An kubutar da wasu daga daliban Kaduna da aka sace
Gwamnatin Kaduna ta ce jami'an tsaro sun kubutar da 180 daga cikin daliban kwalejin gwamnatin tarayya da aka yi garkuwa da su a Jihar a Kaduna, sai dai har yanzu ba a san yawan daliban da aka sace ba.