Yadda ƴan fashi suka tare motar ɗaukar kuɗi ta banki da kai mata hari a Ibadan

Armed robbers attack bullion van in Ibadan

Asalin hoton, Tvc News

'Yan sanda a jihar Oyo sun tabbatar cewa akalla mutum uku ciki har da 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu bayan da wasu 'yan fashin da aka ce sun kai su goma suka sace wata motar ɗaukar kudi a yankin Idi-Ape na birnin Ibadan.

Rundunar 'yan sandan ta ce motar ta dauko kudi ne yayin da 'yan fashin suka kai mata hari a birnin da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Daga nan ne 'yan fashin suka buɗe wa jami'an 'yan sandan da ke raka motar wuta, inda bayan haka suka tafi da kudaden da kawo yanzu ba a san yawansu ba.

Kwamishinar 'yan sanda a jihar Oyo Ngozi Onadeko ta tabbatar da aukuwar fashin ta kuma ce daya daga cikin 'yan sandan ya sami raunuka daga harbin da aka yi masa kuma ya cika daga baya a asibiti.

Kwamishinar wadda ta gana da manema labarai yayin da ta ziyarci wurin da fashin ya auku, ta kuma tabbatar da cewa wani dan sanda ya harbe daya daga cikin 'yan fashin har lahira yayin da suke musayar wuta.

One of di cars wey di robbers attack

Asalin hoton, TVC News

Bayanan hoto, Daya daga cikin motocin da 'yan fashin suka kai ma hari

Yayin da ake musayar wuta wani harsashi ya kashe wani mutumin da ke wucewa a wurin. Wasu mutum hudu ciki har da 'yan sanda biyu na asibiti, kamar yadda 'yan sansa suka ce.

Sai dai gwamnan jihar ta Oyo Seyi Makinde ya mayar da martani kan fashin da ya auku a unguwar Idi-Ape ta birnin Ibadan.

Ga abin da ya ce a wani sakon Twitter, inda ya mika gofiyarsa ga wadanda suka kira lambar neman taimako ta 615 a jihar domin sanar da jami'an tsaro hali da ake ciki:

"Za mu ci gaba da inganta tsarin samar da tsaro da saurin kai dauki ta hanyar amfani da kayan aikin da muke da su a matakin gwamnatin jiha."

Ya kuma ce, "muna mika godiyarmu ga dukkan jami'an tsaron da ke ci gaba da sadaukar da kansu domin kare mu."

Short presentational grey line

Wasu lokuta da 'yan fashi suka kai hari

Fashin Osun

Osun Bank robbery: Ikire, Apomu bank robbers kill pipo, attack police station

Asalin hoton, File foto

Bayanan hoto, An kai wa jihar Osun hari inda 'ya fashi suka afka wa wani banki

A bara, wasu 'yan fashi sun kai hari cikin wasu birane biyu na jihar Osun inda suka afka wa wasu bankuna biyu.

Baya ga bankunan, 'yan fashin sun kai wa wani ofishin 'yan sanda hari ranar Laraba 2 ga watan Yunin 2021.

Rahotanni na cewa 'yan fashin sun isa garuruwan ne da misalin karfe 5.30 zuwa 6 na yamma kuma sun fara harbin mai uwa da wabi, inda suka rikita al'ummar yankin.

Fashin Offa

Two Offa robbery suspects wey Police arrest

Asalin hoton, Nigeria Police Force

Bayanan hoto, Wasu wadanda suka fito fili suka ce sune jagororin 'yan fashin na Offa

A watan Afrilun 2018, wasu 'yan fashi sun kai hari kan wasu bankuna a karamar hukumar Offa ta ihar Kwara a arewacin Najeriya.

Fashin ya kasance mai mumunana tasiri wanda ya lakume rayuka fiye da 30 a wancan lokacin.

'Yan sanda sun kama biyar daga cikin 'yan fashin da kuma wasu su 17 da ake tuhuma da hannu a harin da suka kai kan bankunan kuma tuni an gurfanar da su a kotu.