Muna kokarin gano musabbabin ciwon koda a Yobe - Mai Mala Buni
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A cikin wannan hira ta musamman, gwamnan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya Mai Mala Buni, ya yi karin bayani a kan dokar ta-bacin da suka kaddamar a kan ilimi a jihar, da tsarin da suka yi don ganin cewa an inganta ilimin firamare da sakandare.
Ya kuma yi bayani a kan kwararowar hamada da kuma ciwon koda da mutanen Yobe suke fama da su, sannan da matakin da jihar ta dauka don magance matsalolin.