Aminu Ala: Mawakin ya ce Hukumar fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi

Bayanan bidiyo, Hukumar fim ba ta da hurumin tace wakokin yabon Annabi - Aminu Ala

Fitaccen mawakin Hausa, Aminu Abubakar, wanda aka fi sani da Aminu Ala ya ce hukumar tace fina-finan jihar Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙin yabon Annabi.

Aminu Ala ya shaida wa BBC Hausa cewa yin hakan daidai yake da "matse tunanin" mawaƙa saboda "ba a tace fasaha".

A kwanakin baya ne, hukumar tace fina-fanai ta Kano ta ce babu wani sha'iri da zai ƙara fitar da waƙa a jihar, sai ta ba shi lasisi.

Shugaban hukumar Isma'il Muhammad Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.