Binciken BBC kan masu ikirarin Jihadi na Mocimboa a Mozambique

Bayanan bidiyo, Binciken BBC: Masu ta da ƙayar baya na Mocimboa a Mozambique

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Satar mutane da sare masu kai da ƙona gidaje sun zama ruwan dare da wata ƙungiyar masu ta da ƙayar baya ke aiwatarwa a Cabo Delgado a arewacin Mozambique.

Tun shekarar 2017, sun ƙaddamar da ɗaruruwan hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da tilastawa a ƙalla 700,000 barin muhallansu.

Ba a da wata masaniya kan dalilin wannan rikici. Su waye waɗanann mutanen kuma me suke so? Sashen binciken Africa Eye na BBC ya bi sahunsu a ƙasa da a intanet.