Bidiyon hirar Masari kan inda aka boye daliban makarantar Kankara

Bayanan bidiyo, Bidiyon hirar Masari kan inda aka boye daliban makarantar Ƙanƙara

Latsa hoton sama domin sauraren hirar

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya Aminu Bello Masari ya ce sun san inda aka ɓoye ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza ta Ƙanƙara da aka sace ranar Juma'ar da ta gabata.

Ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa ranar Laraba inda ya ce a halin yanzu suna da kyakkyawan yakini da bayanin inda yaran suke.

Gwamnan ya ce a yanzu haka bayanai sun nuna cewa yaran suna cikin dajin jihar Zamfara, "kuma ko ba dukkansu ba to mafi rinjayensu dai suna can wajen."

Ya ƙara da cewa a yanzu ƙoƙarin da gwamnati ke yi shi ne na a karɓo yaran ba tare da an yi amfani da bakin bindiga ba saboda kar a ji wa wsu rauni ko a kashe wasu bisa tsautsayi.

"A yanzu haka jami'an tsaro sun zagaye dukkan waɗannan wurare da ake zaton yaran suna can," in ji Masari.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Katsinan ta ce yara 333 ne suke hannun ƴan bindigar da suka sace su ranar Juma'a da daddaren, a garin Ƙanƙaran da ke kusa da dajin Rugu da ya yi ƙaurin suna wajen zama maɓoyar ƴan fashin da suka addabi jihar Katsina da maƙwabtanta.

Amma wasu kafofin suna cewa yawan yaran da aka sace ɗin ya haura 600, duk da cewa wasu sun samu kuɓuta a ranar da abin ya faru.

Sai dai bayan da BBC ta tambayi gwamnan iya adadin da a yanzu suka san cewa suna hannun maharan, sai ya ce suna ci gaba da tattara bayanai daga iyayen da suke lunguna da saƙo da ake wahalar samunsu, "yanzu dai yaran za su kai daga 333 zuwa 400.