Hotunan gasar dabbobi masu ban dariya na 2020

Asalin hoton, John Carelli/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
Za ka ji kana sha'awar ajiye dabba a gidanka bayan kallon wadannan hotuna, (in baka da ko daya a gida).
Gasar hotunan dabbobi masu abin dariya ta wannan shekarar za ta kawo muku dabbobin da ke abubuwan ban dariya.
Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna daga cikin wasu jerin hotunan kyautar:
Sarauniyar barkwanci

Asalin hoton, Anne Lindner/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
"Ina ganin wani abu mai kyau sama da ka ga karya na hamma," Anne Linder ta rubuta a kan wannan karyar.
Gasar dai a bude take ga duk wani mai kiwon dabba, babu shamaki kan cewa sai mai ƙwarewa kan ɗaukar hoto.
Abin da ake buƙata kawai wasu kudade ne na shiga, tare da wasu ƙirƙire-ƙirƙiren yadda za a iya gabatar da gasar. Ka'idar ita ce ba a yarda ka sanya wa dabbobin kaya ko gilashi ko hula ba.
Hoto daga cikin kwalbar abinci

Asalin hoton, Candice S/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
Mene ne ya faru a gaba? Abin taƙaici, ba mu sani ba ko wannan karen ya ci wannan jarrabawa ya iya riƙe kansa.
Wanda ya yi nasarar zai karɓi fam 3,000 da aka sanya kyauta, kuma za a miƙa wa kungiyar Blue Cross mai taimaka wa dabbobi da ke Burtaniya.
Manyan 'yan rawa

Asalin hoton, Ian McConnell/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
A shirye-shiryen kasuwanci ana cewa ka da ka yi aiki da dabbobi, sai dai wannan magen kamar an halicce ta ne don rawa a kan dandali. Abin barkwanci.
Lokacin hutu ne yanzu

Asalin hoton, Robert Prat/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
Ba abin da za ka gani a nan sai wata akuya zaune a kan lilon hutawa tana tauna ganye. Hutu zalla.
Riƙe da kyau

Asalin hoton, Karen Hoglund/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
Ka da ka kwaikwayi haka a gida! Za mu iya cewa muna da tabbacin wannan karen bai samu horaswa ba kan tuƙi.
Bugu da ƙari Motar a tsaye take.
"Abin da ake iya gani a wannan hoto miji ne da abin ƙaunarsa a zaune a bayan kujera. Ina riƙe da igiyarsu su duka,'' in ji Karen Hoglund daga Amurka.
Killace kai

Asalin hoton, Ilana Rose/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
Kamar yadda mai karen ya ce, "Wannan ne irin halin da muke ciki a wannan shekarar bayan dokar kullen Covid-19 a fadin duniya".
Doki na musamman

Asalin hoton, Daniel Szumil/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
"Dokin ya kama yi mani dariya, lokacin da na koma mota sai na duba madubi ko da wani abu a fuskata," in ji Daniel Szumilas.
Za a sanar da hoton da ya lashe gasar ta wannan shekarar a ranar 19 ga watan Nuwamba.
Dabba mai abin dariya

Asalin hoton, Elke V/Mars Petcare Comedy Pet Photo Awards
An ceto Noodles daga wajen wani wahalar da dabbobi a Sifaniya aka kuma kai ta Jamus lokacin tana da wata bakwai.
"Wani lokacin tana da abin dariya, ba ta da ɓoye-ɓoye, ƙawa ce ta arziki, ga abin dariya duk da cewa wani lokaci ba ta san tana yi ba," in ji Elke Vogelsang.











