Bidiyon yadda 'yan sanda suka kama 'yan China a Abuja

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda 'yan sanda suka kama 'yan China a Abuja

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu 'yan kasar China biyu bisa zargin kulle wasu 'yan Najeriya inda suka kwashe wata hudu suna tursasa musu yin aiki a otal dinsu.

Mutanen sun kwashe tsawon lokaci suna yin aikau a otal din na 'yan China da ke unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, amma ba a hana su shiga da fita ba sai watanni hudu da suka wuce lokacin da annobar korona ta yawaita a kasashen duniya.