Bidiyo: Makahon da ya yi fice a gyaran injin janareta
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Hausawa kan ce himma ba ta ga rago, wannan wani mutumi ne da ke zaune a birnin Kano wanda tawayar da yake da ita ta makanta ba ta hana shi zagewa ya nemi na kansa ba.
Dubban masu larura irin tasa musamman a arewacin Najeriya kan rungumi harkar bara ne a duk lokacin da suka samu kansu a irin wannan hali, sai dai Malam Garba Abdullahi ya ce babban fatansa shi ne ganin ya samu na kansa.