Hotuna: Yadda sarkin Hausawan Turai ya nada hakimansa

Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a masarautarsa da ke Paris
Bayanan hoto, Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a masarautarsa da ke Paris
Sarkin Hausawan Turai tare da Marafan Hausawa kuma Hakimin London, Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma Dan Isa, Dr Usman T Shehu
Bayanan hoto, Sarkin Hausawan Turai tare da Marafan Hausawa kuma Hakimin London, Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma Dan Isa, Dr Usman T Shehu
Hakimai takwas Sarki Jan Kado ya nada a ranar Asabar a fadarsa da ke Paris
Bayanan hoto, Hakimai takwas Sarki Jan Kado ya nada a ranar Asabar a fadarsa da ke Paris
Paris, France 23 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, Wadanda aka nada sun fito daga kasashe daban-daban na Turai
Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Bayanan hoto, Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Akwai masu rike da sarautar Dan buran, da Sallama, Da Falaki da Shamaki da kuma Uban Doma
Bayanan hoto, Akwai masu rike da sarautar Dan buran, da Sallama, Da Falaki da Shamaki da kuma Uban Doma
Masarautar na da Jakadiyar Sarki, da Giwar Sarki da kuma Gimbiyar Mawaka
Bayanan hoto, Masarautar na da Jakadiyar Sarki, da Giwar Sarki da kuma Gimbiyar Mawaka
An baiwa Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Hausawan Turai, Asabar 24 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, An baiwa Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Hausawan Turai
Nadin sarautar hakiman masarautar Turai, Asabar 23 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, Baya ga wadanda aka nada sarautar, wasu sun halarci bikin nadin daga kasashe daban-daban na nahiyar Turai
An nada Jakadiya da kuma Giwar sarki, Asabar 23 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, An nada Jakadiya da kuma Giwar sarki
Nadin sarautar hakimai a masarautar Hausawa da ke Paris, 23 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, Masu rike da sarauta a masarautar kan sanya kaya irin na al'adar kowace masarauta da ke kasar Hausa
23 ga watan Nuwamba a birnin Paris na kasar Faransa
Bayanan hoto, Wadanda aka nada wa sarauta sun hada da mata da maza daga yankuna daban-daban
Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Bayanan hoto, Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Karagar sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris, Faransa
Bayanan hoto, A makonnin baya, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci masarautar a Paris inda ya jadadda sarautar Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jan Kado
Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba, 2019
Bayanan hoto, Daya daga cikin kofofin shiga fadar sarkin Hausawan Turai da ke Paris a kasar Faransa.