Lafiya Zinariya: Shin ana iya daukar farfadiya ta hanyar taba mai cutar?

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Shin ana iya daukar farfadiya ta hanyar taba mai cutar?

Farfadiya na daya daga manyan cutukan da suka shafi kwakwalwa da ake yawan gani a manya da yara a ko ina a fadin duniya.

Sannan akwai rashin fahimta sosai dangane da wannan matsala wanda hakan ya sa akwai camfe-camfe da dama da ke yi kan cutar.

A makon da ya gabata, likitar kwakwalwa Dakta Joyce Oseghale ta yi bayani kan farfadiya da ire-irenta da abubuwan da ke haifar da ita har ma da alamominta.

A wannan makon kuwa, ta yi bayani ne kan yadda ake magance ta a asibiti da irin kulawar da ya kamata a bai wa mai wannan cuta. Sannan ta yi karin haske kan wasu camfe-camfe da ake yi dangane da cutar farfadiya.