinsa a na farko a Afirka'', in ji Lai Mohammde.
Lai Mohammed dai ya shafe shekara takwas a matsayin ministan yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari.
Jihar Edo ta rage kwanakin aikin gwamnati zuwa wuni uku a mako
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya Godwin Obaseki ya rage kwanakin aikin gwamnti a faɗin jihar daga wuni biyar zuwa uku a mako.
A wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talata ta ce matakin wani ɓanagare ne na rage wa ma'aikata raɗaɗi da matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi zai haifar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “a matsayinmu na gwamnati mai hangen nesa, mun fara duba batun ƙarin albashin ma'aikatan jiharmu daga 30,000 zuwa 40,000 mafi ƙaranci, wanda ya zarta na kowacce jiha a ƙasarmu''.
“Haka kuma muna son tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da biyan wannan kuɗi, yayin da muke fatan ƙara albashin, idan jiharmu ta fara samun kasonta daga kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta tara daga kuɗin cire tallafin man'', in ji sanarwar
Haka kuma gwamnatin jihar ta ce tana sane da irin wahalhalun da matakin cire tallafin man ya haifar wa al'ummar jihar sakamakon ƙarin kuɗin mota da na abinci da ma'aikatan jihar ke fuskanta.
''A don haka ne gwamnatin jiha ke sanar da cewa ta rage wa ma'aikatan jihar kwanakin aikin gwamnati daga wuni biyar zuwa uku, inda za su yi aikin wuni biyun daga gida daga yanzu har zuwa wani lokaci nan gaba'', in ji sanarwar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da wata jiha a ƙasar ke rage adadin kwanakin aikin gwamnati ba, domin rage wa ma'aikata raɗadin cire tallafin man fetur ba.
Ko a farkon makon da muke ciki ma gwamnatin jihar Kwara da ke arewacin ƙasar ta amince da ɗaukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwanakin aikin gwamnati zuwa uku a mako, domin rage wa ma'aikata raɗaɗin da janye tallafin man fetur zai haifar.
Sanarwar ta gwamantin jihar fitar ta umarci shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati da ke faɗin jihar su gaggauta tsara wa ma'aikatansu kwanakin da ya kamata su je aiki
Algeria da Saliyo sun zama mambobi a kwamitin tsaro na MDD
Asalin hoton, Getty Images
An zaɓi ƙasashen Algeriya da Saliyo a matsayin mambobin wuci-gadi a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, bayan wata ƙuri'a da aka kaɗa ranar Talata.
An zaɓi duka ƙasashen biyu ba tare da hamayya ba, waɗanda za su yi wa'adin shekara biyu da zai fara daga ranara 1 ga watan Janairun 2024.
Ƙasashen biyu za su maye gurbin Gabon da Ghana a matsayin mambobin kwamitin na wuci-gadi.
An dai zaɓi ƙasashen Afirkan biyu ne tare da ƙasashen Guyana da Koriya da Kudu da Slovenia.
A wani saƙo da ofishin wakilcin ƙungiyar Tarayyara Afirka a Majalisar Dinkin Duniya ya wallafa a shafinsa na Twitter ya taya ƙasashen murnar zaɓarsu da aka yi
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sabbin ƙasashen biyar da aka zaɓa za su yi aiki da kasashen Ecuador da Japan da Malta da Mozambique da kuma Switzerland a matsayin mambobin kwamitin na wucin-gadi.
Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya mai mambobi 15, shi ke da alhakin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasashen duniya.
Biyar daga cikin mambobin kwamitin wato Amurka da Birtaniya ta Faransa da Rasha da China, na da kujerar dindindin, waɗanda dole sai kowaccensu ta amince kafin ɗaukar kowane irin mataki a kwamitin.
Shugabanni ƙasashen Afirka dai sun jima suna ta kiraye-kirayen samun ƙari a kujerun dindindin na kwamitin, matakin da suke fatan zai sa a samu ƙasashen Afirka cikin masu kujerun na dindindin a kwamitin.
An taɓo batun 'yancin ɗan adam a ganawar Amurka da Saudiyya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Shugaban Amurka Joe Biden da Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken,
ya taɓo batun 'yancin dan Adam yayin ganawar da ya yi da Yarima mai jiran
gadon Saudiyya Mohammed Bin Salman.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin
wajen Amurka, ya ce Mr. Blinken ya jaddada cewa dangantaka tsakanin kasashen
biyu na ƙara ƙarfi musamman a kan batun 'yancin ɗan Adam.
Baya ga batun 'yancin sun kuma tattauana lamarin da ya shafi yauƙaƙa dangantaka tsakinin Saudiyya da Ammurka.
A fannin huldar siyasa kuwa sun tattauna kan dawo da hulɗa tsakanin Saudiyyar da Iran da kuma danganta tsakanin China da Russia sai kuma hula tsakanin Saudiyyar da Isralla.
Tun lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ne dai, Amurka ta fara neman samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Israila da ƙasashen Larabawa.
Sakatare Blinken ya ce ya na ƙoƙarin ci gaba da hakan ne inda a yanzu zai gwada sa'arsa kan Saudiyya ko za ta amince ta fara ɗasawa da Israilar.
Haka kuma ana ganin Washington za ta mayar da hankali kan rikicin Sudan yayin ziyarar ta Blinken.
Mista Blinken ya je Saudiyya ne da zummar ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasarsa da kuma ta Saudiyyar ya biyo bayan rashin fahimtar da ƙasashen suka samu kan farashin mai da kuma kisan gillar da aka yi wa dan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyan da ke Turkiyya.
Bugu da ƙari kuma ziyarar ta biyo bayan dawo da dangantaka ne tsakanin Saudiyya da kuma Iran a kwanakin nan, lamarín da ya sa Iran din sake buɗe ofishinta na Diflomasiyya bayan kwashe shekara bakwai kasashen biyu na zaman doya da manja.
Marabanku
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye, barkan mu da safiyar wannan rana ta Labara.
Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa.