Bidiyon Ku san Malamanku da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Maiduguri

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku san Malamanku tare da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Sheik Sharif Ibrahim Saleh ya ce ya rubuta littatafai fiye da 400 na addinin Musulunci da hannunsa.

Malamin, wanda jigo ne a ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar ya faɗi hakan ne a wata hira d aya yi da BBC Hausa a sabon shirinmu na musamman mai taken ''Ku San Malamanku''.

Sheikh Shariff Saleh shi ne shugaban kwamitin fatawa ta addinin Musulunci a Najeriya.