Mutumin da ya bude kamfanin yawon bude ido na masu fama da nakasa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
An gano cewa Shin Hyunoh yana fama da larurar CMT, wata cuta ce ta zaizayewar jijiyoyi, lokacin yana da shekaru hudu a duniya.
Shekaru 28 bayan haka, Shin, wanda yake kan keken guragu, ya bude kamfanin tafiye-tafiye na musamman.
Ya tsara kamfanin tafiye-tafiye na musamman din ne domin saukakawa masu fama da larura wajen yin abubuwan da suke son yi.