'Cikin shege' ne ya sa aka hana zancen dare a Jigawa

Bayanan sauti'Za a yanke wa wanda ya karya dokar hukuncin biyan tarar naira 50,000'

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren tattaunawarmu da Sanusi A Doro

An haramta zancen dare tsakanin saurayi da budurwa a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar Jigawa a Najeriya.

Majalisar Kansiloli ta karamar hukumar ce ta yi wannan doka sannan kuma daga bisani shugaban karamar hukumar ya sa wa dokar hannu, har aka gudanar da wani kwarya-kwaryar biki, kamar yadda mai magana da yawun karamar hukumar Sanusi Doro ya shaida wa BBC.

Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, idan aka kama saurayi da budurwa suna zance da dare, "za a yanke musu hukuncin zaman gidan yari na wata shida, ko kuma tarar dubu 50."

Karamar hukumar ta bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya sa aka dauki wannan mataki har da "yawaitar juna biyu da ake samu kafin yin aure."

Malam Sanusi ya bayyana cewa ''duk wanda aka kama yana hira da budurwa, ko a manyan garuruwa ko kanana ko a rugagen Fulani, za a gabatar da shi a gaban kotu, kuma zai biya tara ta Naira dubu 50, ko kuma ya yi wata shida a gidan kurkuku.''

Ya bayyana cewa a yanzu haka akwai ma wani da ya kawo shawara kan cewa ya kamata a hana kidan nan irin na ''DJ,'' wanda ake rawa da samari da 'yan mata a lokacin biki.