Majalisar dokokin Najeriya ta buƙaci ƙarin wata shida kan wa'adin amfani da tsoffin kuɗi

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. An gano wani birni a Masar da aka kafa a zamanin Romawa

    Masu binciken kayan tarihi a birnin Luxor na Masar sun ce sun gano wani birni da aka kafa a zamanin Romawa.

    Birnin wanda ya samo asali tun ƙarni na biyu da na uku an bayanna shi a matsayin mafi tsufa kuma mafi mahimmanci da aka gano a gabashin kogin Luxor.

    Bayan wasu gine gine, masu binciken sun kuma tono husumiyoyi biyu da aka yi amfani da su wajan ajiye tantabarai ko kurciya .

    Sun kuma gano abin da suka kira wurin da ke sana’ar karafa da ya ƙunshi tukwane da kayan aiki da tsabar kuɗin Romawa.

  3. Dole ƙasashe su magance mace-macen ƙananan yara - WHO

    magani

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta umarci ƙasashe mambobin hukumar da su ɗauki mataki cikin gaggawa kan amfani da guɓatattun magunguna domin rage yawan mace-macen ƙananan yara.

    Tun cikin watan Oktoba, ƙasashe bakwai sun bayar da rahoton samun gurɓatattun magunguna da ke ɗauke da wasu sinadari, waɗanda aka yi su musamman saboda amfani a masa'antu.

    A shekarar da ta gabata, kimanin yara 300 ne 'yan shekara biyar zuwa sama suka mutu a ƙasashen Gambiya da Uzbekistan da Indonesiya bayan shan wani gurɓataccen maganin da ya haifar musu da ciwon ƙoda.

    Bayan faruwar lamarin ne hukumar WHO ta aike da gargaɗi ga ƙasashen duniya, tana mai buƙatarsu da su gaggauta janye magungunan daga kasuwanni tare da ƙara sanya ido domin gano magungunan.

    A yanzu kuma hukumar na kira ga kamfanonin samar da magungunan da su riƙa sayen kayayyakin haɗa maganin daga wuraren da aka tabbatar da ingancinsu, tare kuma da gwada magungunan da adana bayanan gwajin nasu.

    Haka kuma hukumar ta shawarci masu sayar da magungunan da su sayar da magangunan da kawai suke da amincewar hukumomin da suka dace.

    An ɗora alhakin yawan mace-macen kan rashin ingantaccen tsari da rashin dabarun gano illar magungunan da wuri.

    A lokuta da dama kamfanonin da ke samar da magungunan kan musanta cewa magungunan nasu na ɗauke da gurɓatattun abubuwa.

    WHO ta kuma umarci ƙasashe da su zuba kaɗade masu yawa domin lura da kamfanonin da ke samar da magunguna a ƙasashensu.

  4. Jihohi sun yi watsi da ƙudurin bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kai

    Majalisa

    Asalin hoton, FACEBOOK

    Majalisar dokokin Najeriya ta ce majalisun jihohin ƙasar sun amince da ƙudurori 35 na yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska.

    A zamanta na ranar Talata majalisar dattawan ƙasar ta umarci akawun majalisar da ya miƙa ƙudurori 35 daga cikin 44 da aka yi wa gyaran fuska ga shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, domin ya rattaɓa musu hannu.

    Daga cikin ƙudurorin da ba su samu amincewar majalisun jihohin ƙasar ba, har da ƙudurin dokar bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kai a fannin kuɗaɗe.

    Yayin da yake gabatar da ƙudurin Sanata Opeyemi Bamidele ya ce majalisun jihohin ƙasar 27 sun amince da ƙudurorin 35.

    Dan haka ya ce kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar, ƙudurorin 35 sun samu abin da ake buƙata na amincewar majalisun jihohi akalla 24, domin zama doka a ƙasar.

    Majalisar dattawan ta kuma buƙaci majalisun sauran jihohin da ba su riga sun miƙa mata ƙudurorin da suka amince da su, da su yi hakan nan ba da jimawa ba.

  5. An sace jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya a Mali

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya ce an sace wani ma'aikacin jin-ƙai a gabashin ƙasar Mali.

    An sace Mahamadou Diawara - wanda likita ne da ke aiki WHO - ranar Litinin a gundumar Ménaka.

    A wani saƙon Tuwita da shugaban Hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa ya ce ''Mun yi Allah wadai da sace abokin aikinmu Dakta Mahamadou Diawara, da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka yi ranar 23 ga watan Janairu a cikin motarsa a gundumar Ménaka''.

    "Muna kuma aiki tare da hukumomin ƙasar Mali domin binciko wadada suka sace shi tare da tabbatar da cewa ya dawo cikin iyalansa ba tare da ɓata lokaci ba'', in ji Mista Tedros

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Adadin masu amfani da internet a wayoyinsu ya kai miliyan 154.28 a Najeriya - NCC

    waya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce adadin masu amfani da internet a wayoyinsu a ƙasar ya kai miliyan 154.28, ƙarin kashi 37 cikin shekara takwas.

    Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wasu bayanai da ta wallafa a shafinta na yanar gizo

    Bayanan da NCC ta fitar sun nuna cewa a watan Disamban 2015 adadin masu amfani da internet a wayoyinsu miliyan 97.03 ne, amma zuwa Disamban 2022 adadin ya kai miliyan 154.28.

    Bayanan na NCC sun nuna cewa kuɗin shiga da ƙasar ke samu ta ɓangaren harkokin sadarwa ya ƙaru daga kashi 8.50 a shekarar 2015 zuwa kashi 12.85 a rubu'i na uku na shekarar 2022.

    Haka kuma bayanan sun nuna cewa an samu ƙaruwar masu amfani da waya zuwa kashi 116.60 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda adadin yake a 2015.

  7. Tarayyar Turai ta alƙawarta tallafin dala miliyan 102.5 ga ƙasashen tafkin Chadi

    tafkin Chadi

    Asalin hoton, others

    Ƙungiyar tarayyar Turai ta keɓe dala miliyan 102.5 domin gudanar da ayyukan jin-ƙai ga al'umomin da ke buƙatar tallafi a Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru, yayin da ayyukan jin-ƙai ke ci gaba da samun cikas a yankin tafkin Chadi.

    A wata sanarwa ta ƙungiyar ta fitar ta ce rigingimun da yankin ke fuskanta, waɗanda suka shafi fararen hula da dama, sun tilasta wa al'umomi da dama barin muhallansu, da tagayyara rayuwar wasu da dama, da kuma rashin samun abubuwan biyan buƙata na yau da kullum.

    Daga cikin kuɗaden da ƙungiyar ta alƙawarta bai wa ƙasashen, Najeriya za ta samu dala miliyan 34, sai Jamhuriyar Nijar da za ta samu dala miliyan 25, sai Chadi da za ta samu dala miliyan 26.5 sai kuma Kamaru mai dala miliyan 17.

    Kuɗin na daga cikin tallafin dala miliyan 181.5 da ƙungiyar ta ware wa tafkin Chadi da ƙasar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da yankin Sahel a wannan shekara.

    ''Fiye da mutum miliyan 24 ne a cikin ƙasashen tafkin Chadi huɗu ne aka ƙiyasta cewa suna buƙatar tallafi'' kamar yadda wani jami'in EU ya bayyana.

    Ya ƙara da cewa “waɗanann kuɗade za a bayar da su ne ga al'umomin da ke buƙatar tallafi sakamakon yaƙe-yaƙen da ya haddasa rasa muhallai da kuma ƙaruwar yunwa a yankin.

  8. Majalisar dokokin Najeriya ta buƙaci ƙarin wa'adin wata shida kan amfani da tsoffin kuɗi

    Majalisar Dokokin Najeriya

    Majalisar dokokin Najeriya ta yi kira ga babban bankin ƙasar da ya tsawaita wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar zuwa wata shida masu zuwa.

    Majalisar wakilai da ta dattawan ƙasar sun yi kiran ne a wasu mabambantan zama da suka yi ranar Talata.

    Majalisar wakilan ƙasar ta ce idan ƙasa na buƙatar kowane tsarinta ya kai ga nasara, to dole ta yi la'akari da 'yan ƙasa.

    Majalisar ta ƙara da cewa ta damu matuƙa game da yadda wasu 'yan kasuwa ke ƙin karɓar tsoffin takardun kuɗin, yayin da bankuna ke ƙorafi game da ƙarancin sabbin takardun.

    Majalisar wakilan ta buƙaci shugaban ƙasar da ya saka baki game da wannan batu.

    Dan haka ne ma ta kafa wani kwamiti da zai gana da gwamnan babban bankin da sauran daraktocin bankunan ƙasar game da ƙorafe-ƙorafen ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

    A nata ɓangare majalisar dattawan ƙasar ta ce ya kamata a tsawaita wa'adin sakamkon yadda har yanzu bankunan ƙasar ke saka tsoffin takardun kuɗin a na'urorin cirar kuɗinsu ta ATM.

    Majalisar dattawan ta kuma koka game da wahalhalun da 'yan ƙasar ke fuskanta na bin dogayen layuka a bankuna a faɗin ƙasar domin sauya kuɗaɗensu.

  9. Dakarun Najeriya sun kashe 'yan fashin daji uku a Kaduna

    Sojoji

    Asalin hoton, @DEFENSENIGERIA

    Dakarun Najeriya da ke yaƙi da 'yan bindiga a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kuɓutar da mutum 16 da 'yan fashin daji suka sace a lokacin wani hari da suka ƙaddamar a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a yankunan ƙananan Birnin Gwari da Igabi da ke jihar.

    Kwamishinan al'amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana mai cewa dakarun sojin sun amsa kiran da aka yi musu cewa 'yan fashin suna yankin Udawa zuwa Manini da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, inda suka samu nasarar daƙile harin 'yan fashin dajin tare da kuɓutar da mutum 16.

    Ya ƙara da cewa an kai waɗanda suka ji raunuka asibiti domin a yi musu magani.

    Sanarwar ta kuma ce sojojin sun kuma samu wani kira daga ƙauyen Gonar Dakta a yankin ƙaramar hukumar Igabi, inda suka yi wa 'yan fashin dajin kwanton ɓauna, tare da kashe ɗaya daga cikinsu.

    Inda a nan ma dakarun suka kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kai su asibitin sojoji da ke Jaji domin yi musu magani.

    Haka kuma dakarun sojin sun samu bayan sirri game da wasu gungun 'yan fashin daji da ke tafiya a wasu yankunan ƙananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari waɗanda suka yi iyaka da jihar Naija, inda nan take suka far musu tare da kashe 'yan fashin biyu.

    Dakarun sun kuma ƙwato mashina 11, da bindiga ɗaya ƙirar AK-47, da bindigar harba-ruga ɗaya da abin fashewa ɗaya.

  10. Buhari ya ƙaddamar da layin dogo a Legas

    Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    A yau ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da layin dogo, wanda gwamnatin jihar Legas ta ɗauki nauyin ginawa.

    Buhari ya shiga jirgin ƙasar daga tashar Marina zuwa tashar jirgin ƙasa ta National Theatre.

    Ga rahoton Umar Shehu Elleman daga Legas

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton
  11. An sallami manyan jami'an gwamnatin Ukraine daga aiki kan zargin rashawa

    Ukraine officials quit

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu manyan jamian gwamnati a Ukraine sun yi murabus ko kuma an sallame su daga aiki yayin da shugaba Volodymyr Zelensky ke gudanar da wani sauyi mai alaka da yaki da cin hancin da rashawa.

    Gwamnonin wasu yankunan biyar da mataimakan ministoci huɗu sun rasa ayyukansu.

    Waɗanda suka sauka daga mukamansu sun haɗa da babban mai ba shugaba Zelensky shawara da kuma mataimakin ministan tsaron kasar.

  12. Jamus na duba yiwuwar aika wa Poland tankokin ƴaki

    Germany-Poland tanks

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamus ta ce za ta duba cikin gaggawa bukatar da Poland ta gabatar mata na aike mata da tankunan yaki da aka kera a kasar domin ta turawa Ukraine.

    Firaministan Poland Mataiyuz Morawiyishki ya ce yana fatan Jamus za ta mayar martani cikin sauri tare da ba ta damar fitar da takunan yakin samfurin L 2 guda goma sha hudu.

    Wakilin BBC ya ce matakin da Poland ta ɗauka na yin kira ga Jamus a hukumance a kan ta tura mata da tankunan yaki zai kara matsawa shugaban gwamnatin jamus lamba wajan ganin ya yanke shawara.

    Tun farko sakatare janarar na kungiyar tsaro ta Nato Yen Stoltenberg ya ce yakin da ake yi a Ukarine ya kai wani mataki kuma ya kamata mambobin kungiyar su taimaka wa Ukraine da manyan makamai.

  13. Majalisar dokokin Najeriya ta gayyaci shugabannin bankuna saboda karancin naira

    NATIONAL ASSEMBLY

    Asalin hoton, NATIONAL ASSEMBLY

    Majalisar Dokokin Najeriya a ranar Talata ta gayyaci shuagabannin bankunan kasuwanci domin bayyana a gabanta a ranar Laraba kan karancin sabbin takardun kuɗi da ake fuskanta.

    Babban Darekta kuma Shugaban Bankunan karkashin kwamitin bankuna, za su haɗu da kwamitin wucin gadi na Majalisar da shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado-Doguwa ke jagoranta.

    A wani zama da majalisar ta yi a yau Talata, ta yanke shawarar gayyato bankunan domin su zo gabanta su yi bayani kan matsalolin ƙarancin kuɗi da ake samu daga Babban Bankin Najeriya, inda daga baya za ta gayyato shugabannin na CBN domin zuwa amsa tambayoyi.

    Majalisar ta kuma bukaci a tsawaita wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da wata shida.

  14. An gudanar da taron wayar da kai da tattauna hanyoyin magance matsalolin ilimi a Kano, Daga Zaharaddeen Lawan

    Yayin da ake ci gaba da gabatar da taruka game da ranar ilimi ta duniya, a jihar Kano, cibiyar karfafa gwiwar ƴan mata masu tasowa don neman ilimi ta shirya taron wayar da kai tare da tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin da ilimi ke fama.

    Taken taron ranar ilimi ta duniya na bana shi ne bai wa harkar ilimi kulawar da ta dace don ciyar da al'umma gaba.

    Ku danna kasa don sauraron rahoton wakilinmu na Kano Zahraddeen Lawan.

    Bayanan sautiKu danna hoton sama don sauraron rahoton
  15. Tsananin sanyi ya kashe mutum 124 a Afghanistan

    Afghanistan is enduring its harshest winter in years

    Asalin hoton, AFP

    Akalla mutum 124 sun rasa ransu sakamakon tsananin sanyi a Afghanistan a makonni biyu da suka gabata, a cewar jami'an Taliban.

    Mai magana da yawun Ma'aikatar Agajin ƙasar , ya ce sama da dabbobi 70,000 ne kuma suka mutu a wani yanayi na tsananin sanyi da ba a ga irinsa ba cikin shekara goma.

    Kungiyoyin bayar da agaji da dama sun dakatar da ayyukansu a baya-bayan nan bayan haramta wa matan ƙasar aiki da kungiyoyi masu zaman kansu da Taliban ta yi.

    Wani minista a gwamnatin Taliban ya ce duk da samun waɗanda suka mutu, ba za a janye haramcin ba.

    Muƙaddashin Ministan Agaji, Mullah Mohammad Abbas Akhund, ya faɗawa BBC cewa dutsar kankara ta mamaye yawancin yankuna a ƙasar, inda aka aike da jirage masu saukar ungulu don zuwa ceto mutane, sai dai, jiragen basa samun damar sauka a yankuna da ke da tsaunuka ba.

  16. Faɗa ya ɓarke a gabashin Kongo duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

    The conflict has triggered a humanitarian crisis

    Asalin hoton, AFP

    Sabon faɗa ya ɓarke a gabashin Jamhuriyar Dimokuraddiyar Kongo duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta tsakanin gwamnati da kuma 'yan tawaye.

    Rahotanni sun ce faɗa tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen M23 ya janyo mutane sun tserewa gidajensu a ranar Talata.

    Wani ɗan jarida ya faɗawa BBC da safiyar Talata cewa lamarin ya ɗaiɗaita mutane da dama a garin Mweso.

    Sojoji basu ce komai ba kan sabon faɗan da ya ɓarke, sai dai, wani mai magana da yawun 'yan tawayen, ya zargi dakarun gwamnati da far wa wurarensu a kokarinsu na janyewa saboda yarjejeniyar da aka cimma a Luanda, babban birnin Angola.

    Shugaba Félix Tshisekedi, ya bayyana a mako da ya gabata cewa 'yan tawayen basa ficewa daga yankin, inda suke ƙara girke mutanensu a wasu yankuna.

    Sai dai 'yan tawayen sun zargi shugaba Tshisekedi da cewa bukatarsa kawai ita ce ta wargaza su maimakon cimma yarjejeniyar zaman lafiya kan rikicin.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 400,000 ne suka tserewa gidajensu a rikicin tun shekara da ta gabata.

  17. Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko-Haram da ISWAP

    Troops

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram da ISWAP da dama a ranar Litinin, bayan daƙile wani yunkurin kwantan-ɓauna da suka so yi wa sojojin a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri na jihar Borno.

    A wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na twita, ta ce ta kuma ƙwato makamai da dama da suka haɗa da jigidar harsasai da kuma babura.

    Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Faruk Yahaya, ya yabawa dakarun saboda jajircewarsu, inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa har sai an kawo karshen 'yan tada-ƙayar-bayan da kuma wasu ayyukan bata gari a yankin arewa maso gabas.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Fadawan Shehun Borno uku sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota

    ROAD CRASH

    Asalin hoton, OTHER

    Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta tabbatar da cewa wani hatsarin mota ya rutsa da rayukan wasu fadawan Shehun Borno guda uku, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

    Kwamandan Hukumar a jihar ta Borno, Utten Iki Boyi, ya shaida wa Jaridar Daily Trust a Maiduguri da safiyar ranar Talata cewa mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, amma an ceto uku, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa.

    A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik lokacin da motar ta yi dungure sannan ta kama da wuta.

    Ya ce nan da nan suka tura jami'an su zuwa wajen da lamarin ya faru, inda aka samu mutum uku sun ƙone kurmus har ba a iya gane su.

    Sai dai ya ce an samu nasarar ceto mutum uku inda aka kai su zuwa babban asibitin Beneshiek don yi musu magani.

  19. UNICEF ya yi alkwarin tallafa wa ilimi a yankin arewa maso gabashin Najeriya

    UNICEF

    Asalin hoton, OTHER

    Asusun Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya yi alkwarin ci gaba da tallafawa bangaren ilimi a arewa maso gabas ta yadda yara da yawa za su samu damar zuwa makaranta.

    Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms Christian Munduate, ce ta bayyana hakan lokacin da ta kai ziyara Jami'ar AUN da ke Yola a ranar Litinin don gudanar da shirin tallafawa yara 100 da basa zuwa makaranta da abinci da kuma abubuwnan karatu.

    Ta bayyana kokari da suke na ganin ƙarin yara sun samu damar karatu ta Jami'ar da kuma sauran makarantu a faɗin yankin.

    Munduate ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su bijiro da shirye-shirye da za su kawo ci gaban ilimi a kananan matakai, inda ta nuna bukatar ganin hobbasar bangarori masu zaman kansu saboda ci gaban ilimin yara ƙanana.

    Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Ms Christian ta ce akwai bukatar bai wa yara ilimi saboda idan ba a basu ba, za su iya zama kalubale a nan gaba.

    Wakiliyar ta UNICEF ta shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su ci gaba da zuwa makaranta domin samun ilimi saboda zai zamanto mai amfani a garesu da iyalansu da kuma al'umma.

  20. Kotu a Rwanda ta ɗaure tsohon minista kan zargin rashawa

    Rwanda Government

    Asalin hoton, Rwanda Government

    Wata babbar kotu a kasar Rwanda ta yanke wa wani tsohon ministan matasa da al'adu ɗaurin shekaru biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa, inda ta tsawaita hukuncin da aka yanke masa a baya da shekara guda.

    Hukuncin asali, wanda ya zo a bara, a kan Edouard Bamporiki, wani lamari ne da ba kasafai ake samunsa ba na wani babban jami’in da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar.

    A watan Mayun da ya gabata ne aka dakatar da shi daga mukaminsa, inda aka masa ɗaurin talala yayin da ake bincikensa da laifin almundahana. Ya kasance cikin ɗaurin talalal har zuwa lokacin da aka yanke hukuncin.

    Bamporiki ya amsa laifin da ake zarginsa da shi a shafinsa na Twitter, sannan ya roki shugaba Paul Kagame da ya gafarta masa, amma a watan Satumba wata kotu ta yanke masa hukuncin shekaru hudu - wanda ya daukaka kara.

    A ranar Litinin, alkalin wata babbar kotu a Kigali babban birnin kasar, ya ce dokar ta yi aikinta saboda hakan ya zama izina ga wasu.

    Mai wakokin baƙan mai shekara 39 da haihuwa wadda kuma mai shirya fina-finai a baya, ya kasance babban mai goyon bayan shugaba Kagame da jam'iyya mai mulki kuma ya yi fice cikin lokaci kankani.

    Lauyan sa, Evode Kayitana, ya shaida wa BBC cewa ba su yanke shawara kan ko za su daukaka kara ba.