Dattijuwa mai shekara 82 da mijinta mai shekara 74 na fatan haifar tagwaye a Kano
Latsa wannan hoton da ke sama domin kallon bidiyon wani bangare na hirarmu da ango da amarya
Abin mamaki ba ya karewa. Muhammadu Liti, mai shekara 74, da amaryarsa Fatsuma, mai shakara 82, sun yi aure bayan soyayya ta dan wani lokaci.
Masoyan biyu dai sun hadu ne sakamakon zuwa da Malam Muhammadu yake yi wajen Fatsuma sayen kosai.
Muhammadu Liti ya ce duk namijin da ka ga yana ta shawagi wajen mace ai hakan ba ya rasa alaka da soyayya.
"Mukan tsokani junanmu domin ni ina Bagobiri ita tana Bakatsiniya, amma da soyayya ta ratsa tsakani, sai muka manta da hakan." in ji ango Muhammadu.
An tambayi Amarya Fatsuma ko ta yaya angon ya kama zuciyarta? Sai ta ce, "yakan yi mini kyauta idan ya zo siyayya, kama daga kudi da kayayyakin amfani na yau da kullum."
Da Muhammad Liti yana da mata uku amma daya ta rasu, sai ya maye gurbinta da Fatsuma.
Kalubale
An ta kai wa 'ya'yana gulmar cewa kuna kallo mahaifiyarku za ta yi aure, "amma babbar 'yata Maimuna sai dai in mata addu'a domin kuwa cewa ta yi abin da duk 'ya take wa mahaifyarta za ta yi min, kuma ta yi haka ita ma karamar 'yata Aminatu," in ji amarya Fatsuma.
Ko yaya kike fita hira ga jikoki suma ana sallama da su? Sai ta yi dariya ta ce, sai su cashe, ba zawarinta ai na jikokinta ne, tana zance jikokinta na yi.
Shi ko Malam Muhammad cewa ya yi bai fuskanci wani kalubale ba, saboda yana da ikon fada aji a gidansa.
Da aka tambaye shi ko yaransa maza ba su nuna ma tirjiya ba.
Sai ya ce "Maza, akwai wadanda suka aiko mun da taimako ma na kudi in yi harkar biki."
"Ko da Fatsuma ta girme ni, amma ni ne mijinta dole za ta bi umarni na kuma ni ma in kyautata mata," in ji Muhammad Liti.
Daga karshe, sai amarya ta rangada guda ta ce tana cikin farin ciki sosai, ango kuma ya ce 'yan tagwaye yake fatan samu a gidansa a nan gaba.