Mai dalilin aure ta ce matasan Kano sun fi rububin matan da ke da abun hannunsu
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar:
Masu dalilin aure sun gano cewa matasa na nuna sha'awar auren matan da ke da gidan kansu, yayin da su kuma matan suka fi sha'awar auren masu aikin kaki kamar sojoji da kwastam.
Khalifah Dokaji ya tattauna da Hajiya Amina Ahmad mai dalilin aure da ke zaune a jihar Kano, wadda ta shafe sama da shekaru arba'in tana hada auren.
A cikin hirar ta ce ana zuwa gidanta a ce mata ana son mace - budurwa ko bazawara ko juya ko sakin wawa ko kuma mai gidan kanta.
''Yawanci mazan da suka fi zuwa neman auren shekarunsu na farawa ne daga 30 har zuwa sama da 40, amma abin da zai ba ka mamaki yawanci mazan sai su ce sun fi son mace mai gidan kanta.
''Ka san an san yawanci mata masu gidan kansu matan masu kuɗi ne da aka mutu aka bar musu dukiya,'' in ji Hajiya Amina.
''Ana kuma son mace juya''
Hajiya Amina ta ce baya ga haka ana kuma yawan nuna son mace doguwa baƙa, ko sakin wawa sai kuma wacce ba ta haihuwa, ''an ma fi son juya da ba ta haihuwa.''
''Idan na tambaye su me ya sa suka fi son juya sai su ce ra'ayi kawai. Masu ɗamara ma suna zuwa amma ba sosai ba.
''Su kuma matan sai ka ji sun zo nan suna cewa sun fi so a samo musu kwastam ko jami'an hukumar shiga da fice ko soja ko ƴan sanda.''
Ta ci gaba da cewa to da ƙyar dai aka samo wa wasu mata masu irin waɗannan ɗin, ''amma kuma tsofaffi ne sai matan suka ce ba sa so,'' in ji Hajiya Mai Dalilin Aure.
Tsarin da ake bi
Matar ta ce kafin a fara komai sai ka cike fom da take sayarwa naira 1,000, idan kuma amma ga marasa ƙarfi naira 500 ne.
Matar ta shafe shekara 40 tana wannan harka amma ta ce ba za ta iya tuna yawan mutanen da ta yi wa hanya ba.