Sale Mamman: Ina asibiti aka gaya mini Buhari ya sauke ni daga minista

Bayanan bidiyo, Hira da Sale Mamman tsaohon ministan lantarki na Najeriya

Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Sale Mamman:

Tsohon ministan da ke lura da harkokin wutar lantarkin Najeriya, Injiniya Sale Mamman, ya ce yana asibiti domin a duba lafiyarsa ya samu labarin Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shi daga mukaminsa.

Sai dai tsohon ministan, wanda ya shaida wa BBC Hausa hakan, ya musanta labarin da ke cewa ya yanke jiki ya fadi an garzaya da shi asibiti bayan samun labarin sauke shi daga mukaminsa.

A cewarsa: “ Ni dai na san lafiyata ras, ko da a lokacin da na samu labarin [sauke ni daga minista] na je asibiti duba jikina, a wannan lokaci ake gaya min wannan labari. Har wadansu ba so a gaya min cewa abu ya faru don kada hawan jini ya same ni.”

Injiniya Mamman ya ce ‘yan siyasa ne suka kitsa labarin cewa ya yanke jiki ya fadi yana mai cewa ya bar su da Allah.

Tsohon ministan ya ce cire shi daga kan mukamin bai bata masa rai ba domin kuwa lokacin da aka nada shi bai taba zaton zai zama minista ba.

Ya ce zai ci gaba da harkokin siyasa da goyon bayan Shugaba Buhari a jiharsa ta Taraba.