Mamman Daura: Abu 10 da ya shaida wa BBCHausa

Bayanan bidiyo, Cikakkiyar wannan hira na shafinmu na Yotube

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon hirar Mamman Daura da BBC

Bayan shafe kusan shekara 30 ba tare da magana a kafofin watsa labarai ba, a karon farko Malam Mamman Daura mutumin da ake zargin yana juya akalar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya fito fili ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

'Yan Najeriya da dama ne ba su taɓa jin murya ko kuma ganin hoton Malam Mamman Daura ba, wannan ba ya rasa nasaba da rashin bai wa 'yan jarida dama su tattauna da shi shekara da shekaru.

Malam Mamman wanda tamkar ɗa ne ga Shugaba Buhari, ya miƙa ta'aziyya kan rasuwar manyan aminansa biyu wato Malam Abba Kyari da kuma Sama'ila Isa Funtua a ɗan wannan tsakani.

A wani ɓangaren kuma, ya bayyana ra'ayinsa kan matsayin tattalin arziƙin Najeriya da kuma matsalar tsaro a ƙasar wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Ya kuma fito fili ya yi bayani game da ra'ayinsa kan makomar shugabancin Najeriya a shekara ta 2023, inda ya ce mulkin karɓa-karba bai amshi ƙasar ba.

Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya shaida wa BBC:

'Na ji jiki ƙwarai da rashin aminaina biyu'

A tattaunawar da BBC ta yi da Malam Mamman Daura, ya bayyana cewa ya ji jiki ƙwarai da rashin aminansa biyu, wato Malam Abba Kyari da kuma Sama'ila Isa Funtua. A cewar Malam Mamman Daura, dukkansu sun bai wa gwamnatin Najeriya gudunmawa matuƙa.

A cikin hirar, ya kuma shaida yadda suka fara aminantaka da Abba Kyari da Sama'ila Isa har zuwa rasuwarsu.

'Abba Kyari ya farfaɗo da masana'antun taki 31'

A cewar Malam Mamman Daura, daga shekarar 2016 zuwa yanzu, an farfaɗo da masana'antun samar da taki 31 a Najeriya, kuma duk ƙoƙarin Malam Abba Kyari ne. Malam Mamman, ya ce taki ya wadata yanzu a ƙasar. "A da (buhu) yana ₦15,000, yanzu kuma yana ₦5,500," in ji shi.

.
Bayanan hoto, Mamman Daura yayin tattaunawarsa da ma'aikacin BBC, Mustapha Musa Kaita

Mamman Daura ya bayyana dalilin da ya sa ba ya hira da 'yan jarida

A cewarsa, babu dalilin da zai sa ya fito yana surutu a kafafen watsa labarai, ya ce "lokacin da muka yi aikin jarida kowa yana jin mu, lokacin da na yi aikin gwamnati kowa ya san aikin da muka yi, to yanzu da muka gama sai na yi ta surutu? (To) na ce me"? Malam Mamman ya tambaya.

Alaƙar Mamman Daura da Shugaba Buhari

Mamman Daura ya kuma fayyace dangantakarsa da Shugaba Buhari inda ya ce kamar uba yake a wurinsa. Ya kuma bayyana cewa tare suka taso da Shugaba Buhari tun suna yara ƙanana.

'Bana zaƙewa wajen bai wa Shugaba Buhari Shawara'

A cewar Mamman Daura, yana zuwa wurin ɗan uwansa wato Shugaba Buhari domin su gaisa, kuma idan shugaban ya tambaye shi shawara yana ba shi, amma ba ya zaƙewa ya ce dole sai an yi yadda yake so.

A cewarsa, ba a yi wa gwamnati haka. Ya ce zarge-zargen da ake yi masa cewa yana zaƙewa a wajen shugaban ƙasa ba gaskiya ba ne.

Ra'ayin Mamman Daura kan zaɓen 2023

A ra'ayin Malam Mamman Daura, kamata ya yi jam'iyyar da ke mulki a yanzu ta tsaya ta yi nazari domin duba mutumin da ya fi cancanta a tsakanin duk waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin shugaban ƙasa.

A cewarsa, "za a iya dubawa ko daga arewa (ne) ko daga kudu su tsayar, abin da ya kamata su yi ke nan.

Ya ce amma akwai fahimta da wasu 'yan Najeriya suke da ita duk da cewa ba a rubuce take ba ta mulkin karɓa-karɓa. A cewarsa, "an yi karɓa-karɓa sau ɗaya, (an yi) sau biyu har sau uku, ya kamata ƙasar nan mu zama mun cuɗu, cewa wanda ya fi dacewa ya kamata, ba wanda ya zo daga wuri kaza ba".

'Akwai bambanci tsakanin aikin gwamnati a da, da kuma yanzu'

Ganin cewa Malam Mamman Daura tsohon ma'aikacin gwamnati ne tun lokacin mulkin En'E, BBC ta tambaye shi ko akwai wani bambanci tsakanin aikin gwamnati a da, da kuma yanzu?

A cewarsa akwai bambanci. A can baya idan ma'aikaci ya makara zuwa wurin aiki har shari'a za a iya yi masa, in ji shi. "Amma a yanzu sai ka je ka ga rabin mutanen ministry ba sa nan, ko su tashi da wuri, ko ba su zo ba".

Ya kamata gwamnati ta farfaɗo da noma da kiwo da haƙar ma'adinai

A matsayinsa na mutumin da ya karanci fannin tattalin arziƙi, Mamman Daura ya ce tun yana aiki da jaridar New Nigeria yake kira cewa kada a dogara da man fetur, domin wata rana mai zai zo ya zama ba shi ne abin dogara ba.

Ya ce ga shi yanzu mai ya lalace, "abin da wannan gwamnatin take yi shi ne daidai, a gyara noma da kiwo da (harkar) ma'adinai da masaƙu shi ne mafitarmu", in ji shi.

Ra'ayin Mamman Daura kan rashin tsaro a Najeriya

Malam Daura ya ce lokacin da gwamnatin Buhari ta zo akwai ƙananan hukumomi 18 na jihohin arewa maso gabashin Najeriya da ƙungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta, inda suka kori sarakunan da ke yankin, ya ce a halin yanzu an yi maganin wannan kuma kusan an gama da su.

"Halin da ake ciki a yanzu sabuwar masifa ce, domin lokacin da aka kashe Shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi, sai gwamnatin ƙasar ta tarwatse, ya sayi ɗumbin makamai, duk sai aka yi ta wasoso, to shi ne duka (irin waɗannan) mutanen suke zuwa.

Najeriya da Mali da Burkina Faso da Chad da Nijar duk a hargitse suke," in ji shi.

"Kuna zaune kawai a cikin ƙauye sai mutane su zo da babur su kashe na kashewa su ƙone na ƙonewa su ɓace."

Mafita kan shawo kan matsalar tsaro

A ra'ayin Malam Mamman Daura, mafita kan matsalar tsaro a Yammacin Afrika ita ce duk gwamnatocin ECOWAS, wato Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma su haɗu su yi babban shiri don maganin rashin tsaro.