Yadda mutane suke kona robobi domin dumama jikinsu saboda sanyi a Afghanistan
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Yanayin sanyi da aka soma shiga a Afghanistan ya sa ana gaggauta kai kayan agaji kasar.
Tun lokacin da Taliban ta kwace iko, da kuma takunkuman da aka saka mata, tattalin arzikin kasar ya yi matuƙar tabarbarewa.
Faduwar gwamnatin baya a kasar Afghanistan da kuma matakin da kasashen Yamma suka dauka na janye tallafin da suke bai wa kasar sun sa mutane sun rasa aikin yi.
Kananan yara miliyan daya suna cikin hatsarin kamuwa da tamowa. Yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a kai agajin gaggawa na jinkai kasar.