An kashe 'mutane da dama' a sabon rikicin da ya ɓarke a Jos

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a jihar ta Filato da ke tsakiyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane da dama sakamakon harin da wasu "ɓata-gari" suka kai a kauyen Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos Ta Arewa ranar Litinin da daddare.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Mr Dan Manjang, wanda ya shaida wa BBC Hausa wannan labarin, ya ce kawo yanzu rundunar ƴan sanda ta tabbatar masu da cewa mutum 18 aka kashe a harin.
Sai dai wasu kafafen watsa labaran Najeriya sun ce an kashe fiye da mutum 30 yayin harin.
Mr Manjang ya kara da cewa ɓata-garin "sun kona wadanda za su kona suka na kashewa. Akwai wata gada ma da aka yi ta da katako take hada kauyen zuwa wasu yankunan, sun lalata ta don kada su bari jami'an tsaro su ketara su je wannan kauyen."
A cewarsa, an kama mutum goma da ake zargi da kai harin kuma tuni aka soma gudanar da bincike.
Sai dai ya ce yanzu haka ana zaman zulumi a yankin, ko da yake hukumomi suna bai wa jama'a hakuri don kada su tayar da tarzoma.
An sanya dokar hana fita
Gwamnatin Jihar Filato ta sake saka dokar hana fita kwatakwata a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Dr Makut Macham, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Matakin na zuwa ne bayan harin ƙauyen Yelwa Zangam da ke gundumar Zangam ta jihar.
A cewar Gwamna Simon Lalong, dokar hana fitar ta awa 24 za ta fara aiki ne daga 4:00 na yammacin Laraba 25 ga watan Agusta har zuwa sanarwa ta gaba.
Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako biyu bayan wasu matasa da ake zargi 'yan kabilar Iregwe ne sun kashe mutum 25 matafiya Musulmai da ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya daga Jihar Bauchi bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci wanda Sheikh Dahiru Bauchi yake gudanarwa.
Kisan ya sa gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi uku ciki har da Jos ta Arewa kafin daga baya a sassauta ta. Gwamnatin ta ce har yanzu dokar hana fita daga 6:00 zuwa 6:00 na safe tana nan daram Bassa da Jos ta Kudu.










