Yadda aka yi wa sojojin Nijar 71 sallar jana'iza

A ranar Juma'a ne shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou ya jagoranci yi wa sojoji 71 da suka mutu salla, a birnin Yamai.

Niger
Bayanan hoto, Malamai sun gudanar da addu'o'i lokacin jana'zar sojojin 71 da aka kashe
Shugaba Issoufou
Bayanan hoto, Shugaba Mahamadou Issoufou ne ya jagoranci jana'izar inda ya yi wa iyalin mamatan ta'aziyya
Niger
Bayanan hoto, Shugaba Mahamadou Issoufou ya katse ziyarar aiki da yake yi a Misra
Niger
Bayanan hoto, Shugaba Issoufou da sauran mukarraban gwamnati yayin sallar jana'iza a Yamai
Niger
Bayanan hoto, Shugaba Issoufou na lika wa gawawwakin sojojin alamun tutar jamhuriyar Niger
Niger
Bayanan hoto, Gawawwakin sojoji 71 a kwance kafin yi musu janaza
Niger
Bayanan hoto, Yadda aka gudanar da sallar gawa ga sojojin 71, inda shugabannin da iyalansu suka kasance a wurin
niger
Bayanan hoto, Sojoji 71 a rufe da tutar Nijar kowannensu
Niger
Bayanan hoto, Wata gawar wani soja dauke da alamar tutar Nijar da ke alamta ban girma ga wanda aka makalawa