An rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kan yada ake shirin rantsar da Biden a Amurka da wasu batutuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • Biden ya isa Majalisar Tarayyar Amurka don rantsar da shi
    • Baƙi na ci gaba da halartar wurin bikin rantsar da Joe da Kamala
    • An rantsar da Kamala Harris a matsayin mataimakiyar shugaban Amurka
    • An rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46 mai cikakken iko
    • Joe Biden ya wallafa saƙon Twitter na farko bayan zama shugaban ƙasa
    • Harris ta yi wa Pence rakiya
    • Buhari ya yi wa Biden da Harris murna

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Hotuna: Ziyarar Biden a maƙabartar Arlington

    Shugaba Biden tare da wasu tsofaffin shugabannin Amurka sun ziyarci maƙabartar Arlington, wurin da aka rufe dubban mutane musamman waɗanda suka yi wa ƙasar gwagwarmaya.

    Biden da Harris da wasu tsofaffin shugabannin Amurka sun ajiye furanni kan kabari na musamman da aka yi domin girmama sojojin da suka mutu yayin kare ƙasarsu amma ba a ga gawarsu ba.

    .

    Asalin hoton, Getty Images.

    .

    Asalin hoton, Reuters

    .

    Asalin hoton, Reuters

    .

    Asalin hoton, EPA

  3. LABARAN WASANI NA YAMMA - 20/01/2021

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
  4. Biden ya isa maƙabartar Arlington

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ayarin motocin Shugaban Amurka Joe Biden ya isa maƙabartar Arlington da ke Virginia.

    Dakarun ƙasar za su harba bindiga sau 21 a wurin domin alamta rantsar da sabon shugaban ƙasa.

    Biden da Harris da tsofaffin shugabannin Amurka Bush da Clinton da Obama da iyalansu za su ajiye furanni kan kabarin girmama sojojin da suka mutu yayin kare ƙasarsu amma ba a ga gawarsu ba.

  5. Buhari ya yi wa Biden da Harris murna

    .

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa sabon Shugaban Amurka Joe Biden da kuma mataimakiyarsa, Kamala Harris, murna bayan an rantsar da su a yau.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban Najeriyar kan kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce yana fatan mulkin sabon shugaban da mataimakiyarsa zai zama wata alama ta haɗin kai mai ƙarfi da kuma goya wa Najeriya baya da kuma nahiyar Afrika.

    Shugaba Buharin ya kuma ce yana fatan mulkin Biden zai ƙara danƙon zumuncin da ake da shi a yanzu da kuma aiki tare wurin yaƙi da ta'addanci da sauyin yanayi da talauci da kuma ƙara haɓaka tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen da kuma faɗaɗa kasuwanci.

  6. Daga jihar Florida kuma..

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Jirgin da ya ɗauko tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump daga Washington ya sauka Florida daf da lokacin rantsar da Shugaba Biden.

    Ɗumbin magoya bayansa sun tarbe sa a lokacin da ya isa, inda ake ta waƙe-waƙe da kiran cewa "har yanzu shugaban ƙasa ta ne" da kuma "Trump ne ya ci zaɓe".

    Mista Trump ya ƙare mintuna 30 ko sama da haka na shugabancinsa a cikin filin wasan lambunsa wato Golf.

    Yanzu dai Trump ya zama ɗan ƙasa mai zaman kansa wanda za a ci gaba da shari'ar tsige shi a Majalisar Dattawan Amurka.

    .

    Asalin hoton, Reuters

  7. Harris ta yi wa Pence rakiya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence da matarsa da kuma Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris da mijinta sun tsaya kan matattakalar shiga Capitol inda suke wasa da dariya yayin da suke raka Mike Pence.

    Tun bayan da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya karya al'adar Amurka ta ƙin amincewa ya halarci bikin rantsuwar sabon shugaban ƙasa - mataimakinsa Mike Pence da iyalinsa suka sha alwashin wakiltar gwamnati mai barin gado.

    Ba za a manta da wannan hoto ba da wannan lokaci ba a tarihin Amurka

  8. Joe Biden ya wallafa saƙon Twitter na farko bayan zama shugaban ƙasa

    Shugaban Amurka Joe Biden, ya wallafa saƙonsa na farko a shafinsa na Twitter wanda aka tanada domin shugaban ƙasar Amurka.

    A saƙon da ya wallafa, ya bayyana cewa "babu batun ɓata lokaci idan ana maganar rikicin da muke fuskanta. Zan tafi ofishin shugaban ƙasa nan take domin fara aiki da kuma kuma kawo sauƙi nan take ga Amurkawa".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Bidiyo: Wane ne Joe Biden?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  10. Biden ya kammala jawabinsa na farko

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Joe Biden ya kammala jawabinsa na farko a matsayin shugaban ƙasar Amurka.

    Jawabin nasa ya fi mayar da hankali ne kan batun gina ƙasa da haɗin kai.

  11. Tarihin Kamala Harris

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
  12. Labarai da dumi-dumi, Joe Biden na jawabi a halin yanzu

    Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden na jawabinsa na farko a halin yanzu a matsayin shugaban Amurka na 46.

    Shugaba Biden ya gode wa tsofaffin shugabannin Amurka da suka halarci bikin rantsuwar.

    Haka kuma Biden ɗin ya ce ya yi magana da tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter mai shekara 96 inda ya ce ya gaishe shi ta waya bisa aikin da ya yi wa ƙasar.

    Wanda Biden ya gada, Donald Trump ya zaɓi cewa ba zai halarci wannan bikin rantsuwar ba.

  13. Labarai da dumi-dumi, An rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46 mai cikakken iko

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da Joe Biden a matsayin Shugaban Amurka na 46.

    Alƙali John Roberts ne ya rantsar da shi. Mista Joe ya gaji Donald Trump.

  14. Labarai da dumi-dumi, An rantsar da Kamala Harris a matsayin mataimakiyar shugaban Amurka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da Kamala Harris a matsayin mataimakiyar shugaban Amurka.

    Kamala Harris ce baƙar fata ta farko kuma mace ta farko da ta taɓa riƙe irin wannan muƙamin a Amurka.

    Harris dai ta gaji Mike Pence a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasar, haka kuma Sonia Sotomayor ce alƙalin da ta rantsar da ita.

  15. Baƙi na ci gaba da halartar wurin bikin rantsar da Joe da Kamala

    Shugaban masu rinjaye a Majlisar Dattawan Amurka, Mitch McConnell da kuma tsohuwar Sakatariyar Sufuri, Elaine Chao sun isa wurin bikin rantsar da Joe Biden da Kamala Harris.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An hango Sanata Bernie Sanders riƙe da waya a hannunsa a harabar majalisa.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton da kuma uwar gidansa Hillary Clinton sun isa wurin.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Nan da sa'a ɗaya Kamala Harris za ta zama mataimakiyar shugaban Amurka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran cewa nan da sa'a ɗaya Kamala Harris za ta zama mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka.

    Alƙalin Kotun Ƙolin ƙasar, Sonia Sotomayor ce za ta rantsar da ita wanda hakan wani abin tarihi ne ta hanyoyi da dama.

    Kamala za ta kasance baƙar fata ta farko kuma ƴar Kudancin yankin Asia kuma mace ta farko da za ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa kuma Alƙali mace ƴar yankin Latin Amurka za ta rantsar da ita.

    An bayyana cewa Harris ta buƙaci Sotomayor a matsayin alƙalin da za ta rantsar da ita.

    Shi kuma Biden ya zaɓi Alƙali John Roberts.

  17. Labarai da dumi-dumi, Biden ya isa Majalisar Tarayyar Amurka don rantsar da shi

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Joe Biden da uwar gidansa Jill Biden sun isa harabar Majalisar Amurka inda ake sa ran za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban nan da lokaci kaɗan.

    Za a fara rantsar da mataimakiyar Biden, Kamala Harris sa'annan a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

    Biden ya isa harabar Majalisar cikin matuƙar tsaro inda ɗimbin ayarin motoci ke biye da shi gefe da gefe

    .

    Asalin hoton, Reuters

  18. Labarai da dumi-dumi, Tsofaffin Shugabannin Amurka sun fara isa wurin bikin rantsu

    Tsoffin shugabannin Amurka da matansu sun fara isa harabar Majalisar Tarayyar Amurka domin rantsar da sabon shugaban ƙasar.

    Bill Clinton da uwar gidansa Hillary da Barack Obama da uwar gidansa Michelle sun isa Capitol.

    Ana sa ran Tsohon Shugaba George Bush da uwar gidansa Laura za su halarci bikin

    Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter domin nuna goyon bayansa ga Joe biden gabannin rantsar da shi

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Shirye-shiryen rantsar da Biden a cikin hotuna

    BIDEN

    Asalin hoton, Reuters

    BIDEN

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jami'ai na tabbatar da tsaro a ginin Capitol
    BIDEN

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani bangare na Fadar White inda aka tsaurara matakan tsaro
    BIDEN

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ginin da ake ziyarta domin jimamin wadanda korona ta kashe
    BIDEN

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A garinsu mahaifiyar Kamala Harris a Indiya ma ana ta bukukuwan murnar wannan rana
  20. Labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifa a sama domin sauraron labaran duniya cikin minti guda