Dalilai biyar da ke nuna akwai rashawa a Najeriya

Bayanan bidiyo, Auwal Musa Rafsanjani

Latsa hoton sama domin sauraro da ganin Rafsanjani

Shugaban kungiya mai fafutukar ganin an kawar da rashawa da cin hanci ta CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani ya ce duk da kokarin da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi na dakile rashawa da cin hanci, har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Rafsanjani ya zayyana wasu dalilai guda biyar da ya ce alamu ne na rashawa da cin hanci a Najeriya.